← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 104

Sashe 99

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "Toh ae gwara da kika tada ni, xan yi tsayuwar dare dama" Zahrah tace "Ina take ita?" Hajja ta tabe baki tace "Ae kya bar ni budurwa" daga haka ta mike tana salati ta shiga bayi, mikewa Zahrah tayi ta koma tayi kwanciyarta, da asuba hajja ce ta tada ta tayi sllh, tana idarwa tana daga kan darduman ta gaida Hajja dake ta jan carbi, Hajja ta amsa tace "Kin tashi lafiya?" Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace "Amma kina da ciwon baki koh? Naga kmr magana na maki wahala?" Murmushi Zahrah tayi, Hajja tace "Toh ae ba abun dariya bane sai in sa a sama maki Magani...." Zahrah tace "A'a lafiyata lau!" Hajja tace "Tohhh! Kuna waya da mutan gidan ku?" Girgixa kai Zahrah tayi, Hajja tace "Sbda me" Zahrah tace "Ba waya" Hajja tace "Baki xo da waya bane dama?" Girgixa kai kawai Zahrah tayi, Hajja tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka bata sake cewa komai ba, can Hajja tace "Dawo nn in maki tambaya" mikewa Zahrah tayi ta koma kusa da ita ta xauna, murya can kasa Hajja tace "Halan gudun mijin ki kike?" Girgixa kai Zahrah tayi ba tare da ta kalleta ba, Hajja tace "Anya? Toh wace gulmar ta kawo ki nn jiya Idan ba gudunsa kike ba?" Zahrah tayi murmushi ta girgixa mata kai, Hajja tace "Ke ki fa bude baki ki min magana" a hankali tace "Ni dama a nn nake kwana" Hajja tace "Toh har ya maki kwanakin ki bakwai ne?" Kai Zahrah ta gyada mata, Hajja tace "Karya kike" murmushi Zahrah tayi ta mike tace "Zan je kitchen" daga haka ta fita Hajja ta bi ta da kallo tace "Ikon Allah yau naga halitta" Breakfast Zahrah ta shiga kitchen tana hadawa, cikin minti arba'ain ta gama soye soyen, ta kuma dafa hadadden lipton mai kamshi ta kuma dau nama a deep freezer ta gyara tayi pepper soup da shi, bakwai da kusan rabi ta kai ma Hajja nata, Hajja dake kan darduma har lkcn tace "Ahhh, Dama kuna girki 'ya yan gidan sarauta, to wa ya koya maki girkin?" Murmushi Zahrah tayi ta ajiye mata ta hada mata tea snn ta mike tace "Zan yi wanka" daga haka ta fita ta koma dakinta, ta fito daga wanka tana gyara gashinta aka bude kofar dakin, juyawa tayi, tayi masa kallo daya ta dauke kanta, sanye yake da uniform, hannunsa rike da hularsa ya karaso cikin dakin har ya iso bayanta yace "Ashe an koya maki girki gidan ku" bata ko kallesa ba bare yasa ran samun amsa, kwace comb din hannunta yayi, ta jawo mai xata shafa ya karbe man, wani man ta kuma dauka ya kwace duk ya jefar da su kan gado, tana son tashi amma ta kasa sbda tawul kadai ta daura, gashi yana bayanta, ta madubi yake kallonta shi ma ya hade rai yanda tayi, "Pls ka daina shiga rayuwata Ahmad" bai san lkcn da murmushi yayi escaping lips dinsa ba yace "Ohh really kinsan sunana ashe" mikewa tayi kafin ta bar gun ya rikota, turasa take son yi amma ta kasa, kawai ta saki kuka, buda ido yayi yace "Kuka?" Ganin yanda take kukan sai ya tuno masa da lokacin da take da disorder, ya ji duk jikinsa yyi sanyi, ya kamo hannunta suka koma gefen gado ya xaunar da ita cikin sanyin murya yace "Ohk ohk... Am... am sorry princess, am sorry Jasmine" ganin taki daina kukan bai san lkcn da ya rungumeta ba ya lumshe ido a hankali yace "I said am sorry xan bar shiga rayuwar ki...." A hankali ta tsaida kukan nata, dogon gashinta ya kama ta fixge gashin a hannunsa, murmushi yayi murya can kasa yace "Jasmine dita ta da ba haka take ba, she alwayz wants to be with her Captain, always happy when ever she see's her captain, she alwayz want to do everything with her captain, she's timid, she's alwayz afraid, she's innocent, the sweetest of all, she's alwayz happy and free, she was never arrogant, she don't have I don't care altitude, she never say who she is, she's full of respect, and the amazing of all, she changed me to what I am today, she....." Shiru yayi ta dalilin dago kai da tayi tana kallonsa da manyan idonta, lallausan murmushi ya sakar mata yace "Yeah, I want you to go back to ur former self..." Agogo da yayi stuck din karfe takwas ya sa shi bude ido yana kallon wristwatch dinsa yace "You made me late for work...." Bai karasa ba sai ji tayi ya fara kiss dinta, don kansa ya mike ya fice daga dakin daga karshe, haka ta bisa da kallo har lkcn ta kasa motsi inda take. Da kyar ta mike bayan ta ji fitar motarsa ta shirya cikin atamfa riga da skirt tana xaune gaban mirror tana sa xobunayen zinari guda biyu da ta fito da daga kayan lefenta Hajja ta shigo dakin, tace "Har yanxu wanka yar nn" kallonta tayi tace "Na gama kaya nake sa wa" Hajja tace "Ashe komai iri daya ne na dakunan naku" Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace "Toh taho ki hada min ruwan wanka wancan so mijin na can dakinsa tana sharbar bacci" mikewa Zahrah tayi tace "Toh bari in hada maki a nan" Hajja tace "Toh hada, ko kefa da kike bude baki kike magana yanxu" murmushi Zahrah tayi ta shiga bathroom dinta, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Ga ruwan can na hada" Hajja tace "To tafi ki bude jakata xaki ga wani sabon atamfa duk yafi sauran sabonta ki dauko min, nima kwalliya zan yi yanda kika yi kar ina ji ina gani ki raba ni da Amadi in shiga uku" Dariya Zahrah tayi tace "Kai!" Daga haka ta fice daga dakin, Hajja tace "Ashe dai kina dariya 'yar ayi" ko da Humainah ta fito misalin Karfe goma Hajja na dakin Zahrah har lokacin ta cikata da labaran duniya, ita dai Zahrah ta tallabi kuncinta ne tana kallonta, wani lbrin yasa ta fashe da dariya, wani kuma ta xaro ido wani kuma ta bata fuska, sha daya ta shigo dakin ita ma ta xauna tana kallon Hajja tace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Ahh lafiya lau so miji, sai yanxu kika tashi?" Zahrah ta sunkuyar da Kai kar tayi dariyar da ya taho mata, Humainah ta turo baki tace "Ehh" Hajja tace "Toh Allah ya kiyaye, kun gaisa da takwarar tawa" Humainah ta d'an kalli Zahrah tace "Kin tashi lafiya" Zahrah tace "Alhmdllh" nan dai Hajja ta ci gaba da labaranta masu kai da marasu Kai, gyangyadin da ta dinga yi tana labarin yasa Zahrah ta sauko mata da pillow tace "Toh ki kwanta sai ki ci gaba da labarin" ai ko tana kwanciya ta bingire da bacci, Humainah tayi murmushi ta mike ta fita don daura lunch, bayan kusan minti talatin da fitan ta Zahrah ta mike ta fita don taya ta. Da yamma tun kan Junaid ya dawo Hajja ta hada kayanta wai yana dawowa xai maida ta gida, Humainah tace "Dama ba sati daya kika xo mana ba hajja?" Hajja tace "Ba gantalalliya nake ba ai" Zahrah tace "Toh ki Bari gobe alhamis mana" Hajja tace "Toh ai ba yar iska nake ba" dariya suka yi gaba daya banda ita dake ta faman xuge jaka, tana gamawa tace "Toh dai ayi xama na Allah da annabi banda munafurci da munafukin kishi mara ma'ana, ku dau kan ku kamr yan uwan juna, ke Zahrah ki bar gudun mijin ki, ke kuma Humainah in ma ta shigo dakin ki ki korata idan ba son amshe kwananta kike son yi ba, ni har kishiyata ta rasu sau biyar muka taba dambe da ita, cacan baki kuwa mun yi yafi sau hamsin, Amma lafiya muka xauna bbu tashin hankali shi yasa ku ka gan ni da kyau yanxu, shi kuma salubabben mijin naku xai dawo ya sameni" dai dai nan aka bude gate Hajja tace "Toh Alhmdllh gashi can ma," Junaid na shigow a Hajja tace "Taho ka xauna nn, nasan sokanci baxai bari Ka hada su kayi masu magana kamar yanda nayi yanxu ba" *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 90____91 Har bayan 2 dayz Junaid bai kuma kallon inda wives din nasa suke ba, yana dawowa daga aiki baya fitowa daga bedroom dinsa, su ma ko damuwa ba su nuna sun yi ba barin Zahrah, yanda suke abubuwan su sai ka rantse ba kishiyoyi bane duk da ba wai wani magana can suke ba amma ko da yaushe suna tare, nace to ko don basa nuna sun damu da mijin kamar yanda shima yake nuna bai damu da su bane oho, gwara Humainah idan sun hada ido tana gaishesa duk da baya bin ta kan gaisuwar nata, Zahrah kam ko kallo bai isheta ba, wani takaici yake ji har cikin ransa, kuma ya rasa abinda yasa yake jin haushin halin ko in kula da suke nuna masu, ranan asabar yana kwance daki kawai ya mike ya fita, downstairs ya sauka jin kamar girki ake don a tunaninsa Humainah ce, Zahrah ya gani kitchen din tana juye dafaffen shinkafa a warmer, kallo daya yyi mata ya fice ita ko duk da taji alamar shi ne bata ko dago kanta ba, sama ya koma ya bude kofar dakin Humainah ya sameta kwance, tana ganinsa ta mike xaune, xaunawa yyi gefen gadon yana kallonta yace "Irin kema kin tsiri wani hali da ba naki ba yanxu koh?" Bata ce komai ba ya hade rai yace "Magana nake maki malama" turo baki tayi tace "Toh me nayi?" Yace "Bbu ruwana da abinda kika yi, just that daga yau idan Zahrah ta shiga dakin ki just leave the room for her nd come to my room, nd daga yau kika sake min gaisuwar rainin wayo a parlor xaki sha mamaki, infact bedroom dina xaki dinga xuwa gaisheni daga yanxu, and... I don't care altitude din da kika tsira ma ya tsaya iya idan bana gidan nn, duk girkin da xa ayi ki tabbatar kin kai min bedroom....." Kallonsa take kawae, can tace "Ae bni kadai bace matar ka naga" mikewa yyi strictly yace "Ke kadai nasa hakan, if you want to
Chapter 99 · 0% Book details