← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 64

Sashe 30

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maryam,suka shigo,duk cikansu nufar gadon sukayi"Taba jikinta kaji Taleeb,zazzabi ne mezafi ya lullubeta"Bodejo tayi maganar,hannu yadora akan goshin nata,da sauri ya cire"Kai gaskiya kuwa, Aunty labeeba tace"Zuhra!Zuhra!!tayi maganar tana tabata. A wahalce tadan bude ido tasake lumshewa,dagota Aunty Maryam tayi tasa kanta a cinyar ta tace"Zuhra bude idanuwanki, Zuhra"Uhum! Abinda tace kenan tana rufe idon ruffff "Ikon Allah jikin nata ya canza mata ne lokaci daya,duban Aunty Maryam Taufeeq yayi yace"Aunty ya kamata muje asibiti da itane ko? Aunty labeeba tace"Gaskiya kam don wannan zazzabin ya bigeta gaskiya,dagata.Kamata sukayi suka mikar da ita,jikinta babu inda baya rawa saboda sanyin da takeji,face din har wani pink pink yake na wahala,wani mahaukacin amai ne taji yazo mata,ai kafin kace me tafara kelayarwa,haka jikinta ke cigaba da rawa,amai take sosai,sosai su ma hankalinsu yatashi,cikin muryan kuka take fadin"Abbie!Abbie!! Kamata sukayi ai ganin zata wahala ga jikinta yayi bala'in saki wani yaraf kawai take yasa Taufeeq cak yadauketa,biyosa sukayi,anan ma parlon ragowar 'yan biki suka taso ana tambayar lafiya?kowa yaganta yanda ta canza sai ya tausaya mata. **** Daddy ne da Abba da Baba Hasheem suke farfajiyar gidan da alamun daga masallaci suke,gefensu Sauban ne kansa a tsaye,gani sukayi mutane duuuu sun fito daga apartment din Bodejo, Taufeeq dauke da mutum a hannu,cikin tashin hankali suka nufi wajen suna tambayar abinda ke faruwa,a rude Taufeeq ke tambayar ya Sauban akwai car key a hannunsa?batare da yabashi answer ba yayi saurin nufar motar sa yana mata key, banda bugawa babu abinda kirjinsa keyi,tambayar kansa yake me kuma ya sameta?batare da yasan maganar zucin da yayi tafito ba yaji Aunty Maryam na bashi answer"wallahi muma haka muka sameta a sashen Bodejo,sakata a motar Taufeeq yayi yana zaunar da ita kanta akan kafadar Aunty labeeba, Aunty Maryam ma tashiga,da sauri Ummie takariso a rude take sai tambayar inda zuhran take takeyi,tayi matukar rudewa,haka Ammi dasu Mom,nufar dayan motan tayi tana cewa Taufeeq ya tada"No Ummie ki zauna a gida insha Allah komai zaizo da sauki,wani kallo ta aika masa dashi jikinta yana rawa cikin rawar murya tace"Ace min ka dauko 'yata kamar gawa?shine kake tunanin zan iya samun natsuwa?lallai Taufeeq baka da hankali"cikin daga murya tace"kabudemin mota nace! Bude mata motar yayi Saboda ganin yanda ta canza lokaci daya,Ammi ma tashiga,Adda Zainab ne tabude bayan itama da sauri tafada banda salati babu abinda takeyi,nan fa kowa yayi jugum Su Laila kuwa sai kuka da kuka Saboda a yanayin da kowa yaga anfito da ita hankalinsa dole yatashi,a 360 Taufeeq ya figi motar,tuni securities din gidan suka wawwangale gate din. "Ya Allah ya tayar da kafadunki Fatima, Amma ta fada hakan tana me juyawa,lallashin su Laila Rammat ta shiga yi tana yimusu fadan so suke su sake tayar ma da mutane hankali?su yahakuri insha Allah zata samu lafiya. Koda labarin ya isa ga Akeela sosai tayi farin ciki da hakan don har addu'ah tayi kan Allah yasa kada ma ta tashi daganan ta mace kota huta da kallon ta tana kwasar takaici da haushi. Xahratty Ce Lallai Alqalami yafi takobi 9/6/23. [6/11, 12:36] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 47/48 ....... ______wani Private hospital suka isa me kyau da tsada da alama nanne asibitin da ahalin suke hidimarsu,da isar su kuwa nurses din asibitin suka sanya ta akan gadon marasa lafiya kaitsaye emergency ward aka nufa da ita,likitoci uku ne suka tsaya akanta gefe guda kuma nurses biyu,su kuwa ahalin banda zarya babu abinda suke a dan dogon corridor din ward din sauran kuma duk sun zazzauna,idan ka kalle fuskokin su cike da alhini banda shi da yake zaune ya lumshi ido tare da jinginar da kai a jikin kujerar da yake zaune. Sunanan dai zaune har 9:30 amma babu wani likita da ya fito bare a musu cikakkiyar bayani,dubansu Daddy yayi ya soma magana"Ku tashi kuje gida dare nayi muzamu jira har Doctors din su fito muji abinda ke wakana,matan ku koma gida"yakarisa maganar yana juyar dakai gefe daya. Ummie ce tadago da niyyar yin magana amma sai takasa don Allah yasani tana tsananin girmama Daddy don musu bai taba hada ta dashi ba bare gaddama,cikin sanyin jiki suka mimmike,kallon Daddy Ammi tayi tace"Amma Daddyn su day kun bar daya a cikin mu ko kun manta cewa dole macece zata maida hankali wajen kula da ita?fuskan Daddy babu wani wasa yace"babu bukata zaku iya tafiya ga Sauban nan inma anbata gado zai zauna da ita ya kula da ita"Cikin mamaki suka dago suna dubansa,shima da sauri yabude idanuwan sa yana duban Daddyn nasa.Aunty Maryam tace"amma Yaya kamar hakan be kamata Saboda shidin ba muharraminta bane,kuma dole zata bukaci wani abu kamar shiga toilet da sauran su. Wannan karan sake tamke fuska yayi yana maida duban shi gabadaya akansu yana kokarin magana, Abba ne yarigasa"Hakan ba matsala bane kawai kuje gida don muma munsan da hakan kuma munzauna a islamiya ba jahilai bane mu. Babu wanda ya sake magana a cikinsu duk tashi sukayi suka fita ko wanne da tunanin da yake a cikin zuciyar sa, Ummie kuwa bataji dadi ba ko kadan sai dai bazata iya nunawa,cikin sanyin jiki suka nufi hanyar fita,duban Taufeeq Daddy yace"maza kaje ka maidasu gida dare nayi,amsa yayi cike da girmamawa yana me bin bayan su,muryan Sauban suka tsinkayo"Daddy taya zanyi jinyar ta?naga hakan sam be dace ba wallahi ni bansan ma yanda zan kula da ita ba. Kafin wani yabashi answer doctor's din sun fito ko wanne na share zufa,karisowa Doctor Ahmad yayi Yana duban su Daddy"Alhaji idan babu damuwa zaku iya samu na a office,yana gama fadar haka yanufi office dinsa,kaitsaye rufa masa baya sukayi. Waje yabasu suka zauna,nan suka shiga gaggaisawa da juna zuwa can ya sauke ajiyar zuciya yana duban fuskokin su"To Alhamdulillah munyi nasarar shawo kan matsalar tata ba wani abubane face damuwa wanda ya haddasa mata jinin ta yadan hau kadan tare da ciwon kai kunsan hawan jini ga zazzabi kuma a gefe daya,sai dai insha Allah munyi nasarar gano matsalar Allah yakara lafiya,amma gaskiya kuyi kokarin ganin kunji meye damuwar tata domin kuwa idan aka zuba mata ido a haka to akwai matsala,ajiyan zuciya suka sauke gabadaya Abba ne yayi karfin halin magana"insha Allah likita zamu kiyaye Allah yakara mata lafiya"Da Ameen gabadaya wajen aka amsa dashi suna me mikewa,rakasu Doctor Ahmad yayi yana tambayar me zama,duban shi yayi yace"ga Sauban nan shi zai zauna da ita yayi jinyar nata,da mamaki yake duban su don yasan alakar dake tsakanin Sauban da zuhra batare da nauyin baki ba yace"Amma Alhaji ina ganin da ansamo 'yar uwanta macece tayi jinyar ta idan ma babu sai mu duba muku a nurse's din mu. Daddy ya danyi murmushi yace"Babu bukatan Doctor Ahmad don shidin mijinta ne...... Yana kare fadar hakan sukayi gaba abinsu, daga Sauban har Doctor Ahmad kamewa sukayi a tsaye kamar status saboda mamaki,wani murmushin jin dadi Doctor yayi,yana me dafe kafadar Sauban wanda yayi suman tsaye banda bugawa babu abinda zuciyan sa ke masa yarasa me yakeji a zuciyar sa,farin ciki yake ko bakin ciki?baisani ba,cikin tsananin murna Doctor yace"Na taya ka murna oga Sauban Ashe auren gata aka maka? congratulation!wucewa yayi yana cigaba da mamaki don shima yaso ace ya mallake Zuhra a matsayin matarsa,yana tsaye jikinsa na sake sanyi,ganin tsayuwar babu abinda zai masa yasa ya juya,direct dakin yanufa cikin tafiyar da na izza da kasaita,a hankali yaka ma handle din ya murda,a makoshi yayi sallama tare da kutsa kai cikin dakin da aka canza mata (VIP) idanuwan sa kuri akan kyakkyawar fuskan ta wanda yini guda kawai yasa ya yamutse saboda ciwo,kallonta yakeyi kawai yakeyi jikinsa na sake sanyi a gefe guda yana jin taya shi zai iya rayuwa da mata har biyu?to ta inama shi zaifara?tambayar da yayi ma kansa kenan.Haka ya samu kan kujerar dake gefen gadon nata ya zauna batare da ya dena kallon ta ba yana kissima abubuwa da dama akanta,duban agogo yayi yaga sha daya da kusan rabi ne ma na dare,lumshe ido yayi batare da yanajin dadin zaman kujerar ba.
Chapter 30 · 0% Book details