← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 64

Sashe 22

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanda nakeda cikin Zuhra,kuma Allah inaso cinshi sosai. Kama baki hajiya zainab tayi"cabb!gaskiya shekarun da yawa,Anya kuwa wannan ko kingani zaki iya ci kuwa ma? Dariya ummie tayi tace"ci kuwa sosai,inafa son shi don kawai bansamu bane,kai duk da haka ma nina mance da wani abu wai dan gauda. "Aikuwa insha Allah gobe da sassafe zan dauki driver muje kasuwa munemo garin dan gauda don acan zan siya masara ta kuma nabada nika a hada min komai da komai sai dai dana tashi nazo nayi miki,yajin ma musamu wanda yaji tafarnuwa don nasanki da son tafarnuwa,takarisa maganar tana dariya zuciyar ta fal nishadi. Nan ko suka cigaba da hirarsu suna dinner abin gunin sha'awa. Washegari kuwa kamar yanda hajiya zainab ta alkwaranta haka ne tafaru don wajen karfe sha daya na safe tafara kwabin dan gaudan ta tayi na ummie daban sannan ta kwaba nata dasu Bodejo daduk dai me sha'awan ci, zuhra na tayata,babu bata lokaci ta cewa zuhra tacigaba da zuba dan gaudan da wannan yayi za'a zuba na ummie ne. _____________ "Tab ai wallahi kinbani kunya Akeela kitsaya wannan yarinyar ta farfada miki magana haka?babu abinda ke cinta sai bakin ciki da hassada dole tasan kika mallaki guy dinnan kin mata fintinkau,na gaba yayi gaba na baya ai sai tsintar hula,aike dai kibari kawai zamuyi maganin tane karamar 'yar iska"Suby tayi maganar tana karkada kafafuwa. Akeela tasauke wani ajiyan zuciya tace"ni ba wannan nake tsoro ba kada watarana tace zata tonamin asiri kunsan fa tasammu farin sani ta kuma san abinda muke aikatawa. Tabe mouth zuleey tai tace"to sai mene?su da babu abinda suka sani sai Shan minti da samari fa?abi wannan saurayi abi wancan. "To ai inaso kisan nata me sauki ne akan namu namu yafi nata muni,wallahi ni da ace wani a cikinsu zaiji wannan labarin to nida shiga GALADIMA FAMILY matsayin mata wallahi sai gani sai hange don bazasu taba bari na aure ya Sauban ba,shiyasa nakeso Allah nadena wannan harkan fa don ni duk abinda zai shiga tsakanin aurena da ya sauban gudunsa nakeyi don rasa sa wallahi babban asara ne kuma bazan jura ba,wallahi na rasasa zan iya mutuwa. Wani harara zuleey ta watsa mata a ranta tace" _Hmmm indai ina raye bazaki taba auren saurayin da nake mafarkin aura ba tunda nataso nasan waye Muhammad Taleeb Muhammad Sauban yatafi da imanina,muddin bazan sameshi ba wallahi kema bazaki taba samun saba._ Suby tace"Lallai Akeela keko wani irin so kike ma Sauban haka?kinmance ba'a hada soyayyar mommy data kowa?ina guje miki randa zaki juyama mommy baya don kuwa kinsan sai kinshiga cikin gagaruman matsala. "Huhhhh! Suby don Allah kukasance koda yaushe cikin yimin fatan alheri ba fatan tsiya ba,meyasa kuke kokarin fasamin kwanya ne?inaso kugane cewa ko wanne da matsayinsa a waje na,amma banaso Kuna hada soyayyar ya Sauban data kowa please"takarisa zancen tana bata face. Da mamaki duk suka dubeta,zuleey tace"harda ta mommy?wani banzan kallo Akeela ta watsa mata tace"bansaniba mtsewwww,wallahi zuleey kwana biyu kaman kina neman zama munafuka ce,inafa lure dake kina kokarin shiga tsakanina da Mommy wallahi shiru kawai na miki,hmm kicigaba. "A'ah dakata mana Akeela"zuleey tayi maganar tana mikewa"akan me zakice min munafuka?menamiki na munafunci?kidubi tsaban ido na kicemin munafuka?ko a girme na girmeki kibar ganin ina binki kamar rakumi da akala wallahi bashi zaisa na dauki cin zarafi ba. Itama Akeela a fusace ta hayayyako mata"kada Allah yasa kidauk...... "Guys!guys!! Haba meye haka?kun manta mudin suwaye?meyasa kuke kokarin bawa haters damar shiga tsakaninmu?gaskiya banji dadi ba,gaskiya banson haka inkuwa ba haka ba sai atafi wajen mommy. "Bama sai anje ba!!duk su biyun suka hade baki,murmushi Akeela tasaki tace"Shikenan kiyahakuri zuleey,fuskan zuleey kadaran kadahan itama tace"Allah yabaki hakuri tana kare fadar haka tamike tare da daukan jakanta tadubi Suby tace"ni zan wuce gida yanzu Suby. Murmushi Suby tayi"Lallai zuleey Ashe baki huce ba?babban matsalata dake dama riko,meye amfanin hakan a tsakaninmu? "Ba maganar riko bane Suby zanje gida don nasan hajiya zatayi ta zuba idon ganina yanzu. "Shikenan kigaida gida sai munyi waya,Suby tafada. Akeela tace"adai yayyafewa juna akara hakuri,ko tankata zuleey batayi ba tafice tanajin zuciyarta namata wani irin tukuki. Tabe baki Suby tayi"banziya munafuka ainaji dadin abinda kika mata don yanzu Suby karfi da yaji takoyi munafunci da hassada" Akeela ta dubi Suby tace"Ashe kema kin fahimta?ai sainayi maganinta batasan ina raga mata bane saboda hater's kiris suke jira. Anan dai suka shige daki tare da rufo kofar rufff! *GALADIMA FAMILY* Sosai Ummie tadinga santin dan gaudan mai da yaji don yayi dadi sosai,suma su Bodejo kadan suka dan tsakura. Washegari su Adda zainab da Amma suka tattara komatsan su tare da Sha tara na arziki drivern Daddy yadaukesu don maidasu gida, Amma zata sauka gidan hajiya zainab ta kwana biyu sai takoma Zaria. Haka rayuwa yadinga tafiya tun ana abu saura kwanaki satittika watanni har takai dai yau saura 1month da 3 week's biki,indai aikin ya Sauban kuma yakoma Canada,aka bashi matsayin chairman na branch dinsu na Canada saboda sam basu fatan abinda zaisa su rasa sa matsayin ma'aikacin su jajirtacce mai amana, kafin kace me har ya Sauban yasake zama celebrity,kudi kuwa sun zauna masa sosai su Daddy ke alfahari dashi,shima ya taufeeq yasamu aiki a Abuja yana aiki a CBN, Aseef nedai har yanzu yake lecturing din a ABU wanda hakan sosai yake taba zuciyar Mom,kuma haryanzu bin malaman suke daga ita har hajiya Biba amma babu nasara don Sauban din ma baidawo kasar ba ballanta na aikin yatafi yanda akeso. A dai-dai wannan lokacin ne Kuma akatafi yajin aiki wanda yasa su Laila da nihal dawowa maidugri,su tattaro kayansu gabadaya a sashen Ummie suka tare saboda yanda gabadaya take sangarta 'yan matan. Mom tunda ta fahimci muneefa zata shiga gidan masu arziki kuma manyan mutane sai ta dora ma ranta salama tadena maganar wani hadin Sauban da muneefa kamar yanda ita takeso,don a zahirance iyayen yaron Suma sunada kudi sosai ga asali da nasaba. ________ "Hajiya don Allah kidena wahalar da kanki akan Sauban shidin yafi karfina wallahi ba ajina bane nasani kema Kuma kinsani,to mezesa muyi kokarin yaudarar kanmu?nina ma hakura dashi don ina rokon Allah yaciremin son shi,duk idan nayi sallah sai nayi addu'ah zabin mafi alkhairi. "Ke dalla tafi can kibani waje,wallahi bakinki yasari danyan Kashi Rammat,kinsan Allah kifita idona na rufe,meye Akeelan zata nuna miki?alhalin kinfita komai,yarinyar da ba abinda tasani sai gantali daga bin maza sai madigo,a haka kuma kikeso nabari suyi nasara? inason kudi Rammat!inason su,kina kallo 'yar uwanki duk a gidan mijinta ne baikai sauran karfi ba amma duk watan duniya shike ciyar damu cima mai kyau,shine kike kokarin yimin asaran samun mai kaini hajji da umara duk shekara?hajiya Biba takarisa maganar tana zaro ma Rammat idanuwa. "No hajiya ba haka nake nufi ba idan munada rabo ai ba lalai sai shiba kawai kimin zabin nagari. Tana kare fadan haka ta mike tare da wucewa kitchen. Da harara hajiya Biba tabita"ku kujimin 'ya 'yar bakin ciki,to baki Isa ba wallahi. XAHRATTY CE Lallai Alqalami yafi takobi [5/9, 19:38] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 35/36 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *THIS PAGE IS DEDICATED TO MY SWEET SISTER BILKISOU M BELLO,SHEKARU BIYU CIKIN NA UKU KENAN DA RASUWAR KI,ALLAH YAKAI RAHAMAR SA MAKWANCIN KI NAYI RASHIN AMINIYA,ABOKIYAR SHAWARA,WANDA SAMUN KAMARTA ZAIYI WUYA ALWAYS I MISS YOU AUNTY BILLY _____Guggo Laure ne zaune a daya daga cikin kujerun farlon Galadima,tsaban yanda masifa ke cinta idanuwan nan an kankance su,sauraran bayanan Galadima takeyi har yakai aya sannan tadora. "Yaya muhammadu nifa ba haka nake nufi ba,sam abinda Sauban yakeyi baya kyautawa,kamar yama mance da ranar auren shi da Akeela a kansa?tunda akasanya rana banaji yaron nan yataba nemanta a waya koda sau daya ne,sai kace wanda za'a aura masa makiyiyar sa?takarisa maganar tana sake tsuke fuska. Shidai Daddy shiru yayi gabadaya yana mamaki tare da shocked din halin guggon nasa wanda kullum babu alheri sai tashin hankali,gyaran murya Baba Hashim yayi yace"yanzu Guggo ita yarinyar ce duk ke fada miki haka? "Ai Hashimu koda Akeela bata fadamin ba abune da yake a bayyane domin kuwa ina gani da idanuwa na,ga damuwa karara tattare da ita,nasan baya sonta amma hakanan zai aureta kodan karfafa zumuncin mu,shi nakeso ta aura, Kuma ko baya sonta dole ya zauna da ita wallahi"takai aya tana zazzare idanuwa. "To yanzu menene abinda kikeso ayi Laure? "Tambayar da tuntuni ya kamata ace kamin kenan Yaya,sonake asashi yakira ta a waya kuma ko babu komai yadinga kulata ko yaya ne,amma yarinya tana neman ramewa da karewa a banza a wofi? "Shikenan Allah yashige mana gaba,insha Allah za'a kirashi amasa magana,amma maganar gaskiya Laure niban fiye son yawan korafe-korafe ba,haka za'ayi auren ana korafi dakawo kara?alhalin irin auren nan babu inda baya zuwa?gaskiya banso yakamata kizaunar da ita kikara fahimtar da ita menene aure?don shirmenta yayi yawa"Galadima yayi maganar yana bayyana bacin ransa karara. "Kayahakuri Yaya muhammadu za'a kiyaye. "Aini ba wani abu nace ba kuskuren da ake tatkawa nake kokarin gyarawa don bazamu zuba idanuwa muna gani ayita kawo korafe-korafen matsaloli ba,don Allah kinatsar da ita. Sosai jikin Guggo Laure yayi sanyi,gudun kada yayan nata ya botsare yasa tamike tare da yimusu sallama tafita,jingina Galadima yayi da jkin hadadden kujeran nasa yana me lumshe idanuwa,muryan Baba Hashim ya tsinkayo"ni wallahi lamarin auren Sauban da yarinyar nan fa yafara fitamin a rai,ace tun yanzu korafe-korafe sunfara shigowa ciki to inaga ma anyi?ita Guggo ko la'akari batayi da yaron nan fa auren dole za'a masa,auren biyayya zaiyi,yafada shi baya son yarinyar nd baya son abinda zai bata zumunci,to gaskiya za'a wa tufkar hanci tun wuri. Ajiyan zuciya Daddy ya sauke tare da cewa Allah ya kyauta nan suka cigaba da tattaunawan su akan tsaida ranar bikin tunda iyayen ma'aruf mijin da zai aure muneefa suka basu dama. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har takama yau saura wata guda biki,akuma ranar ne Ammi da Ummie suka shirya sai kasar Dubai don siyoma yara kayan kitchen don ko Mom bata sani ba,a gefen ta itama sai shiri takeyi batare da tasaka kowa a cikinsu ba don tayi alkawarin sai ta shayar da kowa mamaki da kayan kitchen din
Chapter 22 · 0% Book details