← Book details Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 64

Sashe 35

Galadima Family Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da itama saina kasheta aminiyata kinema min mafita kada na hadiye zuciya na mutu wallahi bazan iya ganin Alhaji da wata mace ba,lokacin da nasha wahala na kafin yayi kudin wayasani?sai yanzu da yayi arziki ne yakeda muhimmanci?don Allah munje wajen boka hatsabibi"takarasa maganar tana tagumi da sakin wasu wahayen bakin ciki. Hajiya Aliya kuwa a ranta murmushi takeyi kawai najin dadi domin tabbas tasan idan tashiga gidan Alhaji iliyasu kashin hajiya zainab ya bushe don alkawari tadauka sai ta wulakanta ta,sai ta tozarta ta,gyaran murya tayi tafara magana"Kinga sai dai nakirashi a waya duk yanda mukayi dashi zan sanar dake amma Kisha kurumin ki muddin kinatare dani kindena zubda hawaye,me akayi akai kishiya aminiya?meyasa kike zubda hawayen ki a banza? Adda zainab dai takasa magana sai hmmm da hmmm take cewa, abubuwa sun taru sun mata yawa ga rashin samin nasara akan kanwarta bilkisou yanzu kuma ga matsalar miji ta kunno kai,sai dai taji dadi da sassaucin kalaman aminiyar tata sosai. **** Amare kuwa zama yayi dadi a gidajen biyu Mashahuda da muneefa amarcin su suke ci da tsinke ana zuba soyayya,Akeela kuwa Suby tadawo tatare a gidan tareda da wata yarinya sabuwan hannu suke biyawa Akeela bukatan ta,duk abinda ke faruwa shikam baisani ba,don shi yama fara shirye n komawa nanda 5 day's,shedanci da kazantar da akeyi a gidan Sauban ya tsananta wanda ba kowane yasani ba,domin kuwa madigo babban bala'i ce a doron kasa don har su hjy daharatu Suma zuwa sukeyi, akwai wata rana da sukazo sun gama iskancin su duk suna zaune a parlour sukaji karar door bell,lekawa Suby tayi da sauri tadawo take sanar da Akeela Guggo Laure ce,kikkimtsawa suka sakeyi sannan akaje aka bude mata kofar,tunda taga bakin fuska a gidan tafara harhada rai fuskan ta babu wani cikakken annuri,gaisheta suka fara sai dai dakyar take amsa musu,ganin haka yasa suka tattara yanasu yanasu suka bar gidan,koda suka watse cike da masifa Guggo Laure tafara magana"Ashe Akeela har yanzu bakiyi hankali ba?har yanzu bakidena tara wadannnan tambadaddun yaran ba?wai nikam sai yaushe ne zakiyi hankali?wallahi kikiyaye wadannan yaran,daga ganin idanunsu a soye gogaggun 'yan iska nefa.A raina nace _hajiya Guggo Laure kenan ita Akeelan bakiga gogewan nata ba saina yaran wasu kike hangowa?_ bata fuska Akeela tayi batare da tayi magana ba don tasan yanzu tadinga naci kenan,can dai tace"Guggo zan kiyaye don Allah kibar maganar haka"katseta tayi cikin fada"bazan bar maganar ba aikece kikajawo tun yaushe nake rabaki da wadannan yaran amma bakijin magana?harda wadanda sunma haifeki amma kince a makarnat kuka hadu,wallahi zan gayawa mansir dinner tunda ke bakijin magana,ni don Allah tashi kisama min abin Kari me kyau da soyayyen kwai guda bakawai"tayi magana tana gyara zamanta a kujerar,mikewa Akeela tayi tana mejin haushin zuwan nata a dai-dai wannan lokacin,don harga Allah batason ba don bawai ta gamsu bane,da alama kuma Guggo Laure yini zatayi.Bata wani Jima ba tahado mata lafiyayyen breakfast. A dai-dai lokacin da su hajiya daharatu suka fito a lokacin ne kuma sauban yafito daga sashen sa don raka wasu bakinsa,ganin shi yasa duk suka gigice don kwarjinin sa da kyansa na tafiya da 'y n mata da dama,jikinsu na rawa suka shiga gaisheshi shida abokansa,abokan duk sun amsa amma shi ko tankawa beyi ba illa nazarin su day yashiga yi ganin sam ba mutanen arziki bane,sai dai yaso yagane Suby,cikin sauri suka bar gidan. Shima raka abokan nasa yayi koda yadawo apartment din sa yawuce dai dai nan kuma wayansa tayi kara alamun message yashigo,bayan ya zauna ne yajawo dinsa har zai bude sai kuma yatuna abu yashigo dazu don haka yabude wayan,kaitsaye ta wahtsapp yaga notification din tunda always data a kunne ne,shiga yayi still da number da akaturo masa messag3 din kwanaki still dashi aka turo wannan kuma duk video's ne,shiga cikin profile din yayi,ko bude pics din dake DP din beyi ba,gani yayi an rubuta....batare da yabi takan komai ba yaja tsaki,jawo laptop dinsa yayi ya kunna don sunada meeting da ma'aikatan company nasu shi ta video call zaiyi don an bashi hutun amarci gashi saura 5 day's yakoma. Xahratty CE Lallai Alqalami yafi takobi 20/6/23. [6/24, 17:31] Xahratty (OUM AJMAL): *_GALADIMA FAMILY_* Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 55/56 ______Zaune suke cike da so da kaunar juna suke hirarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi,zaune suke akan plastic chairs kamar dai yanda suka saba,bude gate din security sukayi anan motoci biyu suka kunno kai cikin gidan,motar gaba ta Daddy ce ta biyu kuma kirar Benz ta ya Sauban, ZUHRA jitayi kirjinta ya shiga dakan lugude don wannan shine rana ta farko dasu Daddy zasu kamata a irin wannan yanayin,sannan tabbas tasan dokan gidan,balle murfin motar sukayi suka fito Daddy da Baba Hasheem tun daga nesa idanuwan su Daddy ke kansu,shikuwa Sauban kallo daya ya musu ya kauda kai,ganin sun kawo kusa dasu tunda dai-dai apartment din Ammi dama suke zama cikin sauri zuhra ta nufesu, cikin girmamawa tafara magana"Daddy sannu da zuwa, Baba sannu da zuwa"amsawa sukayi duk cikan su suna duban Shuraim wanda yake karisowa,cikin girmamawa Shuraim ya duka ya shiga gaishe dasu Daddy,face dinsu Daddy kadaran kadahan suka amsa,zuwa can shiru yaratsa wajen,dubanshi Daddy yayi yace"gashi kuma bamu gane ba malam daga ina kake?dan sosa kai Shuraim yayi yafara inda saboda ganin da yayi zuhra ta koma tsumu-tsumu. Baba Hasheem da yaga gane duk abinda suke 6oyewa da yanayin zuhra yace"tambayar ka ake daga ina kayi shiru?yayi maganar cikin dan hassala,cikin sauri Shuraim yace"Dama wajen zuhra nazo hira"Baba Hashim yace"Hira kamar Yaya?Shuraim yace"dama nida zuhra son juna muke kuma nida niyyar aure nake son ta bada wasa ba.Shiru duk sukayi suna zubanya mishi na mujiya,ita kuwa zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi don tabbas tasan idan ba'ayi wasa ba to tata takare yau. "Bakasan tana da iyaye bane da bakazo kanemi izinin su ba kafin kafara zuwa wajen ta? Baba Hasheem yayi ma Shuraim tambayar face dinsa babu alamun wasa ko kadan,shikan shi Shuraim yasha jinin jikinsa musamman da Baba Hasheem,cikin sauri yace"Nasani Baba,sai dai nayi kokarin zuwa sai.....yayi shiru batare da yakarisa ba,"Baba Hashim yace"sai kuma baka zoba?maida duban sa yayi ga zuhra yace"kin kyauta tunda kece keda iko da kanki? yanzu har kinyi girman da zaki kira saurayi yazo zance gidan ku batare da kingama makaranta ba?batare da annemi izinin iyayen ki ba?shiru zuhra tayi jikinta babu inda baya rawa. Cikin daka tsawa dayasa Ammi dasu Laila fitowa yace"Ba magana nake miki ba kike girgiza min kai kamar kadangaruwa? Cikin muryan kuka zuhra tace"don Allah Baba kuyahakuri"girgiza kai kawai Daddy yayi sannan yayi gaba, Baba Hasheem yace"kin kyauta domin duk abinda yafaru kece sila,kenan a school dinma samari kike kulawa ba karatu kikeyi ba kenan?da sauri zuhra tadago tana girgiza kanta hawaye na mata zarya. Batare da yasake magana ba ya wuce, Sauban ma bin bayansa yayi,zuhra kuwa atake anan ta duke tana me salkin wani irin kuka me ban tausayi domin bata kawo zuwan ranar nan kusa,shikan shi Shuraim hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,duban ta yayi cike da tausayawa, Ammi ce takaraso wajen tana me kama zuhra suka nufi cikin apartment dinta,jikinsa yayi bala'in sanyi,a gefe daya kuma ga tausayin kawunan su,dama a waje yake parking motar shi,direct gate ya nufa ya fice daga gidan gabadaya. Haka dai takara sa yinin ranar tayi shi sukuku babu walwala ga tarin fargaba da ya hadu ya mata yawa don kuwa tabbas tanaji a jikinta shirun Daddy ba alheri bane. Bayan sallan isha'i zsune take a dinning sam abincin takasa ci tsakura wa kawai takeyi,sam bakinta babu apatite hakanan tarasa abinda ke mata dadi,Laila ce tashigo cikin sanyin jiki ta dubeta"Sis kitashi kije Daddy nakira wai suna parlour Galadima"jitayi kirjinta ya tsananta bugawa fargaban ta yakaru,ko kaffara bazatayi ba tabbas akanta ne za'ayi wannan zaman,mikewa tayi cikin sanyin jiki tana duban Laila idon ta na cikowa da ruwan hawaye,dafa kafadanta kawai Laila tayi tana mejin tausayin 'yar uwan tata. Cikin sanyin jiki ta yafa gyalin Egyptian gown din dake jikinta tanufi apartment din Bodejo,da sallama tashiga parlour,zaune suke Galadima, Bodejo, Daddy, Baba Hasheem, Ammi, Ummie, Mom sai kuma Sauban dake zaune gefen kafar Galadima ahankali takarisu parlour cikin sanyin jiki,wani irin kallo Ummie ke aika mata dashi don ita batasan meyafaru ba sai a bakin Mom takeji. Zama tayi akan hadadden carpet din wanda ya qawata parlour sosai,gaishesu tashiga yi cikin jam'i,cike da tsokana Galadima yace"feel free mana amaryas,sai kame kikeyi ba?ai asirin ki ya tonu wato nema kike kimin Kishiya saboda kinga natsufa ko?to komin abinki ba'a canzawa tuwo suna"yakarasa maganar yana gyara zaman shade din fuskan sa, Bodejo tace"Hmmm ai kayi kagama ni me kishi dani sai ya shirya"duk dariya aka Sanya banda Sauban daketa daddana wayar,shiru ne ya gifta zuwa can Daddy yayi gyaran murya yana duban zuhra"mamana! Muryan zuhra na rawa tace"na'am Daddy, Daddy yace"kinsan zaman nan akan wa mukayi shi ba sai anyi dogon jawabi ba ko?daga kai zuhra tayi alamun Ea. Daddy yace"Masha Allah,tunda muke a gidannan tun kama daga kan Addojinki su Maryam babu wacce tataba kula wani saurayi kafin aure hatta su Mashahuda batare da anzo annemi izinin mu ba,kece ta farko da kika fara karya dokar gidan nan harki dinga kula wani saurayi ku kulla soyayya batare da duk munsani ba,bazan boye miki ba raina yayi mummunan 6aci domin kuwa hakan babban zunubi ne agareki. Shiru parlour ya dauka zuwa can ya cigaba"nema kike ki maida mu mutanen banza?a'ina har kika samu karfin gwiwwan haka?waye shi a'ina kuka hadu?jikin zuhra yasake sanyi muryan ta na rawa ta shiga basu labarin haduwar ta dashi tundaga farko har karshe,cikin muryan kuka tace"wallahi Daddy ba karya nakeyi ba ka tambayi Aunty Mashahuda da Aunty Safeena,domin dan uwan Ouncle Asheer ne,sosai tabawa su Daddy tausayi amma sukaki nuna mata hakan,cigaba da magana tayi"sannan yaso ya sameku nice na hanasa nace sai na gama school amma don Allah kuyahakuri bazan kara ba. "Hmmm abinda yasa muke hanaku kula da wasu mazan ba komai bane face gudun matsala,domin ke akanki hakan ne ke shirin faruwa dake domin akwai aure akanki"ai a gigice Ummie, Mom,zuhra ke duban Daddy, Ammi kuwa mamaki ne ya kashe ta,jikin ta babu
Chapter 35 · 0% Book details