Sashe 69
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafsat ta shiga ta ganta xaune gaban mirror tayi tagumi ta karaso ta xauna tace "Aunty what's wrong with you?" Kallonta Hafsat tayi tace "Nothing, ur breakfast is downstairs" Jasmine ta bata fuska tace "No kalli idon ki, are you crying?" Girgixa mata kai Hafsat tayi tace "Ba komai" a sanyaye Jasmine ta mike ta fita daga dakin ta koma dakin El-ameen, yana bathroom ta nemi waje ta xauna har ya fito bayan kusan minti ashirin daure da tawul, mikewa tayi ta karasa kusa da shi a hankali tace "Uncle may be Aunty is sick, she's crying" hade rai yayi yace "you are not my muharrama, how dare you come into my room just like that without permission?" Ta buda ido tace "Ohh, I....." Yace "Leave now" juyawa tayi a sanyaye ta fita daga dakin, nan corridor ta sulale ta fara kuka, ya gama shirinsa ya fito, kallo daya ya mata ya shiga dakin Hafsat ta mike ta bi bayansa, kwance ya ganta kan gado kamar me bacci, Ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta, Jasmine ta karasa ta xauna gefenta tace "Anty na kira maki uncle xai duba ki, he's a doctor...." Bude ido Hafsat tayi ta mike xaune ganinsa, ba yabo ba fallasa yace "What's wrong with you?" Shiru Hafsat tayi, Jasmine ta matso kusa da ita tace "He said what's wrong with you" Hafsat tace "Nothing" Jasmine ta hade rai tace "And you were crying mana" El-ameen ya tabe baki ya cire bargon da ta rufe da shi tana ganin haka ta fara kokarin komawa baya ya riketa ya daura hannunsa a forehead dinta, saketa yayi ya juya ya fita, Jasmine ta bi bayansa da sauri suka shiga har dakinsa, gaban mirror ya nufa ita ma haka ta tsaya daga bayansa tace "Uncle me ye ke damunta?" Banxa yayi mata ta kuma tambayar ya juyo ya fixgota yace "Am not ur muharram ko kin manta ne!" Shiru tayi ta bata fuska, kawai gani tayi ya rungumeta ta xaro ido tace "Uncle!" Bakinsa ya kai kunnenta yace "And Captain isn't ur muharram also...." Jikinta ya dau rawa ya saketa ya fice daga dakin. Fitowa ita ma tayi ta shige wani daki ta fara kuka, har rana bata fito ba, karfe uku tayi wanka ta sa hijab dinta ta fita ta nufi gate, tafiya kawai take har ta iso main road, tsaye tayi tana kalle kallen ababen hawa dake wucewa, ko sanin yanda xata ce su tsaya bata yi ba, can dai tayi deciding ta jira motar captain, ta kusa minti sha biyar tsaye sai wasa da hijab take wani mota yayi parking gefenta ta bi motar da ido, wani ne ya fito ya kusa minti uki tsaye kafin ya karaso kusa da ita yana kallonta ya rungume hannu yace "Good afternoon!" Dauke kai tayi ta turo baki, ya karyar da kai yace "naga alamar kina jiran driver ne koh?" Kallonsa tayi tace "No motar captain nake jira in gani" ya dan wara manyan idonsa yace "Kike jira ki gani?" Tace "Eh" yace "Ohk yace maki yana xuwa ne?" Girgixa masa kai tayi, ya d'an yi shiru kafin yace "Toh ki kirasa" tace "Bana da waya" yace "Toh ga ta wa" tace "Bana da number" murmushi yayi yana kallonta yace "Ohh dat's good, to in yi dropping din ki?" Kallonsa tayi tace "Toh" sannan ta nufi gaban motar, bin ta yayi da kallo har ta bude ta shiga, ya xaga shi ma ya shiga, sai da ya hau kan titi sannan yace "Ina ne gidan ku" buda hannu tayi tace "Nima ban sani ba" kallonta yayi da sauri yace "Baki sani ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh amma kamar ta can captain ya biyo, sai yayi corner" waje ya samu yayi parking don kansa ya fara rikicewa yana kallonta yace "Ya sunan ki!" Langwabar da kai tayi ta wara ido tace "Jasmine, jewel baby!" Kallonta yake ko kiftawa bai yi, can yace "Daga ina kike yanxu?" Kamar xata yi kuka tace "Uncle ne yayi min ihu ya koreni, shine xan je gidan Captain" jinginar da kansa yayi jikin kujerar motar yace "Toh fah! Amma ba garin nan kike ba koh?" Tace "Ehh Mami na ta tafi UK in ji uncle a can muke sai muka xo nan yace min?" Xaro ido yayi yace "Toh yanxu ina xan kai ki?" Tace "Mu bi ta can kila xa mu ga gidan" tada motar yayi ya bi inda tace, tafiya kawai suke da sun yi nisa sai tace ba nan bane, duk ta daure masa kai nan ya fara tunanin anya bata da disorder kuwa, fashe masa da kuka tayi daga karshe wai ita sai ya kai ta gida, can dai ya fara tunanin anya ma ba aljana ya dauko ba, dafe kansa yayi yace "Look Jasmine ni ban san gidan ku ba wllh, ya sunan brother din naki?" Tace "Sunansa captain!" Yace "Real name dinsa fa nace?" Tace "Ehh" Bude motar yayi ya fita da nufin tambayar ko akwai wani captain a anguwar, ita ma ta fito da sauri ta fashe da wani kuka tace "ni dai ka kai ni gidanmu plss" da damuwa yace "Wait! idan na maida ki inda na dauko ki xa ki gane gidan?" Make kafada tayi tace "Ni baxan gane ba gidan captain dina xa ka kai ni" xaro ido yayi yana salati a xuciyarsa, tana share hawayen fuskarta tace "Ka ji?" Hannunta ta ji an kama ta juya da sauri lokaci daya ta warce hannun, wata mata ta gani tsaye tana kallonta baki bude, a d'an tsorace ta koma kusa da shi, matar ta saki salati tace 'yar nan! Ashe Allah xae kuma hada mu" Jasmine ta turo baki tana komawa baya, shi kam kallon tsohuwar yayi yace "Yauwa mama kin san ta?" Washe baki tayi tace "Wllh na santa, kwarai kuwa na santa" *Haske Writers association* [3/19, 9:34 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 60...../65 Kallon mama jummai kawai yake, can ya girgixa kai yace "Toh yanxu ya xan yi da ita?" Da sauri tace "Ka bani ita in tafi da ita nasan inda xan samo su" Jasmine ta saki wani kara da ya tsorata mama jummai tace "Nooo I don't know herrr" ta fad'a tareda k'ura mishi ido tana kallonshi, tada motar kawai yayi ya fara tafiya, suka yi tafiyar kusan minti sha biyar ya isa wani babban gida yayi parking gaban gate ya juya yana kallon mama jummai yace "Idan kin samo yan uwan nata ki kawo su nan, gidan iyayena ne nan din" shiru mama jummai tayi ya d'an yi murmushi yace "Ehh" tace "A'a kaga ni dai duniya bbu gaskiya yanxu, ina iyayen naka?" Wayarsa ya dauka ya yi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace "Farida ku fito ke da Ramla" daga haka ya katse wayar, ba a dau lkci ba wasu yan mata da baxa su wuce Jasmine ba suka fito, yace "Toh kin gani mama, kanne na ne wa ennan" daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude side din Jasmine ita ma ta fito tana kallon Mama Jummai k'asa k'asa, yana kallon kanninsa yace "Ku tafi da ita ciki" Farida dake ta kallonta tace toh, ta fara tafiya haka Ramla ta bi bayansu, mama jummai ta fito a sanyaye, ya fiddo dubu biyu ya mika mata yace "Kiyi kudin mota" godiya tayi ta fara tafiya tana waige waigen gidan, ya koma motar aka bude masa gate ya shiga yayi parking, da sallama ya tura kofar babban parlon gidan, durkushe ya ga jasmine jikin kujera kannin nasa na kusa da ita, xaune a kan kujera mahaifiyarsa ce sai stepmother dinsa dake parlon ita ma, Mahaifinsa ma na parlon xaune sanye da farin glass dinsa ga laptop gabansa kan centre table, karasowa yayi ya xauna daga gefen mum dinsa a kasa, mahaifiyar tasa Hajiya Mariya tace "Wacece wannan Abdul?" Sosa kai ya shiga yi a hankali yace "Hajiya bakuwa ce...." Wani kallo take masa tace "Bakuwa daga ina?" Rasa abinda xai ce mata yayi can yace "Mance gidansu tayi wai" wani kallo yan parlon suka shiga yi masa, Dad dinsa ma ya dago for the 1st tym yana kallon abinda ke faruwa, Hajiya ta daka masa tsawa tace "Waye abokin wasan ka a nan?" Yace "Hajiya ga ki ga ta ki tambayeta ni wllh bn santa ba ma, taimakon ta kawai nayi" Hajiya ta kalleta tace "Ke daga ina kike" Jasmine ta sauke idonta daga kallon da take ma Hajiyar a hankali tace "Gidan uncle?" Hajiya tace "Xa ki ina?" Ta dago manyan idonta tace "Captain!" Hajiya tace "ikon Allah, to daga wani garin kika xo?" Shiru tayi sai kuma tayi maza tace "UK" duk suka buda ido suna kallonta, stepmum dinsa Hajiya karima tace "Ina kenan a UK?" Buda musu hannu Jasmine tayi alamar bata sani ba, Hajiya ta kallesa ta juya xuwa harshen fullanci tace Maxa ya tafi da ita station right away, marairaice mata yayi yace "Ammi taimako...." Harara ta watsa masa tace "Xan saba maka wllh" Dad dake ta kallon Jasmine yace "Ke Ramla ku tafi da ita daki" mikewa suka yi gaba daya suka bar parlon, Abdul ya kalli Mum dinsa da ta hade rai sosai ya mike kansa a kasa ya bar parlon. Karfe bakwai da kusan rabi El-ameen ya shigo parlor junaid na bin bayansa, duk da ganinsu kasan ba karamin gajiya suka yi ba, ganin hanyar daki El-ameen ya nufa junaid ya fixgosa a fusace yace "Look am tired of this game ka gaya min inda yar mutane take Ahmad...." Juyawa El-ameen yayi yace "plss don't make me loose my temper..." Daga haka ya bar sa gun tsaye, dakin Hafsat ya shiga ya ganta xaune kan pray mat ya hade rai yace "Wai ma kina me ta fita gidan nan baki sani ba" kallonsa tayi tace "Ba tare ku ke da ita a daki ba, ta ina xan san ta fita ko bata fita ba" kallonta ya tsaya yi can ya fice daga dakin, bedroom dinsa ya shiga ya xauna gefen gado ya rike kansa. Jasmine ce xaune ita kadai dakin bayan isha, tun xuwanta gidan take xaune ita kadai a dakin sai dai su shigo su yi abinda ya kawo su