Sashe 37
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata ba tarasa wanda zata aura sai Daddyn mu shine zata aura,ta biyun kuwa banda sauke ajiyan zuciya babu abinda takeyi tana rungume da bbyn ta,cikin muryan kuka Adda Zainab tace"nasani wallahi nasan Aliya ba hakanan tabar Alhaji ba,nasan halinta nasan abinda zata aikata,shedaniya ce. "Mom kenan sai yau ne kikasan da Aunty Aliya shedaniya ce?tun yaushe nake fada miki kinki yarda,aikinsan mugayen halayen ta tun ada,batare kuke aikata komai ba?sai yanzu data miki shine zaki dawo kifada haka akanta?takarisa maganar tana duban Adda Zainab,itadai shiru tayi ta cigaba dajan hawayen ta, Ammar ne yace"menene kike fada haka islaha?da wanne kiieso Mom taji?Yaya duk abinda nake fada nasani,itama Mom tasani kuma ita tagane karatun da nake nufi,wallahi akan Aunty Aliya har zaneni Mom ta ta6ayi daga nace ni zuciyata be kwanta da ita ba amma tarufe ido tamun duka tana cewa bazan raba zumuncin shekara da shekaru ba"ta ta6e baki sannan ta cigaba"kaga duk wani yake da faran dinda nake ma Aunty Aliya?inayi ne don kawai Mom kartayi fushi dani don akanta zata iya komai. Kuka Adda Zainab tafashe dashi tace"please islaha kiyi shiru haka,banson jin ko sunanta wallahi sai nadau mummunan mataki akan cin amanar da tayi min"islaha tace"hmmm Mom kenan kidai bi komai a hankali,cikin 6acin rai Adda Zainab tace"naki nabi komai a hankalin don abu kaza naki,wai dame kikeso naji ne islaha? Ammar yace"gaskiyan ta ne Mom babu wanda beson yanda kuke tare ba,wallahi yanda kike son ta ko Aunty bilkisou bakiso haka,duk fa munsan komai Mom,kin fifita ta akan duk wani dan uwanki,kawai Allah ya kyauta aikin gama ya gama don gobe ne daurin auren"yana gama fadar haka yabar bedroom din. Kuka sosai Adda Zainab keyi,su dai su islaha suna zaune jugum tare da tausayin uwar tasu. *** *GALADIMA FAMILY* *** Sauban dai yadanji sanyi a ransa jinda yama Akeela a matsayin budurwa sai dai ko kadan bayajin burbushin son,don ko irin tattalin nan da ake na mutum beyi ba da,sosai Akeela tasake jin wani irin son guy din ya ninku mata,sannan sosai ta yarda da cewa lallai tayi sa'a, lafiyayyen namijie ne wanda ko wace lafiyayyar mace take burin samu,lallai yasan sirrin sarrafa mace,sosai takejin ta cikin nishadi,bata farka ba sai wajen 11:16 bata sameshi a bedroom din ba,shikuwa yana mamakin yanda Akeela tazage tana masa abubuwa wadanda sam babu kunya a cikin su. Yana zaune tafito sanye da night gown,ganin sa yana daddana laptop yasa takariso a hankali tazauna kan rabin cinyar sa shafo gefen face dinsa tayi cikin muryan jan hankali tace"honey wallahi jiyan nan ka gajiyar nan dani don kawlai ni jaruma ce sam banda raki,da dai kamar bazaiyi magana ba sai zuwa can batare da yadubeta yace"sorry! Sosai Akeela taji dadi mikewa tayi da niyyar barin parlour,muryan shi tajiwo babu alamun wasa yace"A haka zaki fita saboda baki da hankali?juyowa tayi tapdubesa kamar bashi yayi maganar ba,cikin sanyin jiki tanufi bedroom dinsa,hijjab dinta ta dauka ta sanya sannan tafito tare da fita tabar apartment din,Suby ce takirata kan tanason zuwa,a take anan Akeela ta dakatar da ita kan cewa batanan yanzu zasu fita ita dashi,sallama sukayi dai-dai nan taja tsaki tace"yau nasamu babban nadau hutu ni kuma da komawa wannan harkan sai an kwana biyu. Acan gidan Galadima kuwa banda zazzaga ruwan rashin kunya babu abinda Mom keyi harta kaiga Baba Hasheem ya mareta tare da sanar da ita taje gida zai nemeta,sosai Mom ta gigita da wannan furucin nasa,sashin Galadima ta nufa cikin tashin hankali da kukan ta da komai. Duk hankalin mutanen gidan a ranar yatashi saboda yanda Baba hasheem ya rufe ido kan sai Mom ta tafi gida,sannan ya rantse da muddin bata tafi gida ba to saki ne zai biyo baya idan ta sake ko minti 20 ne,shi kanshi Daddy duk kokarin shi naganin ya shawo kan kanin nasa lamarin ya faskara,waya ya dauka yakira Abba tare da sanar dashi abinda ake ciki,inda yace yananan shigowa gobe da safe. Da kuka da komai Mom take sanar ma da hajiya Biba abinda yafaru,dogon tsaki hajiya Biba taja cikin fusata tace"wato ke ala dole ga 'yar bala'i ko?to wai ma rabi ina ruwanki da sha'anin gidan da har kika tsoma baki?koko ke kadaice mata a gidan? Mom tace"wallahi hajiya kaddara,ninaso ace Aseef ne ya aure Zuhra ba Sauban ba, saboda...sai kuma tasake karisawa,hajiya Biba tace"saboda ubanta nada kudi?wallahi Saboda haka ne yasa kikeson hada auren,rabi nasanki fa nasan halinki,nice nan na haifeki ba wani ba nasanki da bala'in son kudi to bari kiji koni da kika biyo akan wannan mummunan dabi'ar adace don kuwa yanzu nadaina na shiryu,Kinga Rammat? tayi magana tana nuna Rammat taccigaba"ina mata addu'ah kan Allah ya hadata da miji na gari me dan dai rufin asiri ko yaya ne wanda zai rikemin amanar ta domin Kinga nacire buri dason iyawa.Don haka shawarar da zanbaki kicanza hali rabi tun wuri in bahaka ba kinaji kina gani keda gidan GALADIMA family sai gani sai hange sannan kifadawa gidan wahala,a wannan marran,babu wanda bazaiso jininshi ya shiga gidan nan ba,duk akan maganar Aseef kika nemi kashe ma kanki aure,alhalin kinsan sa kinsan halayen sa wallahi Aseef ba kowa zaiso yabashi mata ba,a haka kamar mutumin arziki,kije ki bincika abinda yake aikatawa,kuma wallahi nida kaina zan sanar ma Taleeb komai kiji ma kisani,tana kare fadar hakn tajuya tashige bedroom dinta, Mom kuwa cike da nadama da danasani tafara laluban number Baba Hashim,sai dai ko dagawa ba yayi. Bayan sallar isha'i sai ga Ya Asher da Shuraim,kaitsaye sashen Daddy suka nufa don Daddy yasan da zuwar su a can suka cidda Sauban zaune,cikin girmamawa suka Isa parlour Daddy suna mika gaisuwa,duban Sauban ya Asher yayi yana me mika masa hannu yace"babban Yaya barka da dare,Ashe kana nanne?Sauban cikin kamewar sa yace"wallahi kuwa kwana biyu ya gida ya family? Asher yace"Alhamdulillah ya amarya?Sauban yace"amarya tana lafiya. Nan Shuraim shima yagaisa da Sauban,amsa masa Sauban yayi kamar wani abu baita6a faruwa ba. Kawo musu kayayyakin motsa baki akayi,duk da anyi-anyi suci amma sunki ci akan daga kan abincin ma suka fito, Daddy yace"Malam Asher abinda yasa na nemeka magana ce akan dan uwanka Malam Shuraim gashi!tare da mamana na wajen marigayi sadeeq,kasan alakar dake tsakanin su?Asher yace"Ea to Daddy kwanakin safeena ke fadamin,sannan take nuna min ai suna son junan su,sai nace to me ake jira basai magabata su shiga ba?sai take cemin ai sai ta gama degree dinta,sai nace to aje ko izinine a nema masa yasan anbashi saboda yanayin Shuraim ya nuna serious yake son ta,to nidai tundaga ranar bamu sake magana ba sai kuma dazu Shuraim yazo harda kukan shi. Bayan yakare magana Daddy yace"Malam Shuraim ya mana babban lefi a cikin family dinnan,wanda tunda muke ba'a ta6a mana makamancin sa ba,nafara kula yarinya kafin a nemi izini, ba don komai ba sai saboda gudun matsala"hakuri Asher da Shuraim suka shiga bawa Daddy. Daddy yace"No no no no aini everything will be gone cuz shine zamu bawa hakuri domin mamana akwai aure akanta.....ai wani irin zabura Shuraim yayi yamike tsaye,mouth dinsa yafara rawa,ko kafin yayi magana ruwan hawaye ya riga sirnano masa,kamar ba namiji ba. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi [6/30, 07:41] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 59/60 ______Dukawa yayi da rarrafe yakariso wajen Daddy tare da kama kafansa cikin muryan kuka yace"please please Daddy help me I love her so much,I can't live without her don Allah kada ku rabani da Zuhra rasata babban asara ne a rayuwa ta da nakasu,tana da wasu qualities wanda ba kowa ya sani ba sai wanda yake zaune da ita,naroke ka kamin duk hukuncin da zaka yimin amma banda na rabani da ita"yakarisa maganar yana wani irin kuka mai tsanani,sosai yabawa duk wanda ke parlour tausayi banda Sauban don wani mugun jin haushin yaron yake jiyake kamar yatashi ya rufeshi da duka sai dai face dinsa yagaza nuna hakan,baka isa ka fahimci mode nasa ba. Daddy yace"kayahakuri Malam Shuraim nace maka da auren wani akanta, Daddy kamin alfarma kahadani da wanda ya auretan na rokesa.Kamashi Daddy yayi ya zaunar dashi domin kuwa yayi bala'in basa tausayi matuka"Kunga irin shi ko,kunga dalilin da yasa muke fighting akan kafin afara neman yara a nemi izini, Zuhra tana aure da yayan ta Sauban"da sauri Shuraim ya maida duban sa ga Sauban wanda shima shi yake kallo,haka ya rarrafa wajen shi yana me kama hannayen sa cikin kuka yace"please Yaya don Allah kabarmin zuhra,domin don ni akayi t.....baikarisa ba sukaji Sauban yace"you re very stupid?re you mad?matar auren kake cewa don kai akayi ta?nima inason ta!yes I love her!bude baki yayi zai sake magana amma sai yakasa kawai sai ya girgiza kanshi yafita daga parlour. Dafa kafadansa Daddy yayi yace"kayahakuri kaji ba'a aure akan aure,sai dai temako daya zan maka kaje kasamu natsuwa idan komai yawuce sai kazo ina son ganinka,kamashi Asher yayi yace"babu komai Daddy Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,a'iya sanin da nayiwa su Daddy Shuraim da babu aure akanta Allah sai sun baka ita,gabadaya ko matsawa Shuraim yakasa a ransa kuwa fadi yake _Yanzu shikenan dama bashi ne yake da rabon mallakar zuhra ba?_ ganin da Daddy p yayi kamar ma yaron baya a hayyacinsa yasa ya kamasa ya mikar dashi da kanshi yarikeshi suka fito har parlour, Sauban na zaune a gefen Ammi,suma fitowa sukayi dai-dai lokacin ZUHRA sun shigo dasu Laila,idanuwan su ne suka shiga na juna,atake anan zuhra jikinta yadauki rawa,shikuwa Shuraim hawaye kawai yakeyi,cikin tsananin sauri hade da gudu zuhra ta juya tabar apartment din,kokarin binta Shuraim yakeyi sai dai rikon da ya Asher shima ya masa ya hanasa bintan. Duk wanda ke parlour sai da suka basu tausayi harta shikanshi Sauban din,daqyar Daddy ya lallabashi suka tafi a mota kuwa ko magana ya kasa lokaci daya zazza6i ya rufeshi,wajen 9:26 pm suka isa gidan su Shuraim din.