Sashe 20
Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kisa a ranki aikinki ya kammala gashi kutafi yanzunnan. Da sauri suka mike ko gidan da suke sauka basu koma ba don dama bawai sunzo da kayan canji bane,hand bags ne shima suka tura driver hjy Aliya yaje ya dauki musu,nanfa suka fafaro hanyar dawowa lajeria ______ *NIGERIA*______ Haka wadannan ahalin suka kasance cikin farin ciki inda a washegari Sauban zai koma Malaysia,ummie ma tace zataje maidugri kusa da diyarta ta kwana biyu ta dawo. Tunda babu daman ita ta zauna kodan school dinta,inda Amma itama atake anan tace zata bisu taje sosai sukaji dadi babu bata lokaci Abba da Daddy suka fita nema musu jirgi Wanda zaije borno kona 5:00 pm ne. Cikin yardan Allah kuwa suka samu jirgin inda nan suka tafi suka bar su mommy da Abba da kewarsu,maimoon ma sai rigima suke kan sai sun bi Ummie. Washegari tun 7:00 am Kareem yadauki Sauban don kaishi airport,jirgin 7:30 zaibi hakan yasa basu wani jima da isaba aka fara neman matafiya aiko nan Sauban yatafi suna ma juna waving hannu shida Kareem. Anan ma wani sabon kwarkwaryan walima aka hada don su Mashahuda sunyi farin ciki haka su nihal saboda babu wanda besan 'yar tsaman dake tsakanin Ummie da Zuhra ba. Duk da tasan yatafi Amma sai ta nemi walwalarta tarasa tunda taji labarin shine mutumin da yayi aikin haqo asirin da aka mata itada Ummien ta sai taji wani kiman sa da darajar sa a zuciyar ta,musamman da taji irin kasada da hadarirrikan dake cikin aikin tare da wahalar da yasha sai mutumcin sa ya ninku a idon ta,duk da tasan bawai yinsa take ba hasalima ba birgeta yake yaba yasata jan tsaki akasar ranta ta furta " _to meye abin damuwa da tafiyar nasa?kekam wawuya ce._" Yinin ranar kwanan farin ciki wadannan ahalin keyi,don saura kiris Zuhra tayi lattin School ko wanka batayi ba ta sulale tatafi gashi suna da test. *MALAYSIA* Yauma kamar kullum sanye yake cikin suit gray sosai yayi kyau duk da fuskar sa babu alamun fari'a ko kadan amma hakan 'yan matan company din nan keta binshi da mayataccen kallo,dan tsaki yayi kasa tare da sake tamke fuskar a hankali ya isa office dinsa. Nan aka fara shigowa yimasa barka da zuwa maza da mata. Aiki yakeda shi sosai akan wani designer shoe da yafito wanda sam bema bayyana ba shine take su hada don ko babu komai a fara gani a company nasu shysa take so busy yaudin kam,don duk wanda yazo nemanshi ma baya ma samunsa saboda ya gayama secretary dinsa cewa duk wanda yazo tace yana aiki. Bashi yabar office ba sai kusa to 6:18 na yamma kaitsaye wani shagon coffee yanufa saboda wata hardaddiyar yunwar da yake jinsa. ****** *NIGERIA* ****** "Ni gaskiya yau zan dawo kanme zakice nakara lokaci?kinsan kuwa irin takurar da nake anan?ni da wallahi nasan yau zai jiya zai wuce da tun shekaran jiya na dawo gida,ganinan dawowa yanzu. Akeela takarisa maganar tare da datse kiran tana jan dan siririn tsaki a fili tace"mutum sai shegen taurin kan tsiya,yama kulani baikulani ba hasalima kamar besan da wanzuwa ta ba. "Lallai iska na wahal dame kayan kara! Taji an bata amsa ta bayanta. Juyowa tayi don ganin ko wace isasshiyar ce. Rammat ce zaune kan 2sitter din daya daga cikin set din kujerun guda biyu dake farlon,ta daura kafa daya kan daya sai girgiza su takeyi bakinta dauke da chwengum tana tauna,dagowa tayi akaro na biyu tasake watsama Akeela wani banzan kallo tare da cewa. "Ko mara aji nason mace me aji,ko wawan namiji nasan mace me aji kisama ranki cewa keda ya Sauban tazarar ku tamkar sama da kasa ne yayi Miki nisan da baki isa ki cimmasa sai dai kizo a 'yar aikinsa".Sosai kalaman Rammat suka batama Akeela rai wanda har yasata kasa control din kanta cikin tsantsan hargagi da masifa tataso ma Rammat"karya kikeyi karamar karuwa karamar kilaka,karya kike kice tazarar dake tsakanina da ya Sauban tamkar sama da kasa ne don ko babu komai nidin jininsa ce kuma dan gaba kadan zan zama uwar 'yayansa"takarisa maganar tana zabgama Rammat harara. "Ahayye cassss! Lallai saifa su jininsa su jininsa an wahala,shiyasa ai naga yana tattalaki tare da riritaki ko?ko kina tunanin bansan irin shige da fice da gwagwarmayan da kike bane don samu soyayyan sa?wallahi ba baki nake miki ba Akeela keda samun soyayyar ya Sauban sai Allah,muddin baki natsu ba kinsan Allah ya faku,maganar karuwan ci kuwa ke har kinda bakin magana akan wannan?ke wani irin badala da ta'asa ne bakiyi?kunna datan ki,kishiga cikin IG naki kiga abinda na wallafa. Tana kare faden hakan tadauki handbag dinta tare da barin farlon zuciyar ta fal farin ciki duk da taji zafin maganganun da Akeela ta fada mata amma tasan ko babu komai nata martanin yafi zafi. Da sauri Akeela ta dauki wayar ta da niyyar shiga IG dinta sai ganin kiran Suby tayi,da sauri tayi picking call din. Jin abinda Suby ke karanta mata tacan bangaren yasa zuciyar ta sake tsinkewa batare da tabari takai aya ba takatse kiran,babu zato sai ga Kiran zuleey itama.Dogon tsaki Akeela taja tare da rejecting call din tana meshiga cikin IG dinta inda tafara cin karo da sakon ni ta DM dinta,shiga tayi tafara duddubawa inda banda dakan lugude babu abinda zuciyar ta keyi,kaitsaye wall din Rammat tanufa nan taci karo da wani post da Rammat dintayi wai. _Wai Wanda akasa ma Rana da Akeela ba sonta yakeyi ba hasalima itace tashiga tafita tare da bin malaman tsubbu da matsafa aka shawo mata kansa har akasa rana,a hakan ma shidin baya sonta don yanzu haka tana gidan su don farauto soyayyar sa,inbanda karuwa ma jahila ce taya zatayi tunanin kamilin mutum irin wannan zai so karya kamanta? Tabbas ta yaudare kanta da bata tantance dai-dai da akasin hakan,mudai namu ido Allah yakaimu lokaci musha biki._ Abinka da celebrities kafin wani lokaci magana nata trending a social media wasu har screenshot sukeyi,wani kwallan takaici ne yazo ma Akeela a makoshi cilli tayi da wayar kan kujera tare da fita daga apartment din Ammi,kaitsaye apartment din Mom tanufa. Mashahuda da fitowan ta kenan daga apartment din Abbie don kaima su Ummie abinci taganta,dan tabe mouth tayi. Itakuwa koda tashiga ta cimmusu sunata aikin hira da shewa,ai tana Isa batayi wata wata ba cikake tassssssssssss! _KUYIMIN AFWA MAKARANTA MUNA FAMA DA MATSALAR WUTAN NEPA NE DON BA SAMU MUKE BA,SHIYASA NAKETA ASUSUN NA'URAN NAN NAYIN CAJI , XAHRATTY MAI KAUNAR KUCE XAHRATTY CE Lallai Alqalami yafi takobi 1/5/23. [5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 31/32 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _______Duk cikansu mikewa tsaye sukayi Mom,muneefa,banda Rammat dake zaune dafe da kunci baki a sake,aiko minti biyar ba'a kara ba itama tamike batayi wata wata ba tasauke ma Akeela tagwayen maruka dama da hagu wanda har sai da yasata yin taga zata fadi,cakumo ta tayi tare da fara magana. "Ni sa'ar kice ko ko ancemiki ni irin yaran da kuka raina ne kuje har inda suke ku dakesu,tayi maganar tana me wujijjiga akeelar abinda da dama ba kiba. "To bari kiji idan kina cin kasa kikiyaye ta shori wallahi duk randa kika sakemin wannan jakan cin sai nabiki abinda a kungiyar kuma babu wanda zaiganeki usless kawai.Sosai Akeela tayi mmkin abinda Rammat tayi mata kuma bazata iya ramawa ba don tasan tafi karfinta amma tadau alwashin sai tasa anrama mata ko badane ko bajima,haka tamike jiki a sabule tana fadin"wallahi ki rubuta ki ajeyi sai nabaki mamaki sai namiki abinda baki zata ba.... "Kindade bakiyi ba don abu kaza naki ina jiranki",takarisa maganar tana me nufo Akeela,ai dagudu tabar farlon tana cigaba da zage Mom da muneefa kuwa mezasuyi banda dariya saboda yanda Akeela tabasu dariyar. Koda nufar ta apartment din Ammi cikin sa'a tacidda babu kowa a farlon haka ta isa bedroom dinda tasauka tashiga hada kayanta,babu bata lokaci ta jawo trolley bag dinta nanma bata ci karo da kowa ba kaitsaye fita tayi daga farlon. Haka tafita gidan tare dajan dan akwatinta don barin layin,saboda a layin ba'a samun adaidaita sahu sai anfita don ma suna farkon layine. Haka tabar layin cike da bacin rai har neman number suby takeyi bata samu ba har kwallan takaici tayi. Sai wajen karfe takwas Ammi taga dai shiru shiru bata fito ba gashi za'a ci abinci amma babu ita duban Daddy tayi tace"Oh ni Aisha koyau Akeela lafiya bata fito ba,tashi Mashahuda kikirata kice tazo tayi dinner. "Please Ammi kirabu da ita wallahi ba yunwar takeji ba da tanajin yunwa ai zata fito yin dinner din, Mashahuda tayi maganar tana yatsine face. Dagowa Ammi tayi da niyyar sake mata magana wayar Daddy yafara ringing,ganin sunan Guggo Laure yayi cikin dattaku ya amsa kiran tare da fara gaisheta ko aya bekai a maganar ba tafara zazzaga fada. "Taleeb wai me akeso a maidani a gidan nan ne naku?yanzu fisabilillah wani ahalina bashi da iko a gidan nan har bare ace yafishi? "Subhanallah Guggo meyafaru ne haka? "Yanzu ramatu ne ta yayyarfa ma Akeela mari waye ubanta?dangartakan me mukedasu da har tasamu wannan zarrar?sosai Daddy kanshi ya kulle yarasa wacece take magana akai,cike da kamewan sa yace"Guggo wacece kuma ramatu wallahi bangane maganar da kike akaiba. "To bari nasanar maka da abinda ke faruwa,nan Guggu Laure tafada Daddy duk abinda Akeela tace mata ta ida zancen da cewa"kuma wai saboda raahin mutumcin irin na rabi a gabanta akayi komai amma ta kasa kwabawa. Nannauyan ajiyan zuciya Daddy yasauke tare da bawa Guggo Laure hakuri sannan ya cemata itama Akeela bata kyauta ba don kawai haka tafaru ta tattaro kayanta tadawo gida sam beyi ba ko bata fada musu abinda yafaru ba ai ta musu sallama. "Yo taya zata muku sallama tunda an sakota gaba da musifa tunda akace ansa ranar ta da Sauban makiya keta bayyana kawunan su gabadaya ansata a gaba. Shiru Daddy yayi tare da mamakin halayen Guggon nasu nakin gaskiya sam ita batason gaskiya kuma bataso ka gyara mata kuskurenta komai kankantar sa. "Shikenan Guggo kiyahakuri insha Allah za'a wa tufkan hanci,nan sukayi sallama. Cikin bacin rai Mashahuda ta dubi Daddy tace. "Wallahi Daddy sam Akeelan