Sashe 10
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
rawa yake tace"a'ah wallahi Yaya burina nayi karatu nazaba journalist don Allah kada kafada mai niba aure nakeso ba,kuma ma wazan aura?cike da yarinta tare da tsantsar shagwaba take maganar. Shi Aseef din dana ganku tare ba soyayya kukeyi ba?sannan yaron da yakawo ku gida keda Mashahuda ba soyayya kuke ba?cikin sauri tafara girgiza kai tace"wallahi duka babu Wanda nake soyayya dashi kuma nibansan wani abu soyayya ba niko friend namiji bantaba yiba Allah. Ta sake magana cikin tsantsar yarinta,shiko Sauban dage kafada yayi irin ko a jikinshin nan ya cigaba da driving dinsa cikin kwanciyar hankali. Itakuwa zuhra gabadaya neman natsuwa tayi tarasa burinta yace bazai fada ba.A haka dai suka karisa gida. Da sauri ta balle murfin motar tafito kaitsaye apartment din Ammi tanufa,shikuwa Sauban koda ya ajeta juya kan motan yayi yasake fita. Da sallama tashiga parlon babu kowa sai Aunty Mashahuda,ganin ta yasa tasaki murmushi tana cewa. "Yawwa Zuhra naje nemanki ai dazu shine bodejo tace kinje rubuta Jamb kinsan menene? Girgiza kai Zuhra tayi. Mashahuda tasaki murmushi tace"guy din jiyane da muka hadu a supermarket yakira wai Shuraim koh?shine fa yace nahadashi dake nace baki kusa kinje zana Jamb. Waro idanuwa Zuhra tayi tare da dafe kirji tace"please Aunty Mashahuda kirufamin asiri wallahi adena maganar sa kinsan idan Daddy ko Abbie sukaji zanshiga uku,sannan za'ace guda nawa nake. Mashahuda takama baki tace"toh yanzu zuhra cemasa za'ayi baki sonsa? gaskiya nibazan iya fada masa haka ba sai dai ke kice masa. Zuhra tace"ni bazan iya waya dashi ba Aunty wallahi inajin tsoro kawai abar maganar kirabu dashi Allah,takarisa maganar tana mike tare da fita daga parlon. Murmushi kawai Mashahuda tayi sannan tamike tanufi stairs din Daddy. _____+++_____ A bangaren su Guggo Laure kuwa sai shirye-shirye suke saboda Galadima yakirata cewa su Abba zasu zo daga kaduna a tsayar da magana asa ranar biki. Cike da farin ciki Guggo Laure da Akeela suke,don itama Akeela tsaban murna ma har walima tace zata hada,daga mamanta har Alhaji Mansir sunsamu Ido duk da abin alfaharinsa ne ace 'yarsa tashiga ahalin Galadima amma aida kunya amma wani alqawarin za'a bashi ita akuma zo a fasa. Akeela ce da qawayen ta a dakinta sunata tayata murna daya daga ciki maisuna Suby tace"nikoh akeey baki nuna mana hoton wannan mai sa'ar ba,dayan mesuna zuleey tace"ai da alama shidin ke tsadane fah,dayar maisuna siyama tace"komin tsadarshi ai mu dole tanuna mana shi don ko ba komai anatare duk wanda yaji cewa ma mu nakusa da ita bamusanshi ba ai wallahi dariya za'a mana. Suby tace"gaskiya ne siyama maganar ki Murmushi Akeela tayi wanda dama tun sanda suka fara maganar tashiga gallery dinta inda tayi saving din photos dinshi a IG account dinshi da yake sawa. "Hmmm bbys kenan ku kwantar da hankulan ku gashi tayi maganar tana mikamusu phone dinta. "Wow,suby tafada tana bude mouth, zuleey tace"handsome, siyama tace classic guy. Itakuwa Akeela banda mnurmushi babu abinda takeyi don tasan muddin Allah ya mallaka mata Sauban amatsayin miji to lallai tana daya daga cikin mata masu sa'a. "Kai bby akeey wannan Rich Man din?wanda ko wace mace ke burin aura kika samu?kinsan ko yanda mata ke hauka cewa akansa?to koni ina daya daga cikin fan dinsa. Dan tabe mouth Akeela tayi tace"aiko ko wacce mace kwalelenta don inada tabbacin ahalin da ake ciki babu macen da takaini daraja a wajensa. Suby tace"Lallai ne akeey dole ne team dinmu yasake haskawa dole muba haters wuta. "Yanda kikajin nan Suby,hmm lallai kinyi babban kamu kekam. Akeela tasake sakin murmushi akaro na babu adadi tace"ko babu auratayya tsakanina dashi shidin brother nane da hajiya Laure da Alhaji Muhammad Taufeeq Muhammad (GALADIMA) uwa daya uba daya. Duk zaro idanuwa sukayi waje cike da mamaki. Suby tace"lallai kam muntayaki murna,nanfa suka fara shirye-shiryen yanda party din sa ranar zai kasance don dole duniya Susan wannan abin ko ba komai zamu sake zama celebrates a duniyar tiktok musamman ma ke akeey,cewa zuleey nanfa suka hau ihu bakajin komai sai hayaniyar su da hirarrakin su. Acan fam din Galadima kuwa Daddy ne yakira Sauban bayan sallar isha'i yake tambayar sa wata nawa yake ganin za'a sa ranar. Wani gwauron ajiyar zuciya Sauban ya sauke cikin kamewar sa da nutsuwa yafara magana. "Daddy inda so samu ne asa nanda 1 year saboda inaso naje naga yacce aikin zai kama sannan nayi duk tsare-tsaren da zanyi kafin lokacin insha Allahu everything will be fine. Kura masa ido Daddy yayi tare da dan murmushi yace"gaskiya baza'a sa 10year ba to bari kaji koda mukayi shawara da Alhaji Mansir dasu Abbie dinku da za'a sa 4month ne shine Abbie naku yace a tuntube ka aji tabakinka,Amma wani irin 1 year Sauban babu dadin ji. Sake tsuke face yayi tare da sake rissinar dakai yace"please Daddy a duba a gani. Daddy yadaga masa hannu tare da dubansa face nashi babu alamun wasa ko kadan yace"Za'a tsaida ranar auren ku nanda 8month shikenan. Sosai ransa baiso ba kuma ko kadan baya farin ciki bare mara ba da auren,sai dai duk kwakwanka bazaka gane hakan akan fuskar sa ba. Dan rausayar dakai yayi gefe yace"Shikenan Daddy Allah yasa hakan shine yafi alkhairi. Da Ameen Daddy ya amsa,tare da sa masa albarka don har ransa yake farin ciki da irin danda Allah yabashi,duk da kasan zuciyansa cike yake da tausayin Sauban din. Mikewa yayi tare da masa sai da safe. BAYAN KWANA BIYU Zuhra tunda taji Abbie dinta zaizo takasa sukuni tsananin farin ciki ya dabaibayeta,kudi ta amsa wajen bodejo tabawa security mai bawa fulawa ruwa tace yasiyo mata kaji na turawa guda uku da wasu dai siyayyan,zama tayi ta hada ma mahaifinta lafiyayyen dambun kaza dasu cake da dubulan,da temakon Hannemai aikin bodejo tahada masa komai,ana gobe zasu taho shida Abba tahada komai ta adana,daren ranar cikin tsananin farin ciki tayi bacci. Washegari su Daddy suka shigo maidugri kuma kaitsaye gidan Guggo Laure suka sauka a hanya suka hadu da Baba Hasheem da komai na al'adar saka rana,nan aka musu tarba ta girma wajejen la'asar aka sanya ranar wata takwas. Itadai Guggo Laure ba haka taso ba amma tunda ansa babu yacce zatayi. Haka suka dawo gida, Baba Hasheem apartment dinsa yashiga, Mom yacidda tana hada abinci a dinning,koda yayi sallama da mamaki tajuyo tana dubansa. Murmushi yayi tare da cire hulan kansa ya zauna akan kujerar,sannu da zuwa tamasa sannan tace"wallahi nadamu Abban Aseef tundazu hankalina yaki kwanciya ganin baka dawo daga office ba gashi inata kirar wayar ka taki shiga. Cike da farin ciki Baba Hasheem yace"ya hakuri Rabi wallahi abubuwa ne suka shamin kai munacan wajen sa ranar auren Sauban ne da jikan Guggo Laure!! Wani gingirin gin Mom taji kanta ya mata cikin tsananin rudewa ta dubi Baba Hasheem. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 11/12 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *_Ba zaku gane maza security bane ga mata sai mijinki ya rasu ko kun rabu ..._* *_Duk ranar da akace baki da Aure toh fa sai ahankali kin zama hanya mai insecurity, keda hanyar Zamfara ko Rijana na Kaduna kusan daya *_Yo harda wanda bai isa ya maki magana ba zaiyi.._* *_Amma in kina da Aure Koda mijinki baya tabuka maki komai ke kike ciyar dashi mutane ba zasu taba miki kallon banza ba ..._* *_Don Allah Yan uwa mata mune zamu gayawa juna gaskiya idan matsalar da kike fuskanta ba matsala ta transformer bace da baya kawo wuta , ba Kuma dukanki yake ba kiyiwa Allah kiyi hakuri ki zauna.._* *_Babu auren da ba a fuskantar matsala sai dai muce na wani yafi na wani..._* *_Babban matsalar Bai wuce talauci ba , kuyi hakuri lokaci ne , wannan keburan na taba kowa Dan dai mutane Basu fito sun Fadi matsalarsu bane ..._* *_Ina bawa duk wata matar Aure hakuri, a Kara hakuri, Allah yaci gaba da baku hakuri ya biya maku bukatunku na Alkhairi._*