← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 64

Sashe 26

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka gaida mutan gidan. "Insha Allah zasuji Yaya. Wucewa yayi a ransa yana kissima abubuwa da dama inda lokaci guda ya fahimci inda Shuraim ya dosa,kaitsaye apartment din Ummie ya nufa. "Kingani ba?tun yanzu nafara samun shiga a family naki ko?to dana fito da maitata nasan za'a amince,dariya Zuhra tayi tana kokarin yin magana ne ta hango Laila ta doso inda suke kaitsaye,nuna ma Shuraim Laila tayi tace"kaganta ko?duban inda tanuna masa yayi yace"who is she?dariya Zuhra tayi tace"her name is Laila, she's my lovely sister nd my abokiyar fada,dariya Shuraim yayi itama Laila dariyar tayi don taji amsar da zuhran ta bada,duban Shuraim tayi tace"Barka da zuwa! Dariyq Shuraim yayi yace"Barka dai fatan kina lafiya?ya shirye-shiryen biki? Laila tace"Alhamdulillah shiri ananan anayi sai dai mujira ranar daurin aure,maida dubanta tayi ga Zuhra tace"Ummie na kiranki, Zuhra tace"Okay to bari naje tayi magnan tana duban Shuraim"Ya Shuraim nizan wuce please don Allah kagaishe da mutanen gidan. Takarisa maganar tana me wucewa tabarsu tare da Laila yana janta da hira. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 26/5/23. [6/7, 15:49] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 41/42 ______Kareem ne yadubi Sauban yace"Ango kiran kafa akeyi da alama kawayen amarya ne,kuma nasa akan maganar kudinsu ne"Cikin bacin rai Sauban yace"I don't have time for wadannan 'yan iskan ladies din masu fama da hayakin kai,nine zanbasu 10 millions naira na hidimar biki?to ai banfito a cikin jerin ahalin karuna ba idan har abinda nayi niyyar basu bazai musu ba sai dai subar hidimar da zasuyi. "Calm down! Friend abin bana daukan zafi bane haka,please kabisu a sannu nisam banason abinda zai sanya kabata ma kanka rai ka bata mata ita.... wayar ce aka kara Kira, Sauban ko kalla beyiba duk da face dinsa bazaka ga mahaukacin fushin nan ba,Kareem ne yayi picking call din. Cikin muryan shagwaba tare da karairaye murya,gyaran murya Kareem yayi yace"bashi bane amarya,barka da Rana amaryan bakya lefi koda kin kashe dan masu gida. Batare da gaisuwa ba Akeela tace"uhum Kareem kenan,nace please sweetheart din baya kusane kadauki phone din?dan murmushi Kareem yayi ta hanyar danne bacin ransa yace"aiko baya kusa yabar wayan a dakina ne kafin yaje yadawo but insha Allah idan yadawo zan sanar masa kinkirani"Da sauri Akeela tace"no ba wani abu bane dama tuni akan maganar hidimar kawaye naje haryanzu baku nemesu bane kuma time na tafiya ya kamata abasu abinda kikace. Kareem sosai yasan abokin sa magana daya yakeyi daganan baya canjawa"kingani Akeela abinda yasa bamu nemeku ba maganar gaskiya Sauban yace bazai iya bada 10 millions ba,idan kuma kum matsa sai hakan tofa sai dai ku fasa hidimar taku. Wani kululin bakin ciki da takaici Akeela taji ya ziyarce ta lokaci guda,tanaso tayi rashin kunya amma tsoro ya hanata,cikin karfin hali"Yanzu fisabilillah a ganinka Kareem ya kamata Sweatheart yace bazai bani wannan kudin ba?me akayi akai 10 millions please?meyasa yakeso yamaidani wata karamar yarinya wajen friend's dina?alhalin ansan wanda zan aura Muhammad Taleeb Muhammad nefa haba haba,dage kafada Kareem yayi tamkar tana gabansa yace"to kinji nidai abinda yacemin kenan kije kiyi shawara don yace daga 3 millions bazai kara wani abu b.....batare da yakarisa abinda zaice ba daga bangaren Akeela yaje tace"Kutumar uban can!!! Atake anan kuma wayar ta gimtse alamun ta gane katobarar da tayi kenan.Wani dariya Kareem ya kunshe saboda tabbas tasan Akeela ba irin tsarin macen da abokinsa yakeso bane,dogon tsaki Sauban yayi tare dayin kwafa batare da yace komai ba yamike ya shiga toilet. Acan kuwa gidansu Akeela tabotsare sai masifa take zazzagawa a dakin Guggo Laure tare da kuka,tana fadin itafa Sauban baya sonta,sosai hankalin Guggo Laure ya tashi ranta ya baci matuka amma haka ta danne gudun abinda zaije yadawo taja Akeela cikin dakinta tare da fara kwantar mata da hankali,nan fa tafara lallashinta magana tafara mata kamar haka"inaso ki saurare ni kiji da kyau, ni babban matasalata dake wutan ciki taya bikinki saura kwanaki kifara bacin rai da hayaniya? Cikin muryan kuka Akeela tace"Haba Guggo ni sam abinda guy dinnan yakemin sam baya min dadi,haka sauran mazan suke?koko don yaga ina son shi shiyasa yake min haka?nikawai Guggo kisa mallakemin shi sai abinda nakeso za'ayi"Ajiyan zuciya Guggo Laure ta sauke tace"Ai wannan dole ne kisha kurumin ki dama kina tunanin zamu barshi haka ne?ai wallahi bazai yuwu ba,gashi yaro Yana neman zama mante malloniya,dole ya zama na yana tafin hannu mu mune muke juyasa wanda ko Aisha sai tarasa kwanciyar hankalin ta,cikin tsananin farin ciki Akeela tasaki dariya"yawwa Guggo na shiyasa nake matukar son ki nufa kin fimun Mom wallahi,domin Mom bata damu da damuwa ta ba"... Mtsewwww! Don Allah dena tadin wannan shashan wake maganar ta?cewan Guggo Laure. Wayan Akeela ne yayi ringin cikin sauri tadauka"hello baby's ya akayi ne?daga can bangaren aka amsa"ok to bari nazo dama ina sasan Guggo ne amma ganinan fitowa,takarisa maganar tana mikewa wayar kare a kunnenta tana fita,cikin jin dadi Guggo Laure ke duban ta don ko babu komai tana mata murnan shiga ahalin GALADIMA FAMILY,a fili tace"Wane Mujaheed?ai Akeela ba tsarar ka bace,kuma ba sa'ar ka bace,duk da nice nan na haifi iyayen ku amma kuma da banbanci"Guggo Laure tayi maganar tana wurgama iska harara. Dai-dai sanda ta isa wajen su Suby alokacin wayar ta tadanyi kara alamar message yashigo cikin wayar,cikin zumud ta dago wayar tana dubawa,sai dai abinda taci karo dashi yasa murmushin nata gushewa,da karfi ta furta"kan ubancan,lallai ma mutanen nan nizasu maida wata 'yar iska wai ko mene?jibi don Allah Suby,tayi maganar tana mika mata wayar ta. "Wai iya kacin abinda suka turo kenan?Suby tayi maganar tana duban wayar,cikin hasala Akeela tace"Gashi kuwa kina gani,amma gaskiya ba'a mun adalci ba,inada hidima fa sosai,ga event din gobe,ranar Friday Kuma kamu haba!tayi maganar tana yatsine fuska. "Ai shikenan sai kiyi maleji da abinda yasamu kawai muma abamu kasammu,wani banzan kallo ta aika mata dashi"bangane me kike nufi ba,abaku kasanku kamar Yaya kenan?bata fuska Suby tayi tare da kura mata ido. "Ea mana ko kinmanta ana bawa kawaye wani abune?aka idama kudin nan bata account dinki ya kamata a turo ba, account din daya daga cikin mu zaki bayar mukuma muyi yanda mukeso da kudin"Zuleey tayi maganar tana tamke fuska"kwarai kuwa zuleey amma kinji abinda yarinyar nan ke cewa, Akeela wai me kika maida mu wawaye ko menene? Sauke ajiyan zuciya Akeela tayi tana kokarin danne bacin ranta"A tunanina million 3 bazai hadani da ku ba amma tunda kun matasa zanbaku 200,000 naira shikenan? "A'ah wallahi bazamu amsa ba ya mana kadan,inama lefin kibamu 1 million mu biyu? "Wallahi bazan iyaba,inama lefin 500,000?da wanne zqnji ga Kama hall da sauran su, Zuleey tana kokarin magana Suby ta hanata ta hanyar yi mata magana da ido,badon ranta yaso ba haka tadannne. "Okey to kuzo muje mufara tsare-tsaren yanda komai zai wakana,don inaso muje gidan mommy ne ko kuwa?dukka amsa mata sukayi da hakane. ******** Tarasa dalilin da yasa take tsintar kanta cikin bacin rai a duk sa'ilin da taji anyi maganar auren Sauban din,hakanan takejin wani kunci na ziyartarta tare da tsanar Akeela matuka a ranta,shikuwa mugun haushinsa takeji,a kullum cewa take bacin hadene dana su Aunty Mashahuda da wallahi bazata zauna ayi bikin ba,kai ita duk wanda taga yana rawar kafa akan lamarin na Sauban shima haushinsa takeji. Shigowa Laila tayi don bata jitaba,zama tayi tare da makama cinyar ta duka,da firgici tadago tana dubanta, ajiyar zuciya ta sauke"zuwa nayi nace miki kitashi muje mu amso dinkin mu,gasu ya Taufeeq zasu sauke mu a shagon"bata fuska tayi"Gaskiya nibazan bisu ba idan ku zaku bisu ku bisu amma ni adaidaita zan samu,takarisa maganar tana mikewa don shiga bathroom"Ummie tace nazo na fada miki idan kuma naje nabata amsar hakan to,tayi maganar tana mikewa tsaye.Cikin sauri Zuhra ta dawo tana shan gaban Laila tare da tsuke fuska"ni ban aikeki ba kice mata ganinan nashiga wanka ne,tayi maganar tana juyawa cikin sanyin jiki, dariya Laila ta kunshe tana me fita. Bata wani jima a toilet dinba ta fito ta shirya a gurguje don tasan basu fiye son delayed ba yayyen nasu,ba wani kwalliya tayi ba a fuskar ta,Dubai gown Army Green ta sanya sai sneaker black tayi Rolling kanta,dan karamin hand bag dinta baki tadauka tafita da sauri,ilai kuwa tana fita ta hango Laila da nihal a parking space jikin motar ya Sauban,wani kululin bakin ciki da bacin rai taji ya taso mata lokaci daya,harara Laila ta aikamata tace"Zaki gamu dasu Yaya wallahi babu ruwan mu kin bata musu lokaci,bata kulata ba suka bude motar suka shiga, Taufeeq ne ke driving,shikuwa Sauban laptop ne akan cinyar sa yaketa sarrafata,gaishesu sukayi duk suka amsa,cikin barkwancin sa yadube su"Allah yasa telan be mata muku dinki ba,don nasan teloli sai addu'ah,cikin raha Laila tace"Ai Yaya Ameer ya iya dinki sosai,tun daga Zaria yazo yima su Aunty Mashahuda dinkin biki,namune be gama ba yace sai munzo da kanmu,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Ah gaskiya ne tunda aka dauko tun daga Zaria to lallai nima na sheda,don nasan gimbiyar tawa bata za6en tumin dare ko gimbiya?yayi maganar yana duban Zuhra ta jikin mirror motan,dariya Zuhra tayi wanda sai da point nata ya loma,sannan Gap teeth dinta suma suka samu damar bayyana,lankwasar dakai tayi cikin shagwaba tace"To yaya maganar saloon din bamuje bafa, gashi gobe mother's day,kuma mu a goben ne zamu henna ko?tayi maganar tana duban su nihal,daga mata kai sukayi gabadayansu,nihal tace"Kuma ranar Friday kamu ba! Zuhra tasake shagwabe muryan"Yes yaya and kamu. Tun sanda ta fara magana tatafi da duk wani kuzarinsa lokaci daya yaji wani kasala ta kamashi,banda bugawa babu abinda zuciyar sa keyi,shekara da shekaru kenan yake karya ta abinda zuciyar sa ke raya masa,sam takasa tunkarar wani da maganar balle yasamu sassauci,lumshe idanuwa yayi cikin natsuwa wanda mutum bai isa yagane ya yanayin sa ba. Cikin taushe tare da basarwa yafara ma Taufeeq magana batare da ya dubesa ba"inada baki da zasuzo,wasu daga maleysia wasu kuma daga Canada so ina bukatan hotel me kyau sosa and sai dai niban san kan hotel's din garin nan ba,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Gaskiya nima bansan kan hotel's din garin ba sai dai mukira Kareem kan ya bincika mana,let me call him"yayi maganar
Chapter 26 · 0% Book details