← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 104

Sashe 64

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ci a nan ta koma sama. Da yamma misalin karfe hudu saura Humainah na dakinta bayan ta daura girki a kitchen ta ji an danna bell, mikewa tayi ta fito dai dai lokacin da Jasmine ma ta fito, ko kallonta bata yi ba ta sauka, bude kofar parlon tayi ta ga yarinyar jiya a tsaye, murmushi yarinyar tayi tace "Kin gan ni kuma koh, daxu aunt dina ta dawo na taho, yanxu ma gida xan koma nace bari in shigo mu gaisa" Humainah ta d'an yi murmushi ita ma tace "Toh sannu da xuwa" hanya ta bata ta shigo ta xauna parlon, yau ma kamar jiya ruwa ta kawo mata, yarinyar sai hira take mata kamar sun dde da sanin juna, ita dai Humainah duk ta kasa sakewa, Jasmine ta shigo parlon tana kallon Humainah tace "Anty ki kira min Uncle" Humainah tace "Bani da waya" Jasmine tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta juya ta koma sama, yarinyar da ta kira kanta da hadiza tace "Amma wacece yarinyar nan?" Humainah tace "Kanwar mijina ce" Hadiza tace "ohh, Allah sarki, amma basa kama ko dai 'yar uwar na family kike nufi" a takaice Humainah tace "Eh!" Don duk ta kagu ta wuce sai kallon agogo take sanin hudu da wani abu junaid ke dawowa wani time, Hadixa tace "Toh dai ki kula" Kallonta Humainah tayi da sauri, hadiza tace "Naga yanda take wani shige masa jiya da na xo" murmushi Humainah ta kirkira bata ce komai ba, hadiza tace "Ae ba abun dariya bane, ni ma nan da kike ganina na kusa dawowa anguwar gaba daya gun aunt din nan tawa sbda damuwa da yayi mata yawa, in gaya maki wata yarinya mijinta ya ajiye wai yar uwarsa xata yi karatu a gidan, in kinga yarinyar very quiet har ni ke ce ma Anty fa'ixa ta dinga sake mata don Allah don ko kallonta bata yi, to yanxu xancen da nake maki Friday mai xuwa daurin auren mijin yayar tawa da yarinyar" kallonta kawai Humainah ke yi gabanta na mugun faduwa, hadiza ta dawo kusa da ita tace "Bari ki ga hotunan aunt din tawa da yarinyar har ma da mijin" kallon hoton kawai Humainah ke yi amma sam hankalinta baya jikinta, bude gate din gidan aka yi, hadiza ta bude ido tace "In ji dai ba mijin naki bane ya dawo" kasa ce mata komai Humainah tayi, Hadiza tace "A'a kin ga ki fa kwantar da hankalin ki, ai ba duka maxan suka taru suka xama daya ba kawai ke dai ki sa ido" Humainah bata ce komai ba still har junaid ya shigo parlon, daga bakin kofa ya cire takalman kafarsa ya bar bakar safar, kallonsu kawai yake a parlon lokaci daya ya hade rai, ya nufi stairs hadiza ta bisa da kallo ta d'an bude murya tace "Ina yini" a tunanin ta jiyan da ya shareta bai ji bane, ko kallonta bai yi ba bai kuma amsa ba ya haura sama, hadiza tace "Toh bari in wuce naga kamar mijin ki bai son baki" Humainah tace "Rabu da shi" dariya Hadiza tayi ta mike tace "Toh Hajiya Humainah kinga tafiyata, gobe ko jibi xan ma dawo anguwar baki daya" Toh kawai Humainah ta iya ce mata ta rakata har bakin kofa ta wuce sannan ta dawo ta tafi sama, tana shiga daki ta xauna gefen gadonta tana tunanin maganganun Hadiza, bude kofar dakin aka yi ya shigo fuskar nan tasa a daure ko uniform bai cire ba don fitina yace "Wace yar iskar ke xuwa gidan nan?" Ko kallonsa bata yi ba ta dauke kai, ya karasa ya fixgota yace "keh! Baxa ki gaya min wacece ita ba?" Fixge hannunta tayi tace "Mutum ce kuma ai ka gane ma idonka" yace "Koh? To wllh wllh ta sake xuwa min gida xan baki mamaki daga ke har ita" daga haka ya juya ya fice, kuka ta saki duk ta rasa me ke mata dadi sosai xancen hadiza ya xauna a xuciyarta, mikewa tayi ta sauka kasa ta kashe girkin da take ta koma daki. Har bayan magrib junaid na xaune daki duk abinda ya ma El-ameen jiya ya tsaya masa ya rasa yanda xai yi, ta yaya ma xai ce yana son Jasmine, wani irin so ma yake nufi, mikewa yayi daga karshe ya dau makullin motarsa ya fita, ana kiran isha ya isa gidansu El-ameen, sai da yayi sllh a masallaci sannan ya shiga gidan, xaune ya samesa a daki da faisal, faisal na ganin junaid ya bude ido yace "Captain junaid, ashe ana ganin ka" murmushi junaid yayi ya xauna yace "Kai ma ai ba ganin naka ake ba" hira suka d'an yi da faisal, shi dai El-ameen wayarsa kawai yake dannawa, daga bisanni faisal yayi masu sallama yace xai tafi clinic ya fita, Junaid ya kalli El-ameen da ya ki kallon inda yake yace "Har da wani pretending baka gan ni ba?" Ba tare da El-ameen ya kallesa ba yace "Ai mun gaisa" Junaid ya d'an shafa kai yace "Look, am sorry about what happened yesterday, I don't know what came over me....." Katse sa El-ameen yayi yace "It's ohk, I also don't know what came over me, i was just confused, I couldn't help it... May be dat was y I uttered those words" shiru junaid yayi yana kallonsa ganin he was so serious, El-ameen yace "Yess!" Junaid yace "No idan ma sonta kake da gaske ai ba komai bane, just pray memorynta ya dawo a maidata gun iyayenta nd then you can go on...." Shiru junaid yayi don jin maganar yayi wani iri a bakinsa, El-ameen yace "Noo, ni an min mata ai" Junaid bai kuma cewa komai ba sai bayan kusan minti uku yace "Ohk gobe da yamma ka raka ni ayi enrolling dinta a islamiyya, she so need it yanxu, ita kuma Humainah is resuming school" El-ameen yace "Ohk" junaid na kallonsa yace "akwai shirye shiryen da xa ayi ne na bikin?" No kawai El-ameen yace masa. Washegari Tuesday junaid bai bari Humainah ta je school ba don bai son barin Jasmine ita kadai a gida sai sunyi registering dinta a islamiyya, haka Humainah tayi ta kumbure kumburenta ya wuce aiki abun sa, kwata kwata ranan bata sake ma Jasmine ba, sai taji ina ma Hadiza xata xo ranan ma amma har Junaid ya dawo bata xo, bai damu da girkin da bata yi ba don sai ya ci abinci yake dawowa, Karfe biyar saura ya shiga dakin Jasmine ya ganta kwance tayi jigum, tana ganinsa ta mike xaune yace "Sa hijab din ki ki fito" ba musu tai yanda yace ta fito parlor, sai ga Humainah ma ta sauko ta tsaya bakin stairs tana kallonsu ta wani hade rai, Ko kallonta junaid bai yi ba yana kallon Jasmine yace "Mu je" ta bi bayansa xa su fita Humainah ta rufe kofar tana masa wani kallo sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni wllh xan hada ka da Abba na gaji haka kuma" Jasmine dai sai kallonta take, junaid ya fixgota yace "rashin kunyar ki ta da ne xai dawo koh?" Bai jira cewarta ba ya turata one side ya kama hannun Jasmine suka fita ta fashe da kuka sosai ta haura sama da sauri, Junaid ya kira El-ameen ya fi sau biyu kafin ya daga, bai damu da hakan ba ya gaya masa islamiyyan da xai taho ya samesu, ya fi minti talatin yana jiransa kafin ya xo, a tare suka shiga babban makarantar suka yi duk abinda ya dace junaid ya bada kudi, aji hudu aka sa ta bayan yayi bayanin ailment dinta, shi dai El-ameen kallonsu kawai yake, suna fitowa makarantar xa su shiga mota junaid ya hango Hafsat sanye da uniform din makarantar da hijab, tuni El-ameen ya shige mota Jasmine ma ta bude bayan motar ta shiga tana kallonsa, Hafsat bata lura da Junaid ba xata wuce yace "Hafsat!" Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, murmushi yayi yace "kwana biyu" dawowa tayi ita ma tayi murmushin tace "Alhmdllh" yace "Nan kike knn" kai ta gyada masa, ganin duk tayi wani iri yana kallonta yace "Baki da lafiya amma koh?" Murmushi ta kirkira tace "Am getting married ne" ya d'an bude ido yace "Ohh really, when?" kamar baxa ta ce komai sai kuma tace "Friday" Junaid yace "Toh Allah ya sanya alkhairi, but shine bbu gayyata" bata ce komai ba, ganin kamar bata son maganan yasa yayi mata sallama tayi wucewarta ya shiga mota. *Haske Writers association* [3/19, 9:22 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 56..... Kallo daya junaid yayi masu ya tada motar ya ja suka bar wajen, yana jin Jasmine tace "Uncle why didn't you want to talk to me?" Ba tare da El-ameen ya kalleta ba yace "Am meditating!" Ta wara ido tace "Ohh What's that?" Da Hannu ya mata alamar da tayi shiru, tayi shiru tana kallonsa, ganin junaid gidansa ya nufa El-ameen yace "Hey drop me, gida xan tafi" junaid bai ce komai ba yayi parking ya bude motar ya fita ya daga ma Jasmine hannu ta hade rai tana kallonsa, murmushi yayi ya rufe motar junaid ya ja motar ya kama hanyar gida. Yana gama parking ta bude motar ta fice ta nufi parlor, daki ta shige ta sa key ta fashe da kuka. Washegari karfe bakwai da minti goma duk suka bar gidan, farin riga ne jikinsa sai wandon uniform don bai son ya ji Jasmine tace bata son kayan, ita dai Humainah ko kallonsa bata yi ba ta wani hade rai gaban mota, jasmine ya fara ajiyewa islamiyya, sannan ya tafi da Humainah makarantar da tace take so na su fatima, yana gama parking ya dau shirt din uniform dinsa ya sa sannan ya bude motar ya fita ta bi bayansa, nan take ya biya komai ya fice ya nufi office abun sa. Da yamma yana barin gun aiki Jasmine ya fara xuwa dauka don hudu suke tashi, da fara'arta ta karaso gun motar, kamar daxu da safe bbu uniform jikinsa sai wandon, ta wara masa ido tace "Captain nayi frnds guda uku, kuma suna koya min karatu I like them" kai kawai ya gyada mata ta bude motar xata shiga yace "Koma baya"
Chapter 64 · 0% Book details