Sashe 44
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
din,ita kuwa Zuhra jingina tayi a jikin kofan tana dafe da kirjinta,sosai wani irin tsoron sa ya shigeta,kaitsaye toilet ta nufa ta dauro alwala, alqur'anin dake kan bedside drower dinta tadauka tafara karanta suratul Muhammad,bayan ta gama ta karanta Suratul mulk wanda hakan yazama al'adar ta, addu'o'i tayi sannan taja blancket,bata wani jima ba sai bacci. Shikuwa Sauban koda ya koma shima Shirin bacci yayi bayan yayi addu'o'in sa sannan ya kwanta,kokarin bacci yake,Amma baccin yaki zuwa da ya runtse ido face din yarinyar yake gani"Oh my God, Sauban wat's wrong with you?yarinya karama ce fa, she's still young fa,idan ina lissafi dai-dai yarinyar nan zatayi 19?So why not am thinking about her?huh ya rabb,I know am not loving her"yayi maganar yana runtse ido da kyar bacci yayi awon gaba da shi. ******** Washegari kuwa duk sunje asibiti 'yan gidan Kama daga kan yara har manya,motoci biyar sukayi,ko wacce number mota sai kaga sunan G FAMILY muddin suka wuce ansan sune sai an daga musu hannu saboda temakon tsohon,wanda labarin laruran da yasamu har ya watsu a gari,mutane da dama na masa fatan samun sauki, Bodejo sosai take kuka a lokacin wajen 8:30 su Daddy da Abba ne zasu tafi kasar Malaysia da Galadima cikin muryan kuka Bodejo tace"haba Laure me Galadima yayi miki da ya cancan ci hakan daga gareki?mutum ne me kaunar ki tare da tsananin son ki amma akan jika kikayi sanadiyyar zamowan sa haka,meyasa?tayi maganar tana fadawa jikin Daddy, Daddy, Abba, Baba Hasheem duk rungume ta sukayi suma tana kokarin sasu kuka,sallama su Aunty labeeba sukayi,kaitsaye suna nufar gadon Galadima,suma kukan suka sanya suna fadawa jikinsa,wannan dalilin yayi sanadiyyar tashin sa. Shima hawayen ne ke zuba kawai a idon sa,komai baya motsi sai kwayan idon sa yana murmushi,duk nufar sa sukayi, Aunty Maryam cikin muryan kuka tace"Bodejo me yasame shi hakan?mun tafi min barshi lafiya lou, meyafaru? Bodejo cikin muryan kuka tace"kaddara mairo komai ya faru mukaddari ne sai dai da sanadi. Galadima kuwa kura ma Zuhra Ido yayi duk da murmushin nasa ba kowa ke ganewa ba amma angane,sannan yamai da duban sa ga Sauban yana murmushin,alama ya musu da kai dasu zo,don bakinsa babu halin magana,karasawa sukayi garesa,murmushi yayi yana girgiza kai alamun yana jin dadi. Dr Ahmad ne ya shigo tare da wasu doctor's din, duban Daddy yayi"Alhaji Taleeb lokacin wucewan ku yayi yanzu 9:00,duk juyowa sukayi hankalun su nadawo wa kanshi,wani daga cikin Dr din yace"sunana Dr Amjad Aliyu tare dani zamu tafi"nan kuwa suka fara shirye-shiryen su,gabadaya shisshiga motan sukayi don rakasu airport,goma saura minti 7 suka isa airport din,nan Sauban da Taufeeq sai Abba suka shiga ciki don tayasu kimtse kimtse na visa da sauran su dama already anyi. Karfe 10:40 aka fara sanarwan passengers,sosai Bodejo dasu Aunty Maryam ke kuka, Ammi da Ummie ma haka,sai Mommy da Mom ne suka koma rarrashi,sai da sukaga tashin jirginsu sannan suka nufi wajen motocin su,hannun ta taji an kamo a tsorace ta juya,kamar ba shine riqe da hannun nata ba don fuskewa yayi gabadaya,ita kuwa Zuhra a tsorace take tsananin kunya ya kamata,ga fargaban kada wani ya gansu sai dai abinda bata sani ba shine, Baba Hasheem, Ummie Bodejo, Mom duk sun gansu,sakinta yayi tashiga mota tare dasu Aunty Mashahuda don Taufeeq ne ke jansu, Mashahuda, Laila, Muneefa, Nihal,ita. Sai motan Sauban Baba Hasheem, Bodejo,sai dayar motan Aseef keja Mom ce a ciki,dayan kuma Aunty Maryam keja Ummie, Ammi,sai dayan Aunty labeeba keja Mommy ce sai kuma yara da akasa a wasu motocin,haka suka tafi abinsu gunin sha'awa. Koda suka koma a sashen Bodejo aka yada zango,nan aka shiga maida magana, Mom ce tashiga bada labarin abinda yafaru tun daga zuwan Zuhra da zuwan su Ammi dasu Daddy sashen Sauban din da abinda suma suka gani,sai zuwan Guggo Laure da cin zarafin da tayi har Sauban ya yanke hukuncin nan,cikin muryan kuka Ammi tace"Yanzu fisabilillah da Sauban be yanke saki a tsakanin sa da Akeela ba hakan zai faru? Aida Galadima bazai shiga halin da yake ciki ba,ga lalacewan zumunci"cikin sauri Bodejo tace" Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi [7/10, 19:53] *_GALADIMA FAMILY_* Page: 69/70 ____Koda a lokacin Saudan be saki Akeela ba to wallahi sai ya saketa domin bazai zauna da shedaniya ba,yarinyar nan babu alamun shiriya a tattare da ita kuyi la'akari mana,wallahi ko bayan raina saudan bazaiyi rayuwa da alakakai ba"tana kare dadar hakan tanufi corridor din dakinta, Mommy tace"gaskiyan Bodejo ne sam babu lefin Sauban kawai Guggo Laure sai a hankali ne"Mom ta mere baki tace"Hmm kune bakusan halinta ba,itafa nata kawai tasani nata nata ne koba komai a wannan hargitsin ma tanuna"ajiyan zuciya Aunty Maryam ta sauke tace"Ni tun randa aka kawo yarinyar nan naga 'yan uwan mamanta masu budadden ido da ita kanta jikina yayi sanyi,don babu irin kunyar nan ta amare ko miskala zarratin a tattare da ita"Mom tace"Bana tunanin 'yan uwan maimuna ne gaskiya,don maimuna mutumiyar kirki ce,haka 'yan uwanta,itafa yarinyar nan daurin gindi kawai tasamu wajen Guggo,kunsan akanta sai da Guggo taje har gida ta zazzage hajiyan mu kafin bikin su?wai Rammat zata kwace mata Sauban,haka dai akayi maida zance batare da Ummie tayi magana ba, Baba Hasheem ne yashigo yana duban duk wanda ke parlour,don babu yara duk suna waje suna wasa,sai su Nihal tare da iyayen su,duban Mommy yayi yace"hauwa'u kufara shirye shirye,gobe insha Allah Zuhra zata tare a dakinta,domin hukuncin da aka yanke kenan,yanzu Bodejo tayi magana"Mommy zuciyan ta fesss tace"Insha Allah,mutanen parloun cikin tsananin farin ciki suke har Ummie sai dai bata nuna ba fuskan ta kadaran kadahan, Ammi kuwa kaman tayi rawa"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah kubashi hakuri ni banason auren wallahi banason Yaya ni karatu na zanyi"Zuhra ne ke magana cikin muryan kuka kota ina zufa ne ke tsattsafo mata kamar babu A.C a parloun,duk da mamaki suka tsaya duban ta parloun yayi tsit bakajin komai sai gunjin kukan ta, Mom ce fuska a daure tace"Amma wannan yarinyar anyi ja'irar banza, Kinga wallaphi kikeyaye mu,idan baki son auren mu munaso aikin banza kawai"Mom tayi maganar tana jan tsaki,sosai Zuhra take kuka wanda yasa jikin Ammi yin sanyi,mikewa tayi ta isa ga zuhra ta kamo ta tace"kiyahakuri Zuhra kinga mahaifinki wasiyya yabari na auren ki da son,ki temaka ki aure sa,inaji a jikina ke alkhairi ce agaresa"Ammi tayi maganar tana murmushi Wanda sosai tabama mutanen parloun tausayi, Ummie kuwa a fusace ta taso domin idan bata daki Zuhra ba bazatayi sukuni ba,ganin haka yasa Zuhra fusge hannunta ta nufi dakin da take zama,cikin muryan kuka tace"wallahi banason sa"kamo hannun Ummie Ammi tayi tace"Menene zakiyi haka bilkisou?wai meyasa kina mantawa da zuhra yarinya ce?dole a bita a hankali fa, menene amfanin abinda kike shirin yi? Ummie cikin bacin rai tace"Haba haba Ammin yara Zuhra ce yarinyar?hmmm taga ana lallabata ne"Mommy tace"babu maganar lallabo Aunty bilkisou gaskiya ne zuhra yarinya ce,so sai anbita a hankali,cikin bacin rai Ummie tabar apartment din, Mashahuda da Muneefa ne suka shiga bedroom din da Zuhra ta shiga, Aunty muneefa cikin bacin rai ta dubi Zuhra"yarinya ina guje miki ranar nadama,wai kuwa kinsan waye ya Sauban?kin kuwa san yanda mata suka rikece akansa?mata da dama sun mutu a son sa wallahi idan kika auresa keda kanki sai kinyi alfahari da auren",cikin kuka Zuhra tace"nidai bana son sa,meyasa Abbie zai yanke wannan hukuncin?i know Abbie bazai taba zabamin mijin da zai cutar dani ba,sai dai why not zuciya ta takasa amincewa dashi matsayin miji,bazan iya yarje ma batun iyaye nabaaa.....takarisa zancen tana sakin wani irin kuka me tsuma zuciya"meyasa aure na yazo a haka?duban Aunty Mashahuda tayi"Aunty Mashahuda meyasa baza'ayi irin shagulgulan da akayi a naku ba,bikin ku is d best biki a wannan year din"dafa ta Mashahuda tayi tana murmushi tace"bikinku ya fita daban dana kowa,kiyarda cewa rayuwar auren ku ne kukuma zai zama abin kwatance, cuz Allah zai albarkaci aurrn ku trust me"shiru Zuhra tayi tana jan ajiyan zuciya, Laila tayi dariya tare da cewa"Aunt duk fa munafunci ne itama tana son Yaya, amma zuciyar ta takasa yardan mata da haka, Nihal itama dariyar tayi tace"wallahi kuwa hhhhhh"a fusace Zuhra ta dubesu"Ni banson sa bantaba son sa ba,mutum daya naso a duk duniya akan shi nasan menene so,wato ya Shuraim.....Tasss! Karar mari ya sauka akan kumatun Zuhra,huci kawai yakeyi idanuwan nan sunyi jajawur,cikin sauri Mashahuda,muneefa, Laila, Nihal suka bar bedroom din, Sauban kuwa banda rawa babu abinda bakinsa yake masa,cikin muryan tsawa ya nuna Zuhra"ke...kk..kkee da aure na akanki kike fadar kina son wani?yayi maganar yana nufo Zuhra yana huci,girgiza kai Zuhra keyi"A'ah yaya don Allah kayahakuri bazan sakeb......hannu ya dunkule kamar zai kaimata punch,sai kuma yakaima wall din bedroom din,ita kuwa runtse ido tayi jikinta na rawa,juyawa yayi yafita,cikin takunsa wannan karan dai-dai da tafiyar cikin fushi yakeyi. Mommy ce tashigo dakin cikin sauri,kamo Zuhra tayi"Wai ke bakida hankali ne?sai yaushe zakiyi hankali my Zuhra,kike fadar bakison mutum agaban mahaifiyar sa gatsal haka?cikin kuka tace"Mommy shima fa baya sona"cikin fusata mommy tace"inji uban wa ya fada miki haka? kuka Zuhra ta fashe dashi hankalinta a tashe sai dai takasa furta komai,kukan kawai takeyi,ki tashi kije ki shirya zakije saloon,cikin sanyin jiki ta mike ta fita,babu kowa a palourn na bodejo,kaitsaye apartment din Ummie ta wuce,a palourn kasa ta taras da ita da Taufeeq suna magana,sallama tayi duk suka amsa sannan ta haye stairs,shiryawa tayi cikin riga da straight skirt,harta dau mayafi tasa kome ta tuna?sai kuma tanemo after dress ta dora akan kayan tafita. Duban ta Ummie tayi"inane zaki haka?cikin sanyin ta tace"Mommy tace nashirya nazo za'a wankin kai"daga mata kai Ummie tayi,hanya ta Kama har takai kofan palour tajuyo cikin raunanniyar murya tace"Ummie ki yafemun"tana karisa fadan haka da sauri ta fice. Sai la'asar suka dawo daga wankin kan,a lokacin ne kuma me henna ke jiranta,abinci taci tayi la'asar sannan Aunty Labeeba da Mommy suka fara yimata dilka,bayan an gama aka mata wankan lalle, fara shiryata cikin wata hadaddiyar net wanda aka mata dinkin wedding gown,blueblack tayi kyau dinkin ya hadu,me make-up tafara zane mata face dinta,light make-up aka mata,tayi balai'n kyau,fito da ita akayi farfajiyan gidan,kanofi ne guda uku,mutane ne zazzaune daga familyn gidan,sai makota da kawayen matan gidan don abune da akayi a kurarren lokaci,anyi decoration din filin sosai,kaitsaye aka kaita wajen rumfarta wanda yayi balai'n haduwa da tsaruwa