← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yau ta kama Friday kamu aka shirya guda narwa a Galadima family,amare sunyi kyau matuka gaya,anan ne su Aunty Maryam suka tura su Laila gidan su Akeela akaimata kayan kamun,don dama an amsa majorment nata,Anko sukayi su uku inda,angwayen ma sukayi ankon arniyar danyen shadda sky blue,su kuma amaren net ne sky blue su Aunty labeeba suka musu dinkunan.
Wajen ya kawatu matukar kawatuwa,baka tatan su Suby suka tsinta maganar don su sun zata zasuyi abinsu daban ne,abinka da waje babba fili ne dake bayan gidan Galadima wanda yake mallakinsa,an katangeshi tare da zuba interlock da shuke shuke,lokaci guda masu decoration suka canza masa kamanni yakara wani masifar kyau da tsaruwa,kawayen Akeela da 'yan uwanta guda goma aka bukata,kamar yanda aka bukaci na ma'aruf saurayin muneefa,sukuwa sauran abinka da abu nasu ba'a maganar 'yan uwa,su Suby suma sunyi shigansu na tatattun 'yan duniya itada Zuleey anko sukayi.
Waje fa ya hadu ya tsaru matuka gaya babu abinda kakeji na tashi sai sautin kidan wakar namej me taken "dama".
*****
Kwance take akan gadon Ummien sam bata da alamun tashi ta shirya balle ayi maganar fita,su nihal sunyi maganar har sungaji sun wuce tare da wasu cousin's dinsu agemate, Ummie ce tashigo tana sanye da wata lace maroon tayi matukar kyau face nata dauke da tsantsar fari'a,turus tayi taja tatsaya tana duban ZUHRA cike da mamaki tace"Zuhra zaman me kikeyi anan?kowa yanacan yana watsa idanuwan ganinki ke kina nan kina kwance.Turu mouth gaba tayi tace"Ummie kaina na ciwo ne shiyasa ma banfita ba kuma bazanje ba,takarisa maganar tana sake gyara kwanciyar ta"Lallai to wallahi baki isa ba shashancin banza,yayanki sai kirana yake akan be ganki ba ke kuma kinzo kinrashe?maza
kitashi ki shirya kiwuce tun kafin raina yabaci,haba babyn Ummie kinaso ki batama sweat broo din naki rai ne ranar farin cikinsa?
Girgiza kai Zuhra tayi tana me mikewa badon ranta yaso ba,nan Ummie ta cigaba da lallabata da lallashinta don ta fahimci tunda bikin gidan yakarato take cikin kunci da damuwa,a gurguje tafito ta shirya cikin wani hadadden yadin rose white sai net dinsa wanda Ameer ya zauna ya tsattsafa mata wani street gown me daukan magana,abinka dame kirar cikakkiyar halitta,shape dinta yayi balai'n fita,light make-up tama kanta,tashirya tayi matukar kyau,takalmin high heel shoe me siraran igiya tasanya a 'yar karamar kafanta wanda yaji jan lallen salatep,fitowa tayi cikin takunta me daukan hankali,nan tanufi sashin taron,duk da kowa zaune yake a mazaunin sa amma shigowan ta yasa da yawa hankulan su ya koma kanta,haka abokan angwaye ma, half-caste skin dinta shima yasamu damar sake fito mata da ainahin kyanta,kananun magana ne yadan fara tashi.
Akeela kuwa ganin Zuhra ba karamin baci taji zuciyar ta tayi ba,jitayi kamar ta tashi ta shaqe ta don wallahi ita kanta da take amarya tasan yarinyar tayi bala'in finta kyau nesa bama kusa ba,wani banza kallo tashiga aika mata dashi zuciyar ta na tsananin tatarfasa, Zuhra kuwa ko kallon inda amare da angwaye suke batayi ba babu zato taji sallama ta gefen kujeran da take zaune,duk da kujeru uku ne table a tsakiya amma ita kadaice,dagowa tayi don jin muryar sa,murmushi suka sakin ma juna one time,da ido ya mata alama da ya zauna?cikin cool nd sexy voice dinta kamar me rada tace"yep have a sit,murmushi suka sake sakinma juna,shima yayi kyau sosai Shuraim don babban rigan ta masa kyau gaya.
Wani bacin rai yake tsintar kansa a ciki amma haka yaketa dannewa har aka fara Kiran angwaye da amare su fito suyi rawa,duk da a takure yake jinsa sai dai hakanan yadaure yakamo hannunta suka sauko suma filin,dai-dai yadago idanunsa itama ta dago,ido cikin ido yasan ya mata musamman ganin yanda take hira cikin nishadi da kwanciyar hankali,basarwa tayi ta hanyar dena duban ta tana sake maida hankalinta ga Shuraim dake ta bata dariya.
Tunowa tqyi da Taufeeq cikin hantsari ta dubi Shuraim,excuse me! just give me five minute"daga mata kai yayi masu ma amare manni sun ragu,a dai dai lokacin da aka saki sautin wakar "luwaiiii" na Ado gwanja,tafiya tafara tana karkada jikinta cike da jan aji da basarwa tabude pos dinta ta ciro 'yan dubu-dubun da Daddy yabata tafara manni,aiko nan aka saki tafi tare da shewa,rike hannunta Taufeeq yayi suna rawar cike da natsuwa tare,ai nan danan Nihal da Laila suma suka fito,sun burge mutane da dama,don shi kanshi ya Sauban sun matukar burgesa.
Akeela kuwa face dinnan ansake cureshi lokaci guda,kafin kace me se ga abokan Sauban da suka zo daga abroad suma suna zubama Taufeeq da Zuhra manni,shima Shuraim tasowan yayi, Aunty safna ma haka tare dasu Aunty Maryam,su kansu amaren ba'a barsu a baya ba, Akeela kuwa zuciyar ta jitake kamar zata buga tsaban bakin ciki.
Haka atashi taro lami lafiya aka gama kowa na farin ciki wasu kuma akasinsa.
Chapter 28 · 0% Book details