← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 64

Sashe 14

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai dafa duk taurin nama?ki rufamin asiri kinsan kuwa aikin dangudelle na yarda dashi na yarda da aikinsa,saboda shidin shedani neeeee takarisa maganar tana wani rimi dolen dole na hada zuri'ah da Galadima da wannan makirar tsohuwan Bodejo,inaso na bawa Laure mamaki tasan cewa ni nafita hatsabiban ci wallahi dani take zancen. Duban Rammat tayi wacce take kukan cikin takaici tace"dallah ke kimin shiru,sai kace kema din ba mace ba?yanzu ke ba zaki iya jawo hankalin yaronnan gareki ba?meye amfanin macen da bata iya kissa ba kwata n ta? hajiya Biba takarisa zancen tana huci tare da babban kada hanci. "Hmmm aini Rammat wani takaici take bani hajiya,ga Akeela nan tanaji tana gani zata kwace mata shi. Dan bata face Rammat tayi"Kai Aunty fatan tsiya haka? Wani hararan Mom ta galla mata tare da mikewa ta dauki jakar ta duban hajiya Biba tayi"Hajiya zantafi bnson baban Aseef yadawo yaga bana a gida,Kinga ba'asan na fita ba. Hajiya Biba tace"shikenan sai munyi waya,nan sukayi sallama tafita a ranta da qudurori kalakala,don ta dauki alwashin koda Rammat zata mutu ba zata yarda ta aure Sauban ba. **** **** **** Zaune take a cikin class din suna sauraren lecturer din English don da abinda aka fara tarbansu kenan sosai ta maida hankalinta akan lecture dinda ake musu,sanye take da Arabian gown coffee tayi rolling viel din sosai tayi kyau fatanta kalar half-caste yasake bayyana,duk da sanye take da facemask amma sosai taja hankalin 'yan class din. Yadauki tsawon 20minutes yana musu bayani sannan yafita anan wani lecturer din yashigo yadauki 10 minute's kana yafita,na ukun ne yadauke fifteen minutes kuma daganan wajejen 11:30 suka fito daga lectures gabadaya, student's da dama sun sami bakin department dinnasu suna hira wasu na introducing kansu ga juna saboda asaba. Zuhra kuwa kaitsaye gate tanufa don tafiya gida,tare da wasu daliban da qyar tasamu napep tahau dropped yakaita gida,cike da gajiya ta shiga gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa. Moryoyi ta fara jiyowa na 'yan mata koda tashiga parlon Aunty muneefa ne da Akeela,kan dinning kuma Aunty Mashahuda. Cike da fari'a muneefa tace"A'ah students,yau UNIMAID sunyi sababbin dalibai. Dan murmushi kawai Zuhra tayi tana karisawa wajen Mashahuda dake dinning,itama cike da zolaya tace"Wai yau 'yar gidan Ammi akwai rigima. "Kai Aunty Mashahuda nifa ban gaji ba,dudu lecture's uku mukayi muka fito, takarisa maganar cikin shagwaba. Ammi da saukowan ta kenan daga stairs tace"toh mene idan anmata tausar si auta ce,duk gidan nan itace auta yimata shine zaman lafiya. Cike da tsananin jin nauyin Ammin zuhra ta duqar da Kai tana murmushi,dariya mashahuda ta saki tace"Ammi kinga zuhra wai kejin nauyinki. Murmushi Ammi tayi dai-dai nan wayanta yasoma neman agaji, duban number tayi tare da sakin murmushi tayi picking. "Assalamu alaikum Son. Daga can bangaren Sauban ya lumshe ido cikin tsananin son Ammi yace"Sweetheart barka da rana. Murmushi kwance akan fuskanta tace"barka dai yakake ya aiki? Alhamdulillah Sweatheart jiya inata kiran number dinki yaqi shiga na Daddy ma haka nakira na Mash'huda kuma number busy tanata waya. Ammi tayi dariya me sauti tace"itada taufeeq ne nasani to ya aikin? Alhamdulillah,nima I think nanda sati biyu zan shigo zarian saboda branch dinmu na Abuja zanje naduba. Cikin jindadi Ammi tace"Masha Allah son Allah yakawo min kai lafiya cikin aminci da yardarsa. Cike da jin dadin addu'an ta ya lumshe ido yace"Ameen Sweatheart yasu Mom? don nayi waya dasu Bodejo. Ammi tace"lafiya lou Mom dinku ya kamata kkrata koh? "Ea Insha Allah haka za'ayi. Kana waya dasu Ummien naku da Abbie? Dariya mai sauti Sauban yayi wanda inba Ammi ko su Ummie dasu Bodejo ba bame ganin irinta yace. "Ahhhh kaji Sweatheart sosai ma muna waya dasu. "Yawwa son haka akeso Allah yamaka albarka. "Ameen Ammi sai anjima a gaida yaran gidan. "To Shikenan tafada tana me zare wayar daga kunnenta. Cike da zumudi muneefa da Mashahuda ke tambayar ta ya tambayesu? Ammi tace"kowa ma ya tambaya ya kuma ce a gaida kowa don nanda sati biyu zaishigo kasar. Akeela kuwa wani kululin bakin ciki dana takaici ne suka dirar mata ganin ko damuwa bai nunawa akan ta,kamar ma yamance da ranar wata akansa,hakan yasa cikin bacin rai ta tattara kwamatsanta tabar parlon,babu wanda ya lura da ita sai Zuhra,sai dai ita hakan ko a gyalen ta dan tabe mouth ma tayi. *BAYAN SATI DAYA* Zuhra ce zaune da ita da Shuraim suna hira cike da nishadi don Allah yabawa Shuraim nasarar samun Zuhra don sosai ta sake mishi. Cikin muryan dariya tace"Yaya to idan kasamu balarabiya bazaka iya auren ta ba? "Hmmm yarinya bazaki gane ba,nifa yarinyar da nakeso ko a larabawan ba lalai a masu mai kyanta da quality dinta ba,kedai kibari wataran zaki ganta. Cike da shagwaba Zuhra tace"Lallai ma yayan nan naqi wayon,kawai dai kasa ma mana lokaci wataran kakaini naganta. Zuhra tace"To shikenan Allah ya kaimu. Da Ameen ya amsa yana mejin wani nishadi a ransa na yanda yaga yarinyar tayi bala'in sake masa. Baba Mudi ne ya bude gate saboda horn din da aketa dokawa,ko gama bude gate din beyi ba aka shigo da motar a zafafe, cikin bacin rai ya balle murfin motar ya fito kaitsaye wajen Baba Mudi ya nufa,cikin rashin da'a yafara magana. "Meyasa kake hakane tsohon nan?tunda nataso a gidan nan kai nake ganin matsayin me gadi gashi karfinka yafara karewa,don Allah katafi kabawa me jini a jika shima daman shigowa ya daddale arziqi mana, mtsewwww. Yaja tsaki,shigo Baba mudi girgiza kai kawai yayi a zafafe ya nufi apartment dinsu. Dan siririn tsaki zuhra taja. "Yayadai?shikuma wancen wanene? Zuhra tace"Hmmm barshi cousin dina ne haka yake duk gidannan shine Mara da'a shine wanda baiganin darajar talaka. "Allah yakyauta ubangiji Kuma ya shiryeshi,da Ameen zuhra ta amsa,anan suka cigaba da hirarsu. "Mom Wai dagaske ne?nifa bansamu labari ba sai shekaran jiya dana ga pic dinshi a IG yanda 'yan mata keta rushing akansa har fada wasu sunayi,baya kasarnan to waya sama masa aiki? Mom tace"bansani ba,hmmm burika na biyu basu cika ba don haka bazanyi sake shima na ukun yaqi cika ba. Aseef yace"wasu burika kenan? Mom tace"naso ace ko Sauban ko taufeeq daya a ciki ya aure Muneefa amma gabadaya babu wanda yasamu,abin bakin cika wai Sauban yafika,nifa bana fatan rayuwar wanda zaifi dana ko wanene shi,shiyasa kota halin kaka sai ka aure Zuhra,takarisa maganar tana wani huci. Wani irin sanyin dadi Aseef yaji a ransa. "Ga sa ranar auren sa da akayi kasani ai koh? "Nasani Mom sai dai hakan bedameni ba don sanin wacce zai aura ba kowa bace face bunsura,ai mom idan Sauban ya aure akeey beb ai yaci baya. Mom tace"Toh meya shafeka da cin bayansa?idan yaso ma yaci uban baya,don kullum ni burina kenan dan iskan yaro. Sallama Baba Hasheem yayi ya shigo. Amsawa sukayi nan suka fara yimasa sannu da zuwa,sosai baba hasheem yaji dadin ganin Aseef"A'ah mutanen kaduna yaushe Kuma aka iso? Dan sosa kai Aseef yayi yace"wallahi Baba yanzu bandane da shigowa ba. "Ok to ya kabarsu Kuma? "Lafiya lou wallahi Baba,dama nace Bari nazo na duba ku kwana biyu bamu shigo ba. "Kashiga wajen su Galadima? "A'ah yanzu zanshiga dai. Alhaji kenan to inbanda abinka zaiki shiga ne?dole dai yafara gaisheni tunda nice na haifi abina. "Gaskiya ne wannan,abinda Baba Hasheem yafada kenan yamike yashige corridor din bedroom dinsa. Cikin farin ciki Aseef ya dubi Mom "Please Mom da gaske zan aure zuhra saboda gaskiya yarinyar tayi kota ina! Mom tace"na taba maka wasa ne Aseef? Girgiza kai yayi da sauri. ******** "Kai gaskiya naji dadi Allah yama Bashir albarka ubangiji yasake hada kawunan su, Bodejo ke mgn. Daddy face dinshi dauke da murmushi yace"Ameen ai gabadaya kayan na 15 millions ne yahada musu babu abinda bai siya musu ba har kayan kitchen. Baba hasheem yace"Allah dai yasaka ma Yaya da alkhairi. Da Ameen gabadaya suka amsa, Galadima yace. "To yaushe zasu dawo? Daddy yace"insha Allah yace"kaitsaye ma gobe nan zai iso don yanason ganin Zuhra. Dariya Bodejo tayi tace"Kai sadeeq na sangarta yarinyar nan matuka. Dariya duk aka sanya. Washegari wajejen bayan magrib Daddy ne da Ammi ke zaune sunayin lunch,wayar Daddy ya nemi neman agaji,da sauri ya dauka Yana murmushi saboda sunan Abbie da yagani,sallama yayi. Nan aka fara magana tacan bangaren. "Eah nine lafiya kuwa?Ina me wayar yake ne?daga can bangaren aka sake magana. A gigice Daddy yamike yana furta" _INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN_,Ammi ma mikewa tayi tana Daddyn yara lafiya kuwa? "Sadeeq!Sadeeq!! Aisha Sadeeq yayi hatsari shida bilkisou. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un a lokacin ne Baba Hasheem yashigo shima apartment din Daddy cikin rudu"Yaya!Yaya!! Dagaske ne? Wani yunkurawa Daddy yayi cikin jarumta ya nufo Baba Hasheem,Kama hannunshi yayi. _YANZU FA WASAN ZAI FARA MASOYA GALADIMA FAMILY_ Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 13/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 19/20 _____A gigice suka nufi apartment din Galadima a dai-dai nan wayar Daddy yafara ringing, cikin rudewa ya dauki wayar,daga can bangaren aka fara magana. "Alhaji Taufeeq majinyacin yana cikin wani hali don sai sunan ka yake ambata yana cewa kazo. Bakin Daddy yana rawa ya dubi Baba Hasheem yace"Hashim mutafi asibitin ko kasan ko wane asibiti ne? Baba Hashim yace"sun sanar dani muje kawai nan suka nufi motar Baba Hashim. Tsananin rudewa kuwa Mashahuda tashiga don duk abinda ke faruwa akan idon tane da tsananin gigita tashiga apartment din Bodejo tana Kiran sunanta. Bodejo dake zaune tana shafama Galadima man zafi a kafa ta dago tana cewa"ke kuwa Mashahuda wani irin Kira ne kikeyimin haka mai gigitar wa? A rude takariso tara da durqushewa a gabansu tana sauke numfashi akai-akai. "Bodejo Daddy sun tafi asibiti yanzu aka kira a waya Abbie da Ummie sunyi accident a hanyarsu ta tahowa daga airport. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wane Abbie din? Bodejo tayi maganar tana gyara zanin ta da yake neman sabulewa. Galadima yace"natsu Mashahuda kiyimana bayani. Nan Mashahuda ta sanar musu da duk abinda ke faruwa a lokacin ne Kuma Ammi, Mom,muneefa da yaseer suka shigo parlon. Cikin muryan tsawa Ammi tace"menene haka Mashahuda waya aikoki?haka ake fadan sako. Daga musu hannu Galadima yayi cikin muryan dattaku yace"duk ku zazzauna. "Innalillahi wa
Chapter 14 · 0% Book details