← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 64

Sashe 2

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yaren yahudawa ne?yaranku sun girma kuma ko wannensu idan aka masa aure zama zeyi to akan mene?ga Sauban nan dashi da taufeeq sun cika ko wannensu ba master's ne dashi ba? Galadima yayi maganar yana dubansu cike da nazari, Daddy yace"hakane Alhaji munaso ne dama munemi yaran idan anzo saka ranar su mashahuda kan maganar saka nasu ranar idan yaso komai yazo yanda kowa keso sai a hada bikin nasu rana daya ayi ko sadeeq?yayi maganar yana duban Abbie. Abbie yace"Ea yaya nima inaso nakira Ummien yaran ne nace sutaho gabadaya dama abinda yahanasu zuwa maganar jamb class dinda zuhura keyi ne so zankirasu zutaho nan din kawai.Galadima yace "gaskiya kuwa,anjima idan an idar da sallar la'asar inaso muje daku gabadaya mu duba jikin Laure ance tanata zazzabi tana kwance. Gabadaya suka amsa da insha Allah sannan suka miqe suka nufi masallaci gabadayansu harda Galadima. Zaune yake a dakinsa yana duba wani saqo a laptop dinsa da aka turo masa ta Email dinsa,wani company a qasar maleyshia taturo dashi kan suna son daukanshi aiki idan babu damuwa suna nemanshi Nanda 4days kan yazo za'ayi musu interview a cikin su goma Sha shida 'yan nan Nigeria. Sosai yaji dadin hakan aransa wanda inba kalura dakyau ba bazaka fahimci hakan ba, duk da fuskanshi takasance me tsananin kyau tamkar jinin larabawa,dama shidin jinin shuwaarab ne,miqewa yayi a fili yafurta"ALHAMDULILLAH,Masha Allahu laquwwatu illa billah,jallabiya wata blue black yadakko ta yasaka wacce tayi tsananin yimishi kyau yafita,kaitsaye masallacin dake layinsu ya nufa. Koda aka idar da sallah tare suka fito dasu Daddy,wajen Abbie yanufa fuskanshi dauke da murmushi duk cikansu da mamaki suke dubansa baba hasheem yace"A'ah Sauban yaushe Kuma kadawo garin?Abba yace"tambayeshi dai kam.Dariya yayi tare da dan rissiniwa yafara gaggaishesu, cike dajin dadi gabadayansu suke amsawa. Murmushi yayi wanda yasa dimple din gefen kumatunsa lobawa yace"Ai Ina ajesu kawai najuyo don banma shigo gida ba sai wajejen asubah. Galadima yace"kunji koh?kunji irin gangancin nasa Koh?inbanda kasada mezesa kadawo a wannan lokacin kamar Wanda ake kora? Abbie yace"Sadauki ba na hanaka tafiyar dare ba?ai wannan ganganci ne kadena sam baida amfani. Rissinawa yayi kadan yace"insha Allah za'a kiyaye. Shiga cikin gidan sukayi gabadaya inda su suka nufi farlon Galadima,domin muddin Abbie da Daddy na garin sun shigo to a farlon Galadima akecin abinci,shiko Sauban kaitsaye apertment dinsu yanufa. Da sallama yashiga cikin farlon hayaniya yaran dake farlon keyi Amma jin sallamar shi yasa farlon yakoma shiru inda banda sautin amsa sallamar da yayi bakajin komai, 'yan matan kuwa dake zaune ko wacce wayarta tasaqe suka fara boyewa. "Barka da shigowa Bro Sauban!!!abinda 'yan matan suka fara fada kenan,suko sauran yaran oyoyo suka nufoshi suna mai,sai sai suna qarisowa gabansa sukaja birki suna dariya don sunsan basu isa suyi hugging nashi ba donbshi mutum ne wanda befiye son daqunar yara ba. Murmushi yayi iya lebe tare da cewa"yawwa sannunku,ina Ammi take?nuna masa wani dogon corridor sukayi,yamike kenan da niyyar zuwa sai gata tafito. Da murmushi yatare ta yace"sweetheart,dan hugging nata yayi,hararar wasa ta aika masa dashi wacce da alama babbace don zatayo sa'a da Ummie. Murmushi yayi yace"Me Kuma nayi sweetheart?irin wannan harara haka?Ammi tace"Hmmm zaka sani Ina ganin sanda kashigo gidan nan,wallahi Sauban bakajin tsoro zaka sani ne,muje dinning kaci abinci. Dariya yayi tare da dan kamo shoulder dinta suka nufi hanyar kitchen suka shiga,babu wani jimawa ya Sauban ya fito hannunshi rike da plate biyu ya aje akan dinning yajuya baijima ba yafito riqe da ruwan gora cup,zama yayi kan dinning din yadubi inda 'yan matan suke yace"Mashahuda kije kitchen ki amsa abincin su Daddy kikai farlon Galadima,kekuma muneefa kizo kidauki na boddejo,da to suka amsa don kafin ma ya ida maganar suk sun miqe. Sallama akayi tare da shigowa,Kareem ne yashigo abokin ya Sauban da sauri yaran suka nufeshi suna Oyoyo bro Kareem,bude musu hannu yayi duka su ukun suka fada jikinshi,itakuwa inteey kaitsaye inda ya Sauban yake tanufo,ta wutsiyar ido yadubeta don yasan yarinyar mayyanshi ce duk abinda zai mata tananan kwafufe dashi,kusa dashi tazo ta tsaya tace"ouncle mommy na tace zaka siyomin hollandia idan kadawo tace koka manta natuna maka idan batazo daukana ba kai zaka maidani gida. Dago manyan idanuwansa yayi yana duban yarinyar don yana tsananin mamakin wayon yarinyar don inteey bata wuce 4 yrs ba,murmushi yayi mata yace"bby inteey kenan ainasan mekike nufi nikadai nake gane dama wannan yaren naki,dakko ta yayi yadorata a cinyarsa yafara feeding dinta,idan yayi 1 spoon itama yabata.Sarai yagane abincin zataci shiyasa ta bullo masa ta wannan surutun,Hakeem ne yakariso inda yake yana murmushi donshi mutum ne wanda sam murmushi baya gushewa a fuskarsa,yaron abokin Daddy ne sosai suke zumunci shiyasa yaransu ma Sauban da Hakeem suka dinki. Mikomai hannu Sauban yayi alamun musabaha yace"mutumin Ashe kadawo?shine ko kakirani?Koda yake nayifa lefi ne shiyasa sorry,yaqarisa maganar yana kunshe dariya. A daidai nan Ammi dasu muneefa suka fito kowacce hannunta riqe da basket sai dai na mashahuda sunfi yawa,kowacce doguwar riga ce ajikinta sai veil,gaishe da Kareem sukayi suka fice,Ammi kuwa dinning din tanufo ta zauna tana fadada murmushinta tace"a'ah Kareem kashigo gidan ne? "Aikuwa Ammi inayini munsameku lafiya? "Lafiya lou ya hajiya sakinan dasu bahijja? Lafiya Lou Ammi,dubanshi Ammi tayi tace"tashi kaje kitchen kasa abincin mana don yau mutumin ka akayi. Murmushi Kareem yayi yace"Ammi gurasa kikayi?Amma 'yan matanki suka miki koh? Saboda naga kinaji da kanki don ma Allah yasa Ammin namu macece jaruma,yaqarisa maganar cike da zolaya. Harara Sauban ya aika masa dashi donshi yana mamakin surutun Hakeem haka ko gajiya bayayi,shiga kitchen din Hakeem yayi ya hada gurasar sa yafito abinshi. Inteesar ta sauka jikin ya Sauban takoma wajen Kareem tunda sun cinye nasu don shi Kareem ne wanda baifiye cin abinci ba. Harara yabita dashi tana dariya ta falfala da gudu tabar farlon don sauran yaran dama sunfice sun nufi sashen Mom. A bangaren su mashahuda kuwa suna mikawa su Daddy abincin suka nufi sashen Mom bayan sun gama tsokanar Galadima,don bodejo batanan tana wajen guggo Laure don haka suna bude bedroom dinta suka ajiye mata. Shiga apartment din mom sukayi,mom na kitchen don haka kaitsaye kitchen din suka nufa, Mom sannu da gida,cike da fari'ah tajuyo tace"yawwa sannunku daga ina haka? Muneefa tace"abincin su Daddy muka kaimusu farlon Galadima dana Galadima. Mashahuda kuwa batasan sanda tayi subul da baka ba tace"kai gaskiya matar ya Sauban wallahi ta shiga uku dashi,da yasani ma aikin soja kawai yashiga,tab irin wannan mazurai haka? Dariya mom da muneefa tasaka tace"ai shiyasa bansan sanda nasaqe wayata ba gudun kada ayi sezing dinta. Mashahuda tace"Kuma wallahi kar yagammu kawai dai ya share ni yayi kakar be ganiba. Muneefa ta diddilo Ido cike da tsoro tace"wai dagaske?mashahuda tace"Allah gashi ko amso gurasar mu bamuyi ba,ai wallahi bazan koma ba sai yafita. "Nima bazani ba don nasan halinki sai ki'iya cewa _don Allah muneefa jeki amso Mana abincin_,babu inda zani ahto kadama kiqarisa. Dariya Mom tasaka tace"lallai ne big broo yacika big broo ai haka akeso. Su Daddy Koda suka gama cin abinci basu wani bata lokaci ba suka shiga motocinsu,kaitsaye gidan guggo Laure suka shiga,itama tanada dan nata rufin asirin sai dai ko kwatan kafar na Galadima da iyalensa baikai ba,baba hasheem ne ke driving nasu,gefenshi Abba ne,sai abaya Abbie, Daddy, Galadima. Fitowa sukayi sannan suka budema Galadima shima yafito tare da hadadden sandarsa mai matuqar kyau da tsada yafara dogarawa yana gaba suna biye dashi,maqota sun leqo sai kallansu akeyi. Wani yaro ne da alamu jikan guggo Lauren ne yashiga da gudu yana cewa tayi baqi,duka da cewa flat dinta daban sai na yaranta su biyu maza kowa da nashi flat din da Alhaji sani da Alhaji mansir. Shiga dakin sukayi bakunansu dauke da sallama, bodejo ce ta amsa tana zaune akan kujera,tsohuwa me shakaru sai dai dayake tanada kyan jiki ga kuma arziqi yasa tsufan yamata kyau,itakuwa guggo Laure sallah take Amma tsaban farin ciki ko lazimi bata idar ba tajuyo ta sallame sallar tace"Yaya muhammadu yau Kaine a gidannan?tayi maganar tana dariya, a'ah a'ah a'ah gaskiya naji dadi gaka gasu taleeb da Alhaji sadeeq maraban ku sannu da zuwa. Gaisheta su Daddy sukayi cike da dattaku da muntuntawa suka mata ya jiki,sannan aka shiga gaida bodejo wacce murna da dadi yakasheta a zaune ganin zaratan yaran nata. "Yaya muhammadu nace magana akan akilan kazo ayi koh?dama nace najika shiru ai wallahi da nasan zakazo da banbari yau taje bikin nan ba!Guggo Laure tayi maganar. Galadima yace"wacece kuma haka Laure?ninazo duba jikinki ne,tun sassafe yaronnan sani takirani kan bakijin dadi shiyasa ma bodejo tamatsa zatazo duk da itama ba dadin jikin nata takeyi ba. Guggo Laure tadan tamke fuska tace"a'ah Yaya kamanta ne yarinyar wajen mansir dana maka magana kan inaso a hada aurenta da Sauban ko don zumuncinmu yaqara karfi! Kallon kallo akafara tsakanin Daddy da Abbie da Abba da baba hasheem cike da mamaki,bodejo kuwa hangame baki tayi tana duban guggo Laure. _TOFA WATA SABUWA INJI DAN CACA,ANYA TSOHUWAN NAN BA RIGIMAMMIYAR TSOHUWA BACE?DA ALAMA GALADIMA DA IYALENSA BASUYI AMANNA DA WANNAN MAGANAR BA._ Xahratty Ce Lallai Alqalami yafi takobi [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 03 _please idan kunga kurakurai na typing ba'ayi editing bane so kuyahakuri._ Gyaran murya Galadima yayi tare da duban guggo Laure yace"Laure kenan keda baki da lafiya wani magana ne za'ayi yanzu data wuce ta samun lafiyarki?nikinga su taleeb ko tuntubar su ma banyi da zancen ba a inda mukayi zancen anan nabarshi. Da mamaki sosai a fuskan guggo Laure take duban Galadima. "Au Yaya kana nufin zancen nawa ma bashi da darajar da za'ayi ta?nifa Yaya so nake mu karfafa zumuncinmu tunda bamu samu hadawa ta hanyar 'yaya ba sai muhada ta hanyar jikoki,idan kacire rabi datake aure da Aliyu(Abba) waye nahada ?wannan kuwa jininmu da tsokar mune zamu hada. Galadima cike dattaku irin na tsofaffin mutumci yace"Laure kibari kisake samun sauqi sai ayi maganar sannan muji ta bakin yaran idan sun amince da juna. Salati guggo Laure tasanya tana tafa hannu tace"Yaya muhammadu!kada dai ace yaran zamanin nan sunaso su maidaka kaima dan zamani?bodejo da takasa haquri tuntuni tace"aiko Laure yanzu zamani yazo ba'a ma
Chapter 2 · 0% Book details