← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 64

Sashe 11

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____Au yau akasaka ranar?tayi tambayar fuskarta dauke da murmushi iya labba. Baba Hasheem yace"Eah yau akasa wata takwas muka sanya saboda yanzu za'a fara aikin so sai yaga kamun ludayin aikin,idanma komai yayi normal before lokacin so za'a iya dawo da ranar baya insha Allah. "Kai! Mom tafada wanda sam batayi zaton bakinta ya furta hakan ba,dubanta Baba Hasheem yayi yace"Kai mene kuma Rabi? Da sauri ta wayance ta hanyar sakin wani kayataccen murmushi yace"Hmmm kasan kuwa irin tsananin farin cikin da nayi?wallahi na taya maimuna murna da samun siriki irin Sauban. Wani murmushin jin dadi Baba Hasheem yayi"Tabbas kuwa don Sauban yaro ne wanda kuwa zaiyi sha'awar sa. Mom tasaki murmushi tace"Aikuwa! Zuhra tarasa inda zata saka ranta tsananin murnan ganin Abbie din nata bodejo ta tabe baki tace"Gaskiya Sadeeq duk kabi ka shagwaba yarinyar nan tare da sangarta ta. Dariya Abbie yayi"Bodejo to yaza'ayi? "Abbie kataso kaci abinci tundazu nahada maka lunch saboda nasanka da son cake da meat pie shiyasa namaka sannan na dama maka kunun gyada,takarisa maganar tana kama hannun Abbie din. Murmushi yayi tare da mikewa kai tsaye suka nufi dinning room. Tabe baki bodejo tayi"uhm uhummm tafurta. Dan dariya Galadima yayi yace"hajiya bodejo duk kishin ne haka? Bodejo tace"wane kishi zanyi kawai sai nahau yin kishi saboda wancan kwailar?takarisa maganar tana nuna zuhra. Itadai Zuhra akaikaice tasakin ma bodejo gwalo. *KADUNA JABI ROAD* "Lallai Bilkisou sai yau nasake tabbatar da baki da hankali gabadaya kin wofantar da diyarki ta karfi da yaji kinmaida ita abokiyar gabanki?yarinyar ki nutsattsiya karfi da yaji kinmaida ta marainiya?meye lefinta?itace tace a sanya mata sunan surukarki?ke kanki ba sunan mahaifiyar ubanki kikaci ba? To bari kiji wallahi wallahi ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba,yarinyar nan ko wajenmu baki kawota sam Fateema batasan niba yanzu ke kin kyauta?ke ba abin kunyarki bace ace 'yarki batasan gidanku ba?sai dai tadinga ganina a photo?tsaban hankali irin na yarinyar nan har kirana take a waya. Narantse da Allah Bilkisou fateeman ma tafiki hankali,har mahaifinki ya rasu da bakin cikin abin nan yatafi. Duk da kinkasance mai biyayya amma akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa...... Takarisa fashewa da kuka cikin takaici. "Mtsewwww ai wallahi Amma kinma mata da sauki da yacce tayi watsi da diyarta,kekuma kiyafeta a cikin 'yayanki.... Da sauri Ummie tadago tana duban yayanta Aunty Zainab tace"Haba Aunty mezesa kicewa Amma haka?kunsan kuwa irin zafin da nakeji a cikin zuciya ta?wallahi inajin sonta da kaunar sai dai tsanar da nake mata ya danne sonta da nake mata. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Bilkisou dinyar taki kike cewa kike tsana?lallai. Zainab tashi muje wallahi wallahi Bilkisou muddin baki kaunace diyarki ba All....da sauri Ummie ta rufe bakin Amma tana girgiza kai hawaye na tsiyayo mata. Fincike bakinta Amma tayi sannan tamike tadubi Aunty Zainab tace"Zainab tashi muje. Gyara mayafin gyalenta tayi tadauki jakanta sannan suka fita,Ummie tabiyo bayansu da sauri tana kiran sunan Amma dana Aunty Zainab Amma ko waige. Daidai nan Taufeeq yashigo a gigice yasamu daya daga cikin sofa din yazauna tare da duban Ummie yace. "Ummie meke faruwa ne?Kinga yadda Amma tafita tana kuka nagaishesu amma bata amsa ba infact ma ko tsayawa batayi ba Adda Zainab ce tatsaya muka gaisa. "Ummie nasan dama bazaki bani answer ba amma nasan akan maganar Zuhra ne hakan ke faruwa,wallahi Allah yasani koni banjin dadin abinda kike mata haba Ummie kamar bakece kika haife zuhra b..... "Tasssss!karar mari yafito. Ummie ce ta zabgama Taufeeq marin tana huci tare da nunasa da yatsa alamun gargadi tace"Tashi kafita. Sakin baki Taufeeq yayi yana duban Ummie cike da mamaki don tunda yake a rayuwa ko dunguri Ummie bata taba yimishi ba. "Kana mamaki ne?tashi kafita nace kafin nakuma yarfa maka wani marin. Mikewa yayi tare da duban ta yace"Allah yahuci zuciyar ki Ummie. Wani banzan kallo ta watsa masa. Sum sum Yaya Taufeeq yafice daga parlon. *BAYAN KWANA BIYAR* Ayau ne Sauban jirginsa yadaga sai kasar maleyshia. Bayan tafiyarshi da kwana biyu aka bashi aiki matsayin M.D na company,wadanda hada takalma sukeyi,sannan aka bashi gida hadadde Wanda ya kawatu matuka babu abinda babu a gidan,sannan anbashi mota kirar Benz G-Wagon tabbas duk wani masoyin Sauban yaji labarin nan dole yatayasa murna. Ranar monday shine ranar da yafara fita daga office babu abinda kakeji sai sautin tas tas tas tas sautin karar covershoe dinsa ne.Sosai ayau din kensa yasake fitowa na jinin shuwaarab da kuma buzaye,pink lips dinsa gunin sha'awa,sajen nan nasa yakwanta sai sheqi yake kamar balarabe gashin kansa baki sidik gunin ban sha'awa duk da cewa Ya Sauban ba fari bane amma yana da wata irin kyakkyawan fata irin na Zuhra wato half-caste haka colour nasu yake. Sanye yake da designer suit kirar company Gucci black colour,agogon dake daure a hannunsa Kuma Cartier. Hannayensa riqe da wayoyinsa guda biyu iPhone 11pro da iPhone 13 pro max. Kaitsaye inda motarsa take kirar Benz G-Wagon yanufa da sauri driver din yafito tare da bude masa bangaren back seat,dan rissinawa driver yayi tare da cewa. "Good morning sir! "Morning David hope everythig is Ok? "Yes Sir,David ya amsa dashi yana me yaba kyan da ogan nasa yayi a ransa. Bangaren driver David yashiga tare da tada motar,gate Man ne ya wangale musu gate din kaitsaye David yacilla motar kan kwaltan dake area din. ********** "Ranka yadade dangudelle haba taya zan raina aikinka nida nasanka kasanni shekaru 28 kenan munatare tabbas nasan aikinka yana kyau shiyasa ma koda yaushe nakeda yaqini agareka sam bana wasiwasi akan aikinka. "Hahahahahahahaha! Aka saki dariyar cikin wani murya marar dadi wanda gabadaya sai da sautin dariyar ya amsa dajin,itakuwa Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi saboda tayi tasananin tsorata. "Biba kenan nasan abinda yakawoki nakuma san abinda yake tafe dake,yayi maganar cikin wata irin murya marar dadi. "Hahahahaha wannan yaron dakikeson hada 'yarki dashi tabbas hatsabibi ne don kuwa sam baya wasa da azkar,sannan ita yarinyar da akeson yanzu a hadashi aure da ita ba sonta yakeyi ba sai dai tabbas daga baya zaisota ta hanyar asirii....hahahahaha" Yakarisa maganar yana sakin wannan dariyar nasa da muryansa marar dadin ji. "Hmmm dangudelle nasani nasan komai so nake kamun aiki akansa ya birkice akan maganar aurensa da wancan kodaddiyar yarinyar,ajuyar da akalar maganar kan Rammat,don idan har Rammat bazata sameshi ba to itama Akeela bana fatan tasameshi. Wani irin kallo dangudelle yayiwa Biba tare da sakin wani dariya,zuwa can yatsuke fuska yace"tirkashi aiko bazai yuwuba sai dai suyi zaman kishi tare saboda wannan tsohuwar tsaye take akansa don so take da bala'i su mallake yaron. Share gumi Biba tayi tace"nikam yaza'ayi kenan?tabbas Biba itama saita shiga gidan idan yaso daga baya takoreta. Wani dariyan boka dangudelle yasanya yace"lallai yaron dangata ne don a kaddararsa yanuna daga baya da mace daya zaiyi rayuwa tare da yimata wani irin mahaukacin so,don ko ayanzu yana sonta. Dafe kirji Biba tayi cikin tsananin rudewa tace"wacece wannan yarinyar? "Bansanta ba!duk iya kokarina naganin gano yarinyar nakasa amma tabbas itace matarsa uwar 'yayansa,boka dangudelle yakarasa maganar yana diddilo da idanuwa waje. Itadai Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi dukda kuwa yanda takejin daci aranta saboda ta tsani Sauban tun randa ta haifi a namiji, saboda yanda Sauban keda kwarjini da farin jinin jama'a sam danta baidashi wannan dalilin ne yasa daga ita har Aseef din suka tsane Sauban. Biba tace"dangudelle so nake duk halin da ake ciki Sauban yafada tarkon son Rammat. "Hahahaha....Ke shedaniya! tabbas kinsan zan iya zanyi abinda yafi haka,yayi maganar yana jawo wani kwarya wanda babu komai sai toka yafara cakuda garin tokan da hannu,cike da al'ajabi hoton Sauban ya bayyana yana zaune a office dinsa. "Hahahaha.. dangudelle yasake sakin wata dariyar yace"Zoki ganshi tabbas yaron yasamu daula. Jikin hajiya Biba dana Mom har rawa yakeyi."Aiko tabbas Sauban ne hajiya,hajiya kinga wani irin office dayake zaune a cikinsa? Kafin hajiya Biba tayi magana dangudelle yadaga hannu tare da shafe tokar,nan take hoton ya bace. "Kutashi kuje tabbas zakuji sakamako mai dadi don yanzu haka na wada da dantsaka da lituwa suna hanyar dawowa daga masar kawon saqo kuje na sallameku". Hajiya Biba na shirin magana kenan dangudelle yabace bat,dole suka mike badon sunso ba kowacce da abinda take saqawa a ranta don Mom ita inda dayanda za'ayi kashe mata Sauban kawai za'ayi. _________**________ Yauma kamar kullum tashinta kenan dai karfe hudu a dalilin wani mummunan mafarki da tayi wai anyi rasuwa ga mutane nan cike a Galadima fam sai dai bataga gawar ba sosai hankalinta yayi kololuwan tashi,koda tamike bathroom tashige tadauro alwala tafito tare da shimfida praymat tatada sallah. Koda ta idar lokacin anfara kiraye-kirayen sallar farko,sosai tayi addu'ah. Tadauki tsawon mintuna tana lazimi zuwa can aka tayar da sallar asuba don haka sai itama tamike tatada sallar. Acan gidan Guggo Laure kuwa Akeela ce ta tasata agaba wai ranar da akasanya yayi tsayi da yawa ai 'yan kauye ne kecika ranar aure ita gaskiya a rage. Guggo Laure kuwa sai lallashinta takeyi takuma tabbatar mata da cewa suna zaune ma Sauban din da kanshi zaizo yana neman alfarmar a rage. Dan yatsine face Akeela tayi cike da rashin jin dadi a ranta tace"Ni Guggo ina tsananin kishin sa ne wani irin zazzafan so nake masa,wallahi nida da yanda zanyi kan kada yaso ko wacce mace zanyi saboda ina tsananin kishin sa. Dariya Guggo Laure tayi"mekike ci nabaka nazuba 'yannan?kisa a ranki zai soki kedai kidage da kissa da kisisina sannan ki tabbatar da kin jawosa a jiki ya zamana babu macen da yake gani a matsayin mace saike. Dariya Akeela tayi tace"yanda kikajin nan Guggo kuwa sai dai nayi tsananin yarda dasu Suby su kansu zasu tayani shawo kansa. Mere baki Guggo Laure tayi"Hmmm kesam bakisan sharrin kawaye ba koh?ina gargadinki Akeela amma sam bakiji. "Wallahi Guggo basu da matsala don kawai bakisan su bane domin duk suna tsananin sona wallahi. Murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaro yaro ne to shikenan Allah ya kyauta. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 25/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 13/14 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______Ummie abin duniya duk yataru ya mata yawa taje wajan Amma don
Chapter 11 · 0% Book details