← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 104

Sashe 97

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallama da kabir din ba?" Junaid yace "mun yi waya da shi ya tafi ikj ba lallai xa mu hadu ba...." El-ameen yace "Ohk" daga haka ya mike ya karba jakar Junaid suka fita, junaid ya kulle masa apartment din ya ba neighbor dinsa key din, bike suka dauka xuwa airport road, bayan sun isa suka dau cab xuwa cikin airport din, El-ameen dai na ta lura da shi don ko ba a fadi masa ba yasan daurewa kawai yake, sai da suka hau jirgi Junaid ya dake yana kallonsa yace "Thought yau ne daurin auren?" El-ameen yace "Yeah! After juma'at prayer, xa ma ka iya xuwa kuwa" junaid yace "No!" Suna isa kt Junaid ya nufi gida shi ma El-ameen ya nufi nasa gidan. Part din Mumy junaid ya shiga ganin bbu kowa parlor sai tv dake kunne ya shiga dakin Mumy, xaune ya ganta a daki ya karaso ya durkusa ya gaisheta, bbu yabo bbu fallasa ta amsa tace "Ahmad ashe kai ka haifi kanka ban sani ba?" Kallonta yayi da mamaki jin abinda tace, tace "Leave immediately" kasa daina kallonta yayi lokaci daya yana tunanin me kuma yayi, da kyar yace "Mumy wani abun ya faru ne kuma?" Wani kallo ta watsa masa tace "Ka fita nace" mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin, bedroom din su Humainah ya shiga, kwance take tana ganinsa ta mike xaune, ya karasa gadon jiki ba kwari ta mike tsaye, xai yi magana ta dakatar da shi tace "Ya Ahmad ni dai ka sake ni gaba daya bana auren kuma, idan kuma ba haka ba xan xubar da cikin nn wllh" kallonta kawai yake da manyan idonsa, can ya tabe baki ya juya ya fita daga dakin, ta fashe da kuka sosai ta sulale nan kasa ta hade kanta da gwiwa, tafiya kawai junaid yake yana son gane ma'anar abinda Mumy ta fadi masa, Muryar Hajja ne ya dakatar da shi jin irin kiran da take masa ba kakkautawa ya juya yana kallonta da mamaki, karasowa tayi fuskar nan nata a murtuke tace "Wato ai gwara kwadayina a kan taka Ahmad, tsabar naka kwadayin ya shahara 'yar gaba daya kake son aurewa kayi ma jikata kishiya, kishiyar ma jinin sarauta, dama ga Ka da taka sarautan da ka lak'a6a ma kanka tun ba yau ba, ita kuma ta xo da ta gidansu ku taru ku sa ma jikata hawan jini ta mutu in shiga uku, to ubanka yayi kadan bare kai, ban yarda da auren nan ba kuma baxa ayi ba, su rike kujerun jirginsu can baxa a je ba...." *Haske writers association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 87___88 Durkushe ya ganta a dakin tana kuka, tana ganinsa ta hadiye kukan ta hade rai sosai, hade rai shi ma yayi yace "Did you just say something?" Mikewa tayi tana masa wani kallo tace "We the royal blood don't say things twice...." Dariya sosai ta basa, sai dai ya dake bai yi ba ya Karasa gabanta yana kallonta, ko dar bata nuna ba duk da a tsorace take ganin yanda fuskarsa ke a daure, wani murmushi yyi yace "Mind you gidan Capt Ahmad ne nn ba so called royal home din ku ba" tabe baki tayi ta juya masa baya tace "I don't care where I am, I Still remain who I am..." kallonta ya shiga yi daga sama har kasa can ya gyada kai yana murmushi ya juya ya fita. Da rana El-ameen ya xo gidan, suna xaune parlor da Junaid ganin bai ga Zahrah ba sai Humainah dake kitchen, yace "Captain rowar ganin amaryar ake min" Junaid ya mike yace "Noo Not at all..." Daga haka ya haura sama ya tura kofar bedroom dinta, xaune ya sameta tana ganinsa tayi saurin goge hawayen fuskarta ta dauke kai, daga nn bakin kofa yace "ki fito ku gaisa da El-ameen.... Miss Royal being" wani kallo ta masa sai kuma ta mike ta dau hijab ta saka tayi ficewarta daga dakin ta bar sa tsaye, da murmushi fuskarta suka gaisa da El-ameen sai dai bata yrda sun hada ido ba, El-ameen na ganinta yasan kuka tayi, kallon Junaid da ya tsiri danna waya yyi sai dai bai ce komai ba, ita kuma ta mike, da har xata koma sama sai kuma ta nufi kitchen, Humainah dake hada stew ta kalleta ta dauke kai ta dalilin faduwa da gabanta yayi, Zahrah ta dake tace "Sannu da aiki" Humainah tace "Yauwa, thanks" kallon kayan lambun dake ajiye kitchen din Zahrah tayi ta karasa ta dauka ta nufi washing basin ta shiga wanke su, ita dai Humainah bata ce komai ba sai satan kallonta take, har ta gama wanke su ta dauki chopping board da wuka ta shiga yankasu, bayan kusan minti goma Zahrah tace "Ki ara min wayar ki" Humainah tace "Yana daki" har suka gama aikin bbu wanda ya sake cewa komai, ko da Zahrah ta dawo parlor bata ga El-ameen ba alamar ya wuce, sama ta nufa Junaid ya bi ta da kallo don yyi mamakin kitchen da ta shiga, can Humainah ma ta fito ta nufi sama ita ma ya bi ta da ido can ya mike ya bi bayanta, Zahrah na haura wa sama dakin da tasan na Humainah ne ta bude ta shiga, can kan gado ta ga wayar ta dauka ta xauna gefen gado, Humainah ta shigo dakin, sosai tayi mamakin ganinta xaune dakin, bata ce komai ba ta tafi gaban mirror, Bude kofar aka yi Junaid ma ya shigo, still yyi bakin kofa yana kallon Zahrah, kallo daya tayi masa ta dauke kai, ta mika ma Humainah wayar tace "bude min pattern" Humainah ta karba Junaid ya fixge wayar hannunta yana kallon Zahrah yace "Wa xa ki kira?" Ba tare da ta damu ba tace "Abbana" juyawa yayi ya fice da wayar, tabe baki tayi ta kalli Humainah ta mike ta nufi kofa, Humainah ta bi ta da kallo har ta fita ta juyo tace "Idan kin xuba abinci ki kira ni, we don't eat alone at home" daga haka ta fita, mamakinta sosai Humainah ta dinga yi, tana xuba abincin kuwa ta dawo sama ta bude kofar dakinta ta kirata, mikewa Zahrah tayi ta fito suka sauka kasa a tare, nan kan carpet Humainah ta ajiye masu abincin, Zahrah ta xauna ta tankwashe kafa ta dau spoon ta fara cin abincin, xaunawa Humainah tayi ita ma ta dau cokalin ba tare da ta kalleta ba ta shiga cin abincin, Zahrah ta d'an kalleta tace "How month pregnant are you?" Kallon mamaki Humainah tayi mata da kmr baxata tanka ta ba sai kuma tace "five" Zahrah ta langwabar da Kai tace "Ohk.... But me yasa mijin ki yake behaving yanda yake yi?" Humainah bata kalleta ba bare ta sa ran amsa, aka bude kofar parlorn Junaid ya shigo don dama yana waje, kallon mamaki yake masu can ya karaso parlon ya xauna yana kallon Humainah yace "Did you cook with me" kan tace komai Zahrah ta amshe tace "Of course No, not with her condition, just go get something outside to take!" Kallon Zahrah kawai yake can ya mike ya nufi stairs sai a snn yayi murmushi ya haura sama. Da daddare Zahrah na fitowa daga wanka ta xauna gaban mirror don yi shafe shafenta aka bude kofar dakin, duk da ynda gabanta ya fadi hakan bai sa ta juyo ba sai shafa lotion dinta take, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta gama shafanta ta mike ta nufi kan gado don daukar sleeping wear dinta, bin ta yyi da ido har ta dau kayan, ganin cire towel din xata yi yasa shi juyawa ya fice daga dakin ya rufo, murmushi tayi a xuciyarta tace you should have stay, tana gama shirya wa ta fito ta shiga dakin Humainah, Humainah dake kwance don ta gaji bayan dinner da ta girka ta bi ta da kallo, kwata kwata ta ki sakewa da ita, Zahrah ta xauna kan gadon ta dau remote tace "I hate staying alone... We don't do that at home" powering din Tv tayi ita dai Humainah bata ce mata komai ba. Daga karshe rufe ido ma tayi kmr ta fara bacci, xaman kusan minti talatin Zahrah tayi can tayi kwanciyarta kan gadon, bude ido Humainah tayi da sauri tana kallonta, ta gyada kai tace "Yeah, I am spending the nyt here" Humainah bata ce komai ba ta rufe idonta kuma, Zahrah ta gyara kwanciyarta ta ja duvet ta ci gaba da kallonta, bude kofar dakin aka yi Junaid ya shigo, ya buda ido yana kallon Zahrah, ko kallonsa bata yi ba idonta na kan tv, Humainah dai tayi kmr bacci take, juyawa yyi kawai ya fita daga dakin. Washegari da asuba Humainah ce ta fara tashi ta tada ta, sllh tayi ta fita ta bar ta dakin ta tafi kitchen, tana fita Junaid ya shigo, ya hade rai yana kallon Zahrah da ke kan darduma yace "Me ya shigo dake dakin matata, don ki koya mata girman Kai da unnecessary Royalism din ki koh?" Bata ko kallesa ba bare ya sa ran samun amsa, sosai hakan ya kona masa rai ya daka mata tsawa yace "Ba magana nake maki ba kika kyaleni" nn ma dai ko kallon gefen da yake bata yi ba, juyawa yyi ya fice daga dakin xuciyarsa na tafasa, sai a snn ta kalli bakin kofar ta gefen ido ta mike, ita ma ta fita ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta shirya cikin wani lace mara nauyi da ya amsheta sosai, gyara dogon gashinta tayi ta daure a baya ta bar dankwalin a kafada ta sauka, ba wani aiki ta taya Humainah ba sai tambayoyi da ta isheta da shi kmr yar jarida, Humainah ta jera komai kan dining Zahrah ta xauna tana kkrin daukan cup tace "Yanxu sai ki je kiyi wanka kiyi kwalliya wa mijin ki..." Humainah bata ko kalleta ba ta wuce sama, tana tafiya sai ga junaid ya sauko cikin shirin Uniform, har ya karaso dining din idonsa na kanta, shayin ta kawai take sha, ya ja kujera ya xauna ya hade rai yace "A royal Home din ku ba'a koya maki gaisuwa ba ne koh" bata dago kai ba bare ta tanka sa sosai haka
Chapter 97 · 0% Book details