Sashe 33
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah tsoronta nake ji" Junaid yace "Ohk" yana fita ta dawo kusa da ita a hankali ta xauna tana kare mata kallo, doguwa ce yar siririya da ita, ta tsura ma kyakkyawan fuskarta ido da d'an karamin jan bakinta dake sheki, Khadija ta kama long fingers dinta a hankali tace "I like you sister, Allah ya baki lafiya" kallon hular kanta tayi ta dawo wajen ta d'an cire hular tana lekan kanta ta ga bakin gashinta sai sheki yake, fito da gashin ta shiga yi ta bude ido ganin tsayin gashin, ta lumshe ido tace "Waoww!" Haka tayi ta xama kusa da ita tana kallonta, komai na jikinta me kyau ne, mamaki ta dinga yi inda suka samota har suke son warkar da ita, to yan uwanta fa?? Mikewa tayi jin ana kiran la'asar taje tayi alwala tayi sallah, sannan ta d'an gyara gidan ta dawo ta xauna ta ci gaba da kallonta daga inda ta tsaya, bude kofa taji anyi ta juya da sauri, taga El-ameen ne, ya karaso parlon yace "Capt ya tafi ne" ta gyada masa kai, ya iso kusa da su yana kallonta yace "She's still sleeping koh?" Ta gyada masa kai, ajiye ledan hannunsa yayi ya tada ta ya tafi sama da ita, khadija ta hade rai ta bi sa da kallo, haka kawae taji haushin abinda yayi, ta ja tsaki ta dauke kanta hade da tabe baki ta mike ta koma kujera ta xauna, ba a dau lokaci ba ya sauko, kallonta ya tsaya yi ganin yanda ta hade rai yace "Ke in kin gaji ne tashi ki tafi gidan ku" mikewa tayi ta dau Jakarta ta fice fuu, yayi tsaki ya dau wayarsa da ke ring. Tana fita ta kira Junaid yana d'agawa yace "Ta tashi ne?" tace "Wani tashi? Bayan ya wani ce wai in tafi" Junaid yace "Wa?" Tace "Ya El-ameen mana, wai wani in tafi gida" shiru ya d'an yi kafin yace "Saboda me?" Tace "Oho masa, ya wani dauketa ya kai ta daki bayan bacci take" mikewa Junaid yayi daga zaunen da yake parlon Mumy yace "daki kuma, ke kina ina?" Khadija tace "Ehh mana, ni na riga na fito ma tafiyata xan yi" katse wayar yayi kawai ya ajiye, Mumy dake ta kallonsa tace "Wani dakin? Kuma da wa kake waya" Kallonta yayi da sauri don ya mance tana wajen yace "Ohh dama, dama na aiketa ne, shine... no wai ce min tayi yayarta ta kulle ta a daki, khadija ce" Mumy na masa wani irin kallo tace "Karya kake" ya xaro ido yace "Mumy karya kuma" ta girgixa kai tace "Ahmad am beginning to suspect you this days, behaviours dinka sun fara canxawa, i notice kana boye min wani abu, but be careful" daga haka ta shiga bedroom, Humainah dake xaune parlon ita ma tana gyada kai tace "ta tashi ne? uhnn ko waye ya tashi oho, daki kuma? Uhnn ko wani dakin yake nufi oho, ke kina ina? Uhn ko wacece haka oho, hmm we are beginning to suspect you this days Captain be careful" wani harara ya watsa mata ta mike tayi masa gwalo tace "In tayi tsami ma ji dai" da sauri ta shige dakin Mumy ita ma. Ya shafa kansa a hankali don yasan ko hauka yake baxae bari Mumy taji xancen mahaukaciyar nan ba, tabdi! mikewa yayi da sauri ya dau makullin motarsa ya fita, waje ya fita don bai shigo da motarsa compound ba ya hau motar ya nufi gidan El-ameen, cikin few mins ya isa, yana Parkin ya fito ya shiga gidan, xaune ya tarda El-ameen balcony yana waya, ya tsaya yana kallonsa har ya gama ya hade rai yace "Y did you send khadija away?" El-ameen yace "Haka tace maka, to let me get hold of her" Juyawa Junaid yayi jin an bude gate, wata mace da baxata wuce 27 ba ta shigo, ta karaso balcony ta gaida Junaid, ya gyada mata kai kawai, mikewa El-ameen yayi yace "Welcm, ki shiga daga ciki" ba musu ta shiga parlon, El-ameen yace "we are hiring her for 2 dayz kafin Mama ta dawo, sai ka biyata 10k, old nurse din clinic din mu ce" Junaid ya daga shoulder yace "Anyhow" juyawa yayi yace "sai gobe, na tafi" El-ameen yace "Wato xuwa Kayi ka ga what I was up to da nace khadija ta tafi koh?" Junaid yayi murmushi bai ce komai ba yayi gaba abunsa, El-ameen yayi kwafa ya shiga parlon. Karfe shidda da wani abu Junaid ya shigo gida, ya ga khadija tsaye nesa da b alconynsu, Hajiya da Umma na xaune sai Sadiya da Suhaima, Sadiya sai cewa take "Kawai ki bar min komai a hannuna Hajiya idan na lallasa ta xata fadi inda taje wllh" Umma tace " Ni tun da ta fara mu'amala da shegiyar 'yar da aka kawo gidan nan Humainah take kowa, dabi'un ta suka canxa, ke har kin kai matsayin da xa Kiyi karyan xuwa gidan kawa ki fita tun safe sai yanxu kike shigo mana gida don Kazan ki" junaid ya karasa wajen ya gaida su yace "Hajiya tare muka fita, ta rakani ne" Umma ta watsa masa wani kallo tace "Da yake ba Aysha bace ko Fatima dole ka kareta mu bar ta ta lalace" Juyawa khadija tayi fuu ta nufi part din Mumy, Hajiya ta shiga kwala mata kira tana cewa "Kika kuskura kika shiga wajen nan mai raba ni da ke sai Allah, kuma wllh kin ji na rantse sai kin fadi daga inda kike" *Haske writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 24..... Junaid ya juya shi ma ya bar wajen, Hajiya ta bi bayan khadija tana huci, a balcony ta tsaya ta tura kofar tana cewa "Kar ki bari in shigo parlon nan khadija, tun muna mu biyu ki fito ki wuce" tsayawa Junayd yayi yana kallon ikon Allah, Humainah dake xuge jakar kayanta da ta gama hadawa a parlor ta tabe baki ta mike, ta dauki remote din TV ta kure maganar gaba daya, Hajiya ta xaro ido tana kallonta, ji take kamar ta shaketa kawai ta huta, can dai tace "Ke wai ni sa'ar uwar ki ce kika raina ni haka a gidan nan, ina magana za ki kure min TV?" Humainah ta rike kugu tace "Ni ba dai uwata ba wllh" Sadiya ta karaso bakin kofar parlon tana cewa "Bata fito bane Hajiya" Hajiya ta fashe da kuka tace "Yanxu ni yarinyar nan take ma rashin kunya Sadiya, a haihuwar kaji ban yi jika da shegiyar ba" a fusace Sadiya ta shige parlon tayi kan Humainah, Junaid na ganin haka ya bi bayanta, ai tuni Humainah tayi dakin Mumy da gudu tana kwala mata kira, hakan kuma bai hana Sadiya bin ta ba tana kunduma mata xagi, wani tsawa Junaid yayi mata tun kan ta shiga dakin Mumy ya fixgota ya nuna mata kofa yace "Get out, ko a mafarki kika kuskura kika yi attempt din t'aba ta wllh sai na ba66allaki a gidan nan" kallonsa kawai take fuskar nan nata daure don tasan tana iya magana yanxu ta sha mari, Hajiya ta shigo parlon tana huci tace "Wllh Ahmad idan ka bari na saka ka gaba a gidan nan sai xaman duniyar nan gaba daya ta gagare ka, kayi hankali da ni ka bi ni a hankali, bani da kyau wllh, amma in dai ni ce mu je xuwa sai ka gwammace uwar ka bata haifo ka gidan nan ba, xaka san da ni kake" Mumy ta fito tana ma Hajiya wani kallo tace "Babu abinda kika isa ki masa wanda Allah bai masa ba, mu da Allah muka dogara, aniyar ki ta bi ki kuma" Hajiya tayi shewa tana murmushi tace "Toh mu xuba da ku," daga haka ta juya fuu ta fice, Sadiya ta bi bayanta. Junaid ya girgixa kai ya juya ya fice daga parlon, shi gaba daya xaman gidan ma ya ishe sa kawai. Mumy ta kwalo ma Humainah kira ta fito, strictly tace "ina raba ki da mutanen nan baki ji ko Humainah, ina ruwan ki da su wai da har xaki dinga shiga tsabgarsu, kinsan Allah baxa mu shirya ba idan magana za ki dinga dauko min, so kike su sa ki gaba kema koh? To maxa gama hada kayan ki yanxun nan Ahmad ya tafi da ke inda xai kai ki kafin Abba ya dawo su kuma hada ki da shi" Juyawa Humainah tayi ta koma daki kamar xata yi kuka, Khadija ta fito daga daki tace "Mumy kiyi hakuri," Mumy tace "Kinga idan kin yi laifi ki daina yo wa nan khadija, sai ki tsaya can ki basu hakuri" Khadija ta turo baki ta koma dakin su fatima. Junaid na shigowa bayan yayi wanka ya canxa kaya Mumy tace "Maxa kai ta gidan Aisha kan dare yayi Ahmad" ya kalli agogo don dama fita xai yi ya maida motar jiya, yace "Toh Mumy" Mumy ta kwalo ma Humainah kira tace "Dauko jakar ki da hijab" tana kumbure kumbure ta fito rike da 'yar jakar kayanta da Hijab, Junaid ya mike yace "Sai na dawo Mumy" Mumy tace "Allah ya kiyaye, amma motar waye ka dawo gidan nan jiya da?" Ya d'an shafa kai yace "A frnd, idan na ajiyeta xan mayar ne ma" Mumy tace "Ohk," ya fita Humainah na biye da shi a baya, Mumy tayi murmushi tace "Ba sallama Humainah" kamar xata yi kuka ta daga mata hannu ta fice, Mumy tayi dariya tace "Lallai Humainah" As usual Hajiya da Umma na balcony, duk suka bi su da hararan tsana, tsayawa yayi har Humainah ta karaso inda yake ya karbi jakar hannunta suka nufi parking lot, Umma ta kalli Hajiya tace "Ke wllh naga kamar sonta yake, dubi fa har da wani rike mata jaka, sai ya iya yiwuwa ma ya fito da ita a matsayin warce xai aura idan lokacin da Alhaji ya dibar masa yayi" Hajiya ta xaro ido tace "Ae ko da mun banu mun lalace, meye abun yi Bilki?" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "ba mu ga ta xama ba," Humainah ta kalli motar da Junaid ya shiga tace "Motar waye wannan?" Kallonta yayi ya bude ido yace "Naki" ta hararesa ta xaga ta shiga, yana warming motar