Sashe 39
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanda mata manya wasu ma sunyi 'yar ciki da Akeelan amma haka suka tike sai rawa sukeyi suna rungume da junayen su,duk cikan su ba kayan arziqi bane a jikinsu.Ji sukayi sautin wakar ya tsaya cak,wata hajiya ce tafara jiyowa ganin Sauban yasa tayi mutuwar tsaye don ba karamin kyau yaron yayi mata,tabbas a haife ya haifeta,ganin irin kallon da take masa yasa cikin bala'i ya qanqantar da idanuwa,muryan Akeela ne yafara tashi"Oh honey barka,hope kadawo lafiya?tayi maganar tana nufarsa tare da kokarin fadawa jikinsa,cikin zafin nama ya tureta side,tare da kololuwan 6acin rai ya nunata tare da fara magana"kafin nadawo sashen nan,ki tattara min wadannan 'yan iskan kazaman su barmin gida,if not nadawo wallahi sai na rufe kofan parlourn na muku dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya kamar wani zaki,cikin 6acin rai ya isa sashen shi,kaitsaye bathroom ya isa ya sakin ma kansa shower yana sauke ajiyar zuciya,face dinsa a runtse,idanuwan ta yafara haskowa da yanda tasake wani cika da tsananin kyau,murmushi kawai yasaki,a gurguje yafito ya shirya cikin kananun kaya wadanda suka masa matukar kyau. Fita yayi, dai-dai lokacin su kuma matan wadanda sunkai biyar suka fice daga gidan,yana mamakin yanda Akeela ke tara masa mata a gida musamman wadanda ma sun haifeta sun juya sannan daka kallesu kasan shedanu ne,sam baya son tabbatar da zargin da yake akanta hakan yasa ya saki dogon tsaki, Galadima house ya nufa direct apartment din Bodejo ya isa yana waya da Taufeeq akan rashin lafiyar da Mashahuda keyi,sai tsiya Sauban yake masa wai ko ciki ne. Sam basu kula da juna ba saboda saurin da take taje sashen Mom,sanye take da wata gown wacce tadan bude gabadaya iya gwiwwa ta tsaya mata rigar,sai dai duk da haka be hada tudun saman ta bayyana ba,haka kuma be hana tudun bom bom dinta bayyana. Garam!karar bugewar su ta bayyana,da sauri zuhra tadan dafe goshinta tare da cewa"ouch! Matsawa gefe tayi da sauri saboda kallon da taga Sauban na mata sosai tasha jinin jikinta,sake hade rai yayi dama da ragowar 6acin ran da Akeela ta hada masa yake,cikin tsukakkiyar fuska yace"Ina zaki da wannan dressing din haka?in ina Zuhra tafara"dama..d...dama leqawa zanyi nadubo abu shine,cikin muryan tsawa yace"Dallah go back my friend,wallahi akan ire-iren wadannan banzayen dressing din da kike a gidan nan sai na baki mamaki,yayi maganar yana ra6ata ya wuce, Bodejo da fitowan ta kenan daga palour Galadima tace"To sarkin kwarwa kadawo kenan,yanzu kuma ba zata samu wani sakewa ba,haba jama'a wai meyasa duk idan kashigo da masifar fadan ka baka saukewa kan matarka sai ita? Sauban fuska a daure yace"to ai itama matar tawa ce Bodejo,idan ki kaga na mata fada itama lefi tayi, Bodejo tace"to sannu me mata ai saika cigaba. Mikewa yayi yanufi parlourn Galadima batare da yasake bin ta Bodejo ba. Bayan kwana biyu,gabadaya Zuhra time din kanta ma wahala yake mata cuz exam da suke ta shirye-shiryen farawa sam lokacin ta na karatu ne,sai dai kullum tana shiga kowane apartment da safe gaishesu,a bangaren Ammi kuwa sosai take samun kalawa,don sam Ammi bata dauke ta wata surika ba,sunyi kusan kwana biyu basu hadu dashi ba hakan ba karamin faranta mata rai yayi ba saboda ta fahimci a duk sa'in da zasu hadu sai ya nemi lefi ya liqamata ya hauta da fada,Yau ma kamar kullum da wuri suka gama Exam dalilin hakan yasa kawai ta nufi gidan muneefa,sosai Muneefa tayi murnan ganinta ta dade sosai a gidan sai bayan isha'i sannan Mus'ab yadauko ta yadawo da ita,bude motan tafito tana dan rissinawa tace"to Yaya Mus'ab nagode sosai Allah yabar zumunci, murmushi yayi yace"Ameen kanwar mu kicema rigimammiyar tsohuwan nan bazan samu leqowa ba amma ga wannan ki bata"yayi maganar yana miko mata wani leader bag me kyau sannan sukayi sallama yazuge tinted window dinshi yaja motar,cikin natsuwar ta tashiga gidan,harta gota first gate sai taji kamar ana binta a baya ko kafin tayi yunkurin juyowa taji anfisgota,a gigice ta bude baki da niyyar ihu sai dai jitayi andane bakin da yatsu,sosai taji wani azababben zafi, face dinsa ta kalla sosai ya canza jikinta ne yadauki wani irin rawa da tsuma,bakinsa har rawa yake tsaban masifar dake cinsa fuskar nan tayi jajawur,hadata da jikin gate din yayi,da karfi Zuhra ta rintse ido domin kuwa ta sadakar yau me kwatar ta sai Allah,muryan shi tajiyo cikin amo yana magana"Wancan wane dan iska ne ya ajeki a mota?Fateema da aure na a kanki kike kula wasu mazan?da aurena akanki kike cin amanata?wai halan kina mance ke din matar aure CE koh?yayi maganar cikin muryan tsawa yana me matse mata hannu gam kamar zai balla,wani irin kuka Zuhra ta saki jikinta kuwa banda tsuma babu abinda yakeyi"Am talking to you teemah!!!yayi maganar yana daka wani tsawa wanda yasa Ammi fitowa ita da Daddy don apartment dinsu tadan fi farko duk da kuwa tazarar su,cikin muryan kuka Zuhra tace"wallahi ba wani na kula ba kuma ba wani ne yakawo ni....bata karisa ba yace"To uban waye ya sauke ki a mota?karya zanmiki? "Kai Sauban lafiyan ka kalau kuwa?Wai menene kakeyi haka ne?sakin mata hannu kafin ranka yayi mummunar 6aci wallahi a gidannan"Ammi tayi maganar cikin 6acin rai,yakasa sakin ta saboda bala'in kishin da ke cinsa a ransa, Daddy yace"Wai bada kai ake magana ba?sakinta yayi Yana me kafa mata idanuwan sa da sukayi jawur,itakuwa kanta na kasa banda kuka babu abinda take rusawa. "Meke faruwa ne Sauban? Daddy yayi maganar yana karisowa cikin kamewa,itako zuhra kamata Ammi tayi tare da maidata gefenta,yanaso yayi magana yakasa saboda ruwan kwallan da ya taru masa a idanuwa,juyawa kawai yayi yanajin kansa na sara masa yafita daga gate din, Daddy bece masa komai ba don yaga yanayin mode dinsa,"kamata muje ciki muji meyafaru"kamata Ammi sukayi har parlour ta ajeta kan carpet duk suka zauna,nan Daddy yake tambayanta abinda ke faruwa"Wai saboda yaga an sauke ni a mota shine yashigo yafara fada"tayi maganar cikin sanyin murya, Daddy yace"wanene ya ajeki a motar? Zuhra tace"Yaya Mus'ab din Aunty Muneefa ne"Daddy yace"A'ina kuka hadu dashi har ya dauko ki?nan Zuhra ta fara in ina alamun rashin gaskiya"da...dag...daga gidan su naje wajen Aunty Muneefa daga school na wuce"Daddy yace"okay to karfe nawa ya saukeki?zuhra tace"wajen 8:17 kayahakuri Daddy"Daddy yace"wakika tambaya? Zuhra cikin tsananin tashin hankali tace"Bodejo kawai tasani. Girgiza kai kawai Daddy yayi yace"tashi kije da safe zan nemeku kedashi"cikin muryan kuka Zuhra ta mike tafita,da kallon tausayi Ammi tabita tana takaicin abinda Sauban kema Zuhra,duban Daddy Ammi tayi zatayi magana,hannu yadaga mata tare da cewa"Hmmmmm!"dole Ammi taja bakinta ta tsuke. Duk da ya fita apartment din da 6acin rai amma hakan be hanashi soyewa da matarsa ba,duk da bawai wani dadi da gamsuwa yake ba amma haka yake hakuri don gudun fadawa halaka. ********** "A gaskiya Alhaji nagaji da rashin adalcin da ake gwadamin a gidannan kada fa kamanta nima fa matarka ce,akan me tunda kazo duk inda zaka sai da hajiya Aliya kake zuwa?dame tafini?kyau ko kuwa ilimin addini dana boko?dan murmushi Alhaji iliyasu yayi yana girgiza kafa tare da sipping coffee"Alhaji magana fa nake maka"Adda Zainab tayi maganar damuwa tattare da a face dinta,ajiye cup din Alhaji iliyasu yayi yana duban Adda Zainab"Bata fiki da komai hasalima ke kika fita dashi,amma fa kuma ada,domin kuwa a yanzu tafimin ke sau dubun dubata,kin manta ada lokacin da kika fifita ta akan kowa naki,hatta ni mijina?sai nace miki kizo muyi tafiya kiki,amma ita da zarar tamiki kike binta ki tafi?to bari kiji a yanzu Hajiya Aliya tafimin ke nesa ma ba kusa ba. Wani kuka Adda Zainab tasa tace"wallahi baka isa ba Alhaji,wallahi sai na illata hajiya Aliya sai na maidata abar kwatance"tana karisa fadar hakan tafita tana share hawaye tare da jin matsananaciyar Hajiya Aliya da Alhaji iliyasu a ranta,zuciyar ta sai ingizata takeyi akan wani kuduri nata. Shikuwa Alhaji iliyasu sam baiji dar ba hasalima waya yadauka yakira hajiya Aliya akan tagama shirinta su wuce. Sosai komai ya dagulewa Adda Zainab,gashi boka hatsabibi yadena sauraranta kwata-kwata hakan yasa tafara bin malamai akan dai sabauta Ummie don tadau alwashin sai ta sabauta ta tana ganin duk abinda yake faruwa a gidan ta ba komai bane kamar matsalar ta da Ummie ( _Kai jama'a hassada mugun ciwo,mu guji kanmu da hassada domin kuwa masifa ne,gadai Adda Zainab nan haka kawai babu abinda Ummie ta mata amma ta tsaneta sam bata son ko bude ido tayi taganta a doron kasa, Allah yasa mudace ya rabamu da ciwon hassada Ameen domin maganinsa nada matukar wahala_. ) Tarasa me zatayi burinta ya cika ganin da tayi dukiyoyin ta zai tafi a banza a wofi yasa tadawo bangaren kuma Hajiya Aliya,itadai islaha sosai yakema mahaifiyar tata nasiha sai dai da alamun kamar tayi nisa batajin kira domin a duk sa'ad da tamata fada ranar kwana take zaginta har ta waya take kiranta ta cimata mutumci,hakan be hana islaha yima mahaifiyar tata nasiha. Satin su Alhaji iliyasu uku suka dawo gida daga honeymoon din tare da murnar samun cikin Hajiya Aliya,bakaramin razana da gigita Adda Zainab tashiga ba domin har Suma tayi ta tayi tare da sumbatu,wanda hakan ya haifar mata da kwanciyar asibiti,hankalin yaranta yayi kololuwan tashi yayi,su Amma duk sunzo fada sosai Amma tayi mata akan wannan halin da tadauka tadorawa kanta, Ummie ma da Mommy da Mashahuda sunje,jin yanda Adda Zainab keta sumbatun Hajiya Aliya ta ci amanarta yasa duk jikinsu sanyi,sai dai ita a bangaren ta ba haka bane domin kuwa gani Ummie ba karamin wani tsanar ta takuma ji ba. ****** Sosai ta wahala da abortion din da tayi,dubara ce tafado musu,cikin sauri suka hanzarta komawa gida,inda Akeela tayi kace-kace da toilet da jini,a hanzarce su Hajiya dahara suka bar gidan,a cewar su yanda plan dinsu zai tafi yanda suke so,haka Akeela tayi faca da jini,takun Sauban tafaraji yanufo bedroom din nata,nanfa ta juyar da idanuwa tafara nishe nishen karya,a hanzarce ya nufota yana me tallafota izuwa jikinsa,kuka tafashe dashi tace"honey nayi miscarriage ka kallo jinin dake fita daga jikina....ai da hanzari Sauban ya dauke yafice da ita,dawowan sa kenan daga Kiran da Daddy yamusu shida Zuhra,inda aka samata tsauraran dokoki. Kaitsaye hospital din su Dr Ahmad ya nufa da ita,temakon gaggawa suka shiga bata,anan Dr Ahmad ke tabbatar ma da Sauban cewa lallai Akeela tayi miscarriage din cike na