← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 64

Sashe 12

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bata hakuri amma gabadaya taki saurarenta tasake jaddada mata cewa muddin bataja'yarta a jiki ba to tamance itama tana da uwa a raye. Kiran number Aunty Zainab tafada mata duk yacce sukai da Amma,itama fir tarufe Ido tama Ummie sol. Tsakanin Ummie da hajiya Zainab tazarar shekara daya da rabi ne. Haka dai Ummie tadawo gida jikinta sam babu kwari tarasa wanda zataje wajensa suyi magana taji dadi ita ba kawaye ba,a yanzu duk wanda zataje wajensa neman shawara kara mata takaici zasuyi,banda huci babu abinda takeyi a fili tafurta"Natsaneki Zuhra tabbas bacin nice dakaina na haifeki zan iya tsine miki saboda kina daf da rabani daduk wasu masoya na,na haifawa kaina masifa na haifawa kaina jaraba? Sosai hankalin ya Taufeeq yatashi don yana gaf da shigowa parlon yaji zan tuttukan da Ummie keyi, idanuwansa sun kada sunyi jajazur juyawa yayi yafasa shigowa parlon,kaitsaye bq dinsa yanufa a daddafe, Aseef sai masa magana yake amma Ina baiji ba. Da harara Aseef yabishi a fili yafurta"Idiot"cikin murya kasa kasa. ****** Zuhra ce cikin shagwaba da sangarta take latso wasu hawaye mere dan mitsitsin mouth lip dinta tayi tana muttsike Ido cikin muryan son kuka tace"Toh yanzu Abbie idan kuntafi yaushe zaka dawo?ni wallahi bangaji da ganinka ba fah. Dan dariya Abbie yayi tare da shafa kanta yace"zamu dawo azumi mana kinmanta azumin saura 1month?so insha Allah I think sai lokacin zamu sake zuwa. Daddy ne suka kariso shida Abba da Baba Hasheem, Daddy ya dubi zuhra yace"A'ah mamana kema yau zaki koma ne bamu da labari? Dan sinnar da kai zuhra tayi cikin girmamawa tana wasa da yatsunta tace"A'ah Daddy narako su Abba ne da zasu tafi. Dan murmushi sukayi gabadaya Abba yace"hmmm kya fadi gaskiya,Yaya kuka take nema tamaka koh?yakarasa zancen cikin zolaya. Dan rissinawa tayi tadauki ledan dake gefenta tamika ma Abbie tace"Abbie gashi abaiwa Ummie na da mommy,akwai sweet da chocolate na maimoon da Ateek. Abbie ya amsa yace"toh shikenan Allah yamiki albarka. Da Ameen ta amsa tare da matsawa saboda gabadaya sun nufi mota daya motar Daddy kenan da ita zasu fita, Baba Hasheem ne ke driving gefensa kuma Abba ne,sai baya Daddy da Abbie cike daso da kaunar junansu suka fita,zuhra natsaye har Baba mudi yabude musu gate suka fice,hawaye ne ya zubu mata da sauri tasa hannu ta goge,saboda shigowar Aunty muneefa datagani da wasu 'yanmata biyu. Abangaren Abbie shima runtse idanuwa yayi yabude tare da sauke ajiyar zuciya yana mejin tsananin tausayin diyarsa duk Daddy na lure dashi shima girgiza kai kawai yayi,kaitsaye motar airport tanufa. Zuhra murmushi a face dinta tatare Aunty muneefa. "Aunty muneefa barka dama kece?muneefa na murmushi tace"Eah zuhra kwana biyu bananan ina school shiyasa. Haka kawai Zuhra taji sam wacce suke tare da muneefa batayi mata ba don haka ko kallonta batayi ba,a gefen ma haka ne don lokaci daya taji tsanar zuhra ta dirar mata,sake shaqa tayi a dalilin ko inkular da zuhran tanuna mata,yarinya qarama da sanabe,tafadi hakan a ranta. "Dawowata kenan yanzu nabiya gidan Guggo Laure shiyasa ko hutawa banyi ba,murmushi zuhra tayi. "Eyya Aunty nima apartment dinku zanshiga don ko jiya danazo gaida Mom batanan. Muneefa tace"ok muje koh? Dayar ce tayatsine face"Muneefa bari naje nafara miqa gaisuwa ta ga Ammi kafin nadawo. "Kai Allah don Allah kizo muje mu warware gajiya dududu yaushe muka shigo?dayarl budurwar tafAdal Zuhra kuwa ko sauraren su batayi ba tanufi sashen Mom,a kaikace budurwar ta dalla mata harara. Muneefa tace"Don Allah rabu da ita Suby kinsan Akeela da rawar kai. Zuhra kuwa koda tashiga sashen Mom tagaisheta sosai Mom din taji dadi don Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta sannan takema Aseef sha'awar auren ta. Tana gafda shiga apartment din Ammi Akeela tafito, Zuhra dauke kai tayi kamar bata ganta ba itako Akeela wani banzan kallo ta watsa mata. Koda zuhra tashiga kai tsaye ta nufi kitchen don tasan Ammi tana can,ilaikuwa sunata aiki itada Aunty Mashahuda da maid dinta Amina. Murmushi kwance a face din Ammi ta tarbe Zuhra,dan rissinawa tayi ta gaishe da Ammi. Dan turo mouth tayi alamun shagwaba tare da karyar da wuya tace"kai Aunty shine ko ki aiko nazo nataya aikin?nasan Daddy akema abin shan ruwa. Hararar wasa tawatsa mata sannan tace"Aiba sai nace kizo ayiba keda kanki zakizo"takarisa maganar tana dan murmushi. "Ammi wallahi namanta Daddy yana azumi saboda naje raka Abbie ne shiyasa duk na shagala. Kallon ta Ammi tayi fari'a kwance a saman fuskarta tace"Don Allah kirabu da wannan Auntyn taki,aikinma da sauki don mesa ana masa girke girken bashi nan. Dan dariya kadan zuhra tayi batare da tayi magana ba tafara yanka cabej din dake kan mable din. Mashahuda tace"Hmm ai Yaya akwai shi da iyasa aiki ni wallahi tausayi matar sa kebani. Sallaman su muneefa ne yasasu juyawa gabadaya,kallo daya zuhra tamusu tadauke kai saboda ganin yarinyar nan tadazu. Da murmushi Akeela tamatso kusa da Mashahuda tace"sis kawo in tayaki goge carrot din,dan yatsine face kadan Mashahuda tayi tare da dan sakin yaqe tace"No kada kidamu munkusa gamawa ma ai tunda ga zuhra na gyara cabej. Akeela badon taso ba haka tahakura,ita kuwa Suby gabadaya hankalin ta yakoma kan zuhra faffadan kugunta kawai take kallo( _acewarta_). Muneefa tace"Sis muje kada kuyi magrib, Ammi tasaki murmushi tare da duban Akeela"Akeela ya hajiya maimunan take? Cike dajin dadi tace"wallahi tananan lafiya mommah. Murmushi Ammi tasake saki akaro na biyu tace"to don Allah kigaisheta mungude sosai. "Ai babu damuwa mommah nima fa 'yar gida ce. Ammi murmushi kawai tayi bata sake magana ba,muneefa tace"yee gaskiya ne Auntymmu, Allah dai yabar kauna keda ya SAUBAN! A gigice zuhra tadago tana duban muneefa sai dai kowa hankalinsa baya kanta,wani mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta a cikin jin an ambaci sunan Wanda batayi zato ba,a kaikai ce tasake duban Akeela da wasu second's zuwa can ta sauke ajiyar zuciya,aranta tace toni meye damuwa na? Nanfa muneefa tafara magana"Ai wallahi bikin nan haba za'ayi abinda ba'a taba yiba sai ansan anyi biki na jinin Galadima auren ya Sauban ai dole muci uwar sabada. Akeela tace"ai gaskiya za'ayi biki nagani nafada hmmm kudai Allah yakaimu lokacin, mommah muntafi tayi maganar tana ma Ammi bye bye. Daga Zuhra har Mashahuda kallon mamaki sukabi Akeela dashi, Mashahuda tadubi Ammi tace. "Cabdi wallahi Ammi kinsan da matsala Yaya Maison mace mai kunya amma jibi wacce aka bashi matsayin mata?hmm wallahi nidai bana son Yaya ya aureta sam,tayi maganar tana daga hannu tare da nuna iyakacin gaskiyar ta, sauke ajiyan zuciya Ammi tayi tace"please Mashahuda ni bana son kananun zantuka haba abar maganar. "Hmm Ammi kema fa kinsan Yaya be dace da wannan yarinyar b.... "Allah Mashahuda zan saba miki,tayi maganar cikin muryan bacin rai. Itadai Zuhra ko tankawa batayi ba tanata yanka cabej dinta,sai dai hakanan tatsinci zuciyar ta cikin bacin rai lokaci guda. Hakanan taji tayi mugun tsanar Sauban din dashi da Akeela. *******^^^****** Sosai yaqara gogewa da kyau yazama wani classic guy wanda ko a malysia ma 'yan mata rububinsa sukeyi. Yarasa dalilin da yasa yake sake tsanar auren da ake nema a qaqaba mishi itakanta yarinyar bayajin zai iya aurenta duk da kuwa besanta ba. Messenger sane yashigo office din yace"Sir kayi baki. Duban CCTV camera dinda ke office din yayi yana duban mutanen dake Zaune a wajan office din nasa,maido da duban sa yayi ga massenger yace"Miracle who re those people? "I don't know Sir,yayi maganar cike da girmamawa. Dan girgiza kai Sauban yayi tare da cewa"Ok jeka shigo dasu. "Ok Sir,yayi maganar yana fita babu jimawa yashigo da baqin. ******** "Boka so nake a sauko da auren lokacin da aka sanya na bikin nan wallahi yayi tsayi ita kanta yarinyar takosa ace tayi aure tahuta,bari kaji nifa so nake a mallake mana yaron ya zama na bayajin maganar kowa sai nawa,kai yazama mai taurin kan tsiya. "Hahahaha,aka kyalkyale da dariya,wani dan wadan aljani ne wanda sam bayada kyan gani ko kadan kuma daga ganinsa baya da imani yace" _BANADA LAFIYA FANS DON ALLAH INA BARAR ADDU'AN KU Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 15/16 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ PLS KUTAYANI DA ADDU'AH MASOYA ALLAH YAKARAMIN LAFIYA DON CIWO YASANI GABA SHIYASA KUKA JINI SHIRU KWANA BIYU BANJIN DADI, NAGODE SOSAI DA SAKONNIN GAISUWAR KU MUSSAMMAN MA KE *MAMAN HEELAL* KEDIN TA DABANCE. _____Zuhra ce zaune a parlon Bodejo tana yimata massage,sallamar Baba mudi gateman sukaji a bakin kofan parlon,amsawa sukayi inda Bodejo tabashi izinin shigowa. Cike da girmamawa ya rissina yace"Barka da warhaka Bodejo,inayini ina gajiya? fuskar ta kadaran kadahan tace"yauwa mudi lafiya Alhamdulillah ya kuma aiki? Baba mudi yace. "Alhamdulillah! Dama wani yaro ne a waje yazo yake cemin don Allah nakira masa Fateema. Cikin natsuwa Zuhra tadago tadubi Bodejo itama ita take kallo,maida dubansa tayi ga Baba mudi tace"Fateema kuma mudi?wa Fateema tasani a garin nan har zai aiko akira masa ita? Tayi tambayar cike da mamaki. "Wallahi kuwa Bodejo bansan shi ba nidai yanata roqona kan nakira masa ita. "Ikon Allah ko wanene haka oho?tashi kije kiji ko wanene. Dan tsamm Zuhra tayi tare da dan bata face tace"nikam bazani ba Bodejo wallahi bansan shiba kawai ina zaman zamana ya wani kirani? Takarisa maganar tana kokarin shiga hanyan corridor din Bodejo,sakin baki Bodejo tayi tana duban Zuhra,kallon Baba mudi tayi tace"shikenan mudi kace tana zuwa. Mikewa yayi tare da fita,murmushi kawai Bodejo tayi tana kokarin mikewa ne sai ga Mashahuda tashigo,dan gaida Bodejo tayi sannan tace. "Bodejo ina Zuhra ne tundazu Shuraim yazo nemanta Baba mudi yace yazo ya kirata amma taqi fitowa. Dan tabe mouth Bodejo tayi"Toh ni ina nasanin mata,bansan me take nufi ba,wanine shuraish?dan gwalo idanuwa Mashahuda tayi"kaji Bodejo kuma da bata suna bafa shuraish ba Shuraim ake cewa. "Uhum kudai kuka sani da wani iyayi da sanabe abinda dai nafada shikika maimaita. Rausayar dakai tayi kaitsaye ta nufi bedroom din Bodejo. Koda tashiga kwance taga Zuhra sai daddanna phone nata take hankali kwance,ganin Mashahuda yasa tamike cike da fara'a a fuskarta tace"Aunty Mashahuda kece? Hararar wasa ta zabga mata tace"kyace mana nice tun dazu mutumi yazo nemanki kina wulaqanta sa haba Zuhra menene haka?
Chapter 12 · 0% Book details