← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 104

Sashe 58

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

yakeyi, ido ta lumshe tana sauk'e ajjyar zuciya, cikin wata iriyar murya yace "am sorry Jasmine", itadai shiru kawai tayi tana sauraronshi, a hankali ya janyeta daga jikinshi ya d'ago hab'arta yace "am sorry okay?", yasa hannu ya share mata hawayen dake fuskarta, gaba d'ayanta yarinyar tausayi take bashi, mik'ewa yayi tareda kamo hannunta ya tayar da ita yace "Kinyi Sallah?", kai ta girgiza mishi yace "kiyi min magana, don't nod", a hankali tace "banyi ba", yace "Shiga kiyi alwala, I will b here waiting for you", ba musu tayi hanyan toilet d'in dake palo, saida taje bakin k'ofa snn ta sake juyowa taga ita yake kallo kamin ta shige toilet d'in, yana zaune ta fito ta d'auki hijab d'inta dake gefe ta saka, har ta idar da Sallah idonshi na kanta yana observing yanda take Sallahn, ta d'an jima zaune bayan ta idar snn ta kalleshi tace "Av prayed, nace Allah ya bani lafiya", kai ya kad'a yace "that's good, kullum ki dinga yin haka kinji?", tace "toh", ya mik'e yana maida wayarshi aljihu yace "zaki rakani?", kallonshi ta tsaya yi da manyan idonta kamar batasan mey yace ba saida yayi murmushi snn yace "I mean would you like to go out with me?" Har zatayi nodding kanta tayi maza tace "Toh", yace "Good saka Hijabinki mu tafi", tana gama sawa ta dubeshi da manyan milky eyes d'inta tace "Shoe d'ina ban ganshi ba kuma nace na barwa waccan Aunty", kallonta yayi kawai yace "muje, we will buy another one", lokaci lokaci yake juyowa ya kalleta yana driving, itakam kanta ta jingina jikin glass tana ta kallon garin, a Jifatu yayi parking, ce mata yayi ta zauna ta jirashi ya shiga ya gama siyayyan da zaiyi snn ya fito, takalmin da ya mik'a mata ta saka tana jin dad'i snn ya wuce dasu Royal Joint, a nan yayi musu order abinci suka wuce gida, hannunshi riqe da abincin da ya siyo ita kuma riqe da na shoe d'in da ya siya matan, suna shigowa gida daidai nan Humainah na sauk'owa kan bene, wani irin fad'uwa, da murna Jasmine ta kalli ledan shoes dake hannunta snn ta kalli Humainah dake tsaye tace "Aunty kinga new Shoe d'ina da wannan Uncle d'in ya bani, he is nice, kema kice mishi kinaso ya baki", Humainah dake tsaye gabanta na bugawa juyawa tayi ta koma d'aki, Jasmine ganin ta tafi yasa ta juyo da kallonta ga Junaid da yake kallon inda Humainah tabi, tace "Aunty nan ma A siya mata irin shoe d'ina", kallonta kawai yayi yace "Jeki d'auko plate", ledan da yake hannunta ta ajiye tayi kitchen, zaune ta tarar dashi yana danna waya, d'agowa yayi ya dubeta ganin ta tsaya mishi a ka yace "Sit down and serve yourself the food", zama tayi ta janyo leda d'aya ta bud'e ta shiga zuba fried rice d'in a plate ta fara ci, tashi yayi ya d'auki d'ayan ledan ya haura sama dashi, d'akin Humainah ya tura duk wutan d'akin kashe yake, kunnawa yayi ya k'arasa shigowa, a tsakiyan gadon ya ganta kwance ta dunqule waje d'aya, zama yayi bakin gadon bayan ya ajiye ledan hannunshi, sau biyu yana k'iranta yajita shiru, a hankali ya d'agota dan yasan ba bacci take ba, fuskarta da ya kumbura dan kuka ya k'urawa ido , hannu yasa ya shafi hawayen yana murzawa da d'an yatsanshi yace "Sana'ar da kika samu kenan yanzu?", turashi ta shiga yi daga jikinta, firmly ya riqeta, ganin ta kasa kwace kanta yasa ta fashewa da wani irin kuka tana sulalewa k'asa tace "ni ka sakeni ka fitamin daga d'aki", har ranshi yakejin kukan nata, d'agota ya sakeyi yace "Humainah mey ke damunki wai for crying out Loud?, me kike so?", shiru tayi mishi taqi cewa komai tana ci gaba da kukan, a hankali ta d'ago tana share hawayenta tace "Ka maidani gidanmu, inason ganin Abba na", wani irin kallo ya bita dashi *Haske Writers association* [1/14, 9:17 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 50..... Washe gari ma kamar jiya haka suka wuni gidan, yana zaune d'akin Humainah da tayi kamar batasan da zamanshi ba, Mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma nasa, yana danna wayarsa yaji kamar ana sallama bakin kofa, tashi yayi ya isa gun kofar ya bude ya ganta tsaye, a hankali tace "Nace Assalamu Alaikum!" D'an murmushi yayi yace "Gud! Ya aka yi?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Kin gama cin abincin?" Gyada masa kai tayi yace "toh mu je" fitowa yayi daga dakin ya shiga wanda take ta bi bayansa, ya xauna gefen gado ta karaso ita ma ta xauna daga kasa inda yake, yace "No dawo ki kwanta kiyi bacci" tace "I've not bathed" mikewa yayi ya shiga toilet ya hada mata ruwa ya fito yace "Toh tafi kiyi" ta mike ta cire hijab ta shiga toilet din ya bi ta da kallo, fita yayi daga dakin jin kamar wayarsa na kara ya shiga nasa dakin, 1st love ya gani jikin screen din, ya dau wayar ya xauna sannan yayi picking hade da yin sallama, Mumy ta amsa ya gaisheta ba tare da ta amsa ba tace "Ina Humainah" kallon kofa yayi yace "tana daki Mumy" Mumy tace "Aysha tace kuka kawai yake?" Ya d'an bude ido yace "Mumy ai kinsan yanda take behaving ni ban san me ke damunta ba" Mumy tace "Kai mata wayar" yace "Toh, xan kira idan na kai mata" daga haka ya katse wayar, da kyar ya mike gabansa na faduwa ya fita daga dakin ya shiga nasa, kwance ya sameta ta lullube gaba daya da bargo, ya karasa ya xauna kusa da ita ya yaye bargon yace "Humainah ga Mumy" kin bude ido tayi ya dagota ta buge masa hannu tana turasa, yace "Mumy ce xata maki magana" tana bude idon hawaye suka biyo baya, ta fada jikinsa tana kuka a hankali, rasa me xai ce mata yayi, ya dago kanta yana kallon fuskarta, murya can kasa yace "Humainah!" Kallonsa tayi bata ce komai ba hawaye na bin kuncinta, wayarsa ne ya soma ringing ya dauka yana kallon Screen din, can ya kalleta yace "Mumy xata yi magana da ke, plss ki bar kukan nan" bata ce komai ba ya d'aga ya kai mata kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace "Humainah!" A hankali tace "Na'am, ina yini Mumy" Mumy ta amsa tace "What's wrong with you kike kuka har yanxu?" Wasu hawayen ne suka xubo mata tace "Ba komai Mumy" Mumy tace "Ba komai kuma? Haka kawai kike kuka?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace "Toh xan xo gobe" a hankali tace "Toh!" Mumy ta katse wayar, ya dago kanta da sauri yace "What did she say?" Komawa tayi ta kwanta tace "Nothing" ya dawo kusa da ita yace "Karya kike" k'in ce masa komai tayi, ya dagota yace "Baxa ki gaya min ba" turasa tayi tace "Let me" jawota jikinsa yayi yace "Ae sai kin gaya min" ta hade rai tace "Stop this, bana so" kallon bakinta kawai yake, ta fara kokarin sauka ya rikota, cike da masifa ta buge masa hannu xata yi magana ya dago kanta sai jin bakinsa cikin nata tayi, buda ido tayi tana kokarin turasa ta kasa ya kwantar da ita ya lumshe ido, tsorata tayi ganin ya fara wuce limit, lokaci daya ya kawar mata da tsoron ta sakar masa jiki kamar ba ita ba, yanda ya kwantar da kai ka rantse kace ba captain Junaid ba, murda kofar dakin aka yi, ya saketa da sauri ya koma baya ita kuma ta shige cikin bargo, Jasmine ce ta shigo dakin da hijab sai towel dake jikinta, kamar xata yi kuka tana kallonsa tace "Ni banga bag din kayana ba" kallonta kawai yake da rinannun idonsa, shiru tayi ita ma tana kallonsa, juyawa tayi ta fita ta tsaya daga bakin kofa a hankali tace "Assalamu Alaikum!" Lumshe ido yayi ya bude yana shafa kansa bai ce komai ba, sallaman ta kuma yi kamar xata yi kuka, amsawa yayi fuskarsa daure, ta shigo ta tsaya daga bakin kofa, sai dai ta kasa cewa komai ganin yanda ya tamke fuska, kallonta yayi yace "From now on idan kika sake shiga waje ba sallama I will slap you" hawaye ne ya cika idonta ta gyada masa kai ta juya a hankali ta fita, juyawa yayi yana kallon Humainah da tayi lamo cikin bargo, ya shafa kansa ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa, wanka ya shiga yayi, ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa yayi shafa'i da wutr, yana xaune kan darduma har Karfe sha daya can ya mike ya fita daga dakin, tsaye yayi bakin kofa yana kallon dakin da Jasmine take don kofar a bude yake, ya karasa ya shiga dakin, kwance ya ganta daga gefe kusa da bakin kofar tana bacci har lokacin Hijab da towel ne jikinta, durkusawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace "Jasmine" ganin bata motsa ba ya mike ya fita daga dakin ya sauka parlor ya dauko mata jakar kayanta ya dawo sama, ajiye jakar yayi ya bude ya fiddo mata doguwar riga ja mara nauyi, kiranta ya kuma yi a hankali bata tashi ba, ya d'an buga kafadar ta ta mike xaune da sauri tana mitsika ido tace "Uncle!" Ganinsa yasa tayi saurin cewa "Captain!" Bai ce komai ba ya mika mata rigar hannunsa yace "Tashi ki sa kayan ki" karban kayan tayi yana kallonta ta cire hijab din jikinta ta mike, dauke idonsa yayi daga kallon nata a nan wajen ta saka kayan da ya bata, ta dawo kusa da shi tace "Na sa" mikewa yayi ba tare da ya kalleta ba still ya nufi gado ya ce "Xo ki kwanta" tace "Kai ma xaka yi bacci nan koh?" Yace "Eh" karasowa tayi ta hau gadon ta kwanta har da matsa masa, lulluba mata bargo yayi ya xauna gefen gadon ya kunna Tv yace "Sai na gama kallo xan kwanta" har sha biyu bai ga alamar xata yi bacci ba, ya kalleta yace "Sleep mana" tace "Sleep captain" murmushi yayi ya gyada mata kai yace "Ke ki fara yi sai nima in yi" lumshe idonta tayi ya tsura mata
Chapter 58 · 0% Book details