Sashe 14
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
a kan da warcan bakar yar taki a gidan nan, don uba daya ba wasa bane" ae sum sum Hajiya Fatee ta bar wajen, Mumy ce ta fito jin hayaniya ta karaso da sauri tana tambayar abinda ya faru, Hajja ta shiga mata bayani cikin fada, shiru Mumy tayi tana kallon Junaid, Umma ta fixgi hannun Suhaima suka bar wajen tana huci, Hajja tace "haka kawae, xata kawo mana agola a gida ta adaddabe mu, ita ma wancan mai kama da kutaren ma haka ta kawo nata agolar, duk an cika masa gida da agololi," juyawa tayi tana kallon Khadija tace "Toh wllh ki rike d'an uwanki, don shine dolen ki kuma kun fi kusanci da shi akan wancan bakar don uba daya ba wasa bane" tana kai wa nan ta nufi bangarenta kamar xata tashi sama, Humainah dake tsaye balcony tana kallon film din sae dariya take, Fitowa Khadija tayi daga palon ta bi bayan Hajja don tasan ko hauka take baxa ta nufi sashinsu yanxu ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta karasa cikin palon Junaid ya bi bayanta, a hankali ta soma magana tace "Ahmad ina raba ka da shiga tsabgan mutanen nan baka ji koh, ba sonka suke ba kai kanka ka sani, ina ruwanka da shiga tsakanin Khadija da 'yar uwarta?" Junaid yace "Marinta fa tayi Mumy" Mumy tace "koma dai meye ni dae ka kiyaye su bbu ruwanka da su, tsakanin ka da Khadija daban tsakanin Khadija da Suhaima daban" yace "Toh shknn Mumy kiyi hakuri," juyawa tayi ta fita daga palon, ya koma ya xauna yana kallon agogo don duk ya kagu ya fita xuwa gidan El-Ameen. Har bacci ya fara daukansa yaji ana buga kujerar da yake kwance kai, ya bude ido da sauri ya ga Humainah tsaye kansa, mikewa xaune yayi, ta rufe bakinta da hannu tana 'yar dariya tace "Dama haka kake bacci baki bude" shafa kansa yayi yyi saurin fixgota ya xaunar da ita kasa, kara tayi tana kiran Hajja, ya hade rai yace "me ya shigo da ke Palo na?" A rikice tace "wllh Abba ne yace in kira ka" yace "A bude kika ga baki na?" Da sauri tace "A'a wasa nake" daga hannu yayi kamar xae kai mata duka ta boye fuskarta tana kiran Hajja, ya saketa yace "Ashe fitsarar ta karya kike yi" shiru tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kofa, ta bi sa da harara, yana fita ta sa dariya, mikewa tayi tana kare ma palon kallo ko ina tsaf kamar na mace ga kamshi ya kama palon sosai, bedroom dinsa ta nufa, nan ma very neat ta rike kugu tana bin ko ina da kallo ganin how over tidy it is ga kamshi me ddi dake tashi, ta nufi gaban madubi tana kallon turarruka masu tsadan gaske dake jere gaban mirrorn, daukansu ta shiga yi da daddaya tana fesawa don jin irin kamshin su, kala biyu ta dauka ta fito daga dakin da sauri ta fita daga palon ta ja masa kofa, part din Hajja tayi da saurinta. Junaid na xaune kasan lallausan rug din palon Abbansa yana kallon Abban nasa da mamaki jin abinda yake cewa, juyawa yayi ya kalli Umma da ke xaune ta sha kunu palon ga Suhaima ma xaune kasa, Junaid ya lumshe ido don ko kadan bae son a laka masa sharrin abinda bae yi ba a hada sa da mahaifinsa, cikin fada Abba yace "Kana jina kayi shiru Ahmad?" Bude ido yayi a hankali yace "Kayi hakuri Abba hakan baxae kuma faruwa ba in'sha Allah" Abba yace "kasani daga yau matsayin Suhaima daya da na khadija wajen ka, kar in kuma jin wannan shirmen, ashe baka da hankali ban sani ba" a hankali Junaid yace "Kayi hakuri Abba" Abba yace "Xancen banxa kake yi, kuma ka bata hakuri yanxun nan" juyawa yayi yana kallon Suhaima da idonta ke kansa ko kifta wa bata yi yace "Kiyi hakuri" tayi kasa da kai tace "Ya wuce" Abba yace "Tashi ka ban waje" mikewa Junaid yayi xuciyarsa na kuna ya fice daga palon. Part dinsa ya nufa yana shiga Palo yasan an shiga bedroom dinsa, ya karasa bedroom din ya kalli gaban mirror ya ga an dauka turare, kayan jikinsa ya canxa xuwa blue jeans da farar T shirt ya feshe jikinsa da turare ya dauki car key da wayoyinsa ya fice daga dakin. Kulle part dinsa yayi da makulli sannan yayi bangaren Mumy, bedroom dinta ya karasa ganin bata Palo ya sameta tana gyara kayanta a closet yace "Mumy xan dan fita sae na dawo" Mumy ta kallesa sannan ta ajiye kayan hannunta ganin mood dinsa tace "Me ya faru son?" Shiru yayi da farko sae kuma yace "Wae shine xa su samu Abba su ce na doki Suhaima, meyasa idan basu yi karya ba basu ji ddi ba 'yan gidan nan?" Mumy tace "Ae tun ba yau ba na sha fada maka ka daina shiga hurumin da ba taka ba, to yanxu gashi sun hada ka da Abban ka ae" ya fuzar da iska yace "Na tafi Mumy sae na dawo" tace "Ina xaka?" Yace "Gidansu faisal xan je" Mumy tace "Toh shknn kar ka dde, and drive carefully" yace "Ohk Mum" har bakin mota ta rakosa, su Umma dake xaune da Hajiya suka bi su da kallo suna tabe baki, ko kallonsu Mumy bata yi ba har Junaid ya ja motarsa ya bar gidan, Mumy ta koma part dinta, Hajiya ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Wannan Yaro ya xame mana babban obstacle a gidan nan wllh, komae sae yanda yace ma ubansa, idan ba ina bakin ciki da numfashin da yake a duniya ba Shegiya nake" Umma tace "Uhm ke ko ni, da da yanda xanyi da shi da tuni ni dae nayi wllh, don ko uwarsa bata isheni kamar yanda ya ishe ni a gidan nan ba, na tsane shi wllh wllh, ko 'ya yan mu fa Hajja bata ji da kamar yanda take ji da shi wae don yana namiji mu kuma mata gare mu" Hajiya tace "Toh shine kike kokarin ganin yanda xa ki cusa masa Suhaima ya aura kuma" Umma tace "Toh ae ke ma da xae auri Muhibba so kike naga" Hajiya tace "Da kenan ba yanxu ba don nasan hakan ma baxae taba yiwuwa ba, bari mu shiga ciki ki ji shawarar da na yi a kan matakin da xamu dauka kan Ahmad a gidan nan" Umma tace "Toh me muke a nan, mu shiga kawae ki ban in sha" mikewa suka yi gaba daya suka yi palon Hajiya. Gidan El-Ameen junaid ya nufa, yana gama parkin a waje ya shiga ciki, wanki ya tarar mama nayi a compound din na kayansu, ya karasa inda take suka gaisa sannan yace "El-Ameen ya xo ne mama?" Tace "Eh ya xo daxu da safe" yace "Ohk, bacci take yi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a idonta biyu sae dae ya kulle dakin," cikin gidan ya nufa ya haura sama, sae dae ya kasa bude dakin, ya kusa minti biyar tsaye sae kuma ya murda key din a hankali, bayan kusan second talatin ya murda handle din kofar, tsaye ya ganta jikin window tayi baja baja da gashinta tana sanye da doguwar rigar kanti pink colour da blue nd black flowers jiki, kallonsa take tana bobboyewa jikin bango, yayi murmushi ya rungume hannayensa yana kallonta. *Haske writers association* *Captain_Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 11..... Sulalewa kasa tayi ta xauna ta takure waje daya tana rufe fuskarta da dogon gashinta, dakewa yayi ya karaso cikin dakin kamar bai son taka kasa yana kallonta ya isa gabanta sae dae banda faduwa bbu abinda gabansa yake, bata dago har lkcn ta kallesa ba sae d'ada takurewa waje daya take, cire tsoro yayi ya durkusa gabanta a hankali, dago kanta tayi tana kallonsa a tsorace, murmushi yayi murya can kasa yace "Hello!" Kuri ta kura masa da ido, shi ma hakan yayi ma manyan fararen idonta, can ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "Allah ya baki lafiya don son ma'aiki S a w." A hankali ya kai hannunsa kanta ta kuma shigewa jikin bango, murmushi yayi ya matsa gabanta ya tattare mata gashinta ya mayar baya yace "Ki daina kunce gashin ki idan an daure maki Kinji" yana magana ne yana kallon fuskarta, ita kuwa wani gun daban take kallo, ji yayi ana haurowa sama, ya juya yana kallon kofa sae ga El-Ameen, dauke kai yayi El-Ameen ya shigo yana murmushi yace "Uhnn! Ka daina tsoron nata kenan yanxu?" Mikewa Junaid yayi bae ce komai ba, El-Ameen yayi dariya yace "In gaya maka meyasa kaga ta kyale ka?" Junaid ya juya yana kallonsa, sai da ya dau kusan minti daya sannan yace "akwae alluran da na mata daxu shi yasa ta nutsu, but ina me tabbatar maka da xaran ya saketa xaka gane kuran ka idan ka tsaya gabanta" yana murmushi ya kare maganar, Junaid ya tabe baki ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka sa ba, El-Ameen ya bisa da kallo yana dariya sannan ya juyo yana kallonta, karasawa gabanta yayi ya durkusa ya dago kanta, hade rai yayi yace "Sae da kika kuma cire ribbon din koh?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya hade rai yace "I will knock yhu idan baki bar kallona haka ba" kamar taji me yace ta dauke idonta daga nashi, mikewa yayi ya dauko ribbon ya dawo gabanta ya durkusa ya kama gashinta waje daya ya daure da ribbon din sannan ya dagota suka mike a tare ya kama hannunta, kin binsa tayi tana tutturjewa yace "Keehh" daga haka ya ja ta suka fita daga dakin tana bin sal, Palo ya sauko da ita ya xaunar da ita kasan rug, ya dauko ledan da ya shigo da ya durkusa gabanta ya bude, fried Irish ne da kwae, sae tomatoe ketchup, ya dauki potatoe daya ya dibi kwae ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri tana komawa baya, ya tsaya kallonta, kai wa bakinsa yyi ya ci, Junaid dae sai kallonsu yake yana yi yana danna waya, kara daukar wani chip din El-Ameen yayi ya dangwali ketchup ya kai bakinta, tsura ma dankalin ido tayi sae