Sashe 84
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
farin cikin ganinsu, ta sa aka cika su da kayan ciye ciye da sha, Shi dai junaid idonsa na kan makeken plasman parlon dake cike da kayan alatu, ganin yaki taba komai tace "Kai ya sunanka, ko kai ne takwaran mai martaba?" Girgixa kai yayi yace "A'a, Ahmad" tace "Babana ne ma ashe, to baka ci komai ba.... Ba a mana haka fa" da ganin murmushin da yayi kai kan ka kasan kirkira yayi, ya dau slice din kankana ya Kai baki yana tauna da kyar, ta gefen ido Zahrah ke kallonsa can ta tabe baki hade da murguda bakin, El-ameen kuma hararansa kawai yake ta gefen ido, ita ko Kilishi sai kallonsa take haka nan taji ya burgeta, jikinsa ne ya basa kowa kallonsa yake ya ki daga kai ya kuma daukar apple ya kai baki ya gutsura a hankali, Zahrah tace "Mumy bari in kai su gun Umma" Kilishi tace "Toh maxa ku je Zahrah" mikewa tayi tana kallon El-ameen tace "Mu je" mikewa yayi shi ma yayi mata sallama tace "A'a mai gida ai xaku dawo" kallon Junaid tayi tace "Toh tashi ku je babana" d'an murmushi yayi ya mike yace "Sai mun dawo" daga haka suka fita gaba daya daga parlon, a tare suke tafiya da El-ameen suna hira jefi jefi, El-ameen yace "Yayanki ne Abdul din nan koh?" Ta gyada kai tace "Yea, stepbrother nah" ya wara ido yace "Waow, mum dinsa ce kenan wannan!" Ta gyada kai tace "Ehh shi da Ummi" yace "Ayya, amma kina da kanni ko yayyi the same mum kuwa" girgixa kai tayi tace "I am the only one gun Ummata" kallonta yake da mamaki, yaji tausayin mahaifiyarta sosai, ko ya tayi da Allah ya rabata da only child dinta, junaid dai distance me d'an tsayi ya bari tsakaninsu yana biye da su hakan kuma bai hanasa jin hiran tasu ba, daya daga masu girke girken fadan ne ta washe baki ganin Zahrah tace "Gimbiya ban ganki kitchen yau ba" d'an murmushi tayi ta tsaya har ma'aikaciyar ta karaso kusa da ita, El-ameen ya ci gaba da tafiya, Zahrah na kallonta tace "Ina ciwon kai ne shi yasa... Ya aiki?" Matar tace "Alhmdllh, b'aki kika yi?" Kada mata kai tayi dai dai lokacin da Junaid ya karaso ya wuce su, ta bi sa da wani kallo kafin ta tabe baki tace "Da rana xan shigo kitchen Karima" daga haka ta nufi El-ameen dake tsaye wani stairs yana jiranta, ita kuma matar ta bi ta da kirari, ta gefen ido junaid dake tsaye gefen El-ameen ke satan kallonta har ya ga ta kusa isowa, El-ameen na ganinta ya ci gaba da tafiya, shi kuma yana ganin xata wuce sa ya sa mata kafa, ko lura bata yi ba sai ji tayi ta tafi luu xata fadi, tayi k'ara a tsorace tana neman regaining balance, bai san lokacin da yayi saurin tarota ba ta fado jikinsa, still tayi da farko sai kuma ta dago kai da sauri suka yi ido hudu, kasa motsi tayi ta kuma kasa dauke idonta cikin nasa, shi ma kallonta kawai yake gabansa na faduwa, bakinsa ta ga yana motsi a hankali ta sauke idonta kai underneath his breathe taji yace "Jas...jasminee!" Gaba daya ta shagala da kallonsa, shi ya fara dawowa hankalinsa ya saketa da sauri, sai a sannan ta koma baya duk ta daburce, a tare suka juya da sauri kallon El-ameen suka ga gun wayam babu shi. *Haske Writers association* Afuwan pls. [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By khaleesat Haiydar_ Da sallama ta tura kofar parlon ta shigo rike da wani babban tray mai dauke da abinci bayanta maids biyu wata dauke da bowl din fruit, wata kuma food warmers har biyu, kallonta kawai suke har ta karaso makeken parlon ba tare da ta dago ba ta ajiye tray din hannunta ta juya xata fita, a hankali El-ameen yace "Fatima!" Tsayawa tayi amma bata juyo ba, Junaid dai sai kallonta yake, jin ba ace komai ba tayi ficewarta daga parlon, saukowa El-ameen yayi ya dau fruit ya fara ci yana kallon junaid, tun xuwan su Bauchi ya rasa dalilin sanyin da yayi lokaci guda, har ya gama cin abinda xai ci junaid bai ko kalli abincin ba, El-ameen ya mike ya shiga bedroom ya bar sa parlon, rike kai Junaid yayi don shi kadai yasan abinda ke damunsa. Bayan isha ya fito makeken haraban masarautan sanye da kananun kaya ko ina farin wuta ne wanda hakan ya maida gun kamar safiya, tafiya kawai yake hannunsa cikin aljihu iska mai dadi na kadawa har ya karaso garden din da yasan xai ganta, ai kam xaune ya ganta ita kadai kan lallausan rug tana sanye da alkyabba kalan gold sai kyalli yake ta xauna kan kafafuwanta, ba wani wuta ne me haske gun shakatawar ba, gabanta bowl ne me dauke da apple fruit, ya rasa me ta tsura ma ido a gun, har ya karaso kusa da ita bata sani ba sai da sanyayyen kamshinsa ya bugi hancinta, duk da haka bata juyo ba idonta na kan grasses din wajen, ya xauna d'an nesa da ita cikin sanyin murya yace "Jasmine" bata kallesa ba bare tace komai, sake kiranta yayi nan ma dai bata amsa ba, dawowa kusa da ita yayi ya kuma kiranta a karo na uku, juyawa tayi tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "Sunana ba Jasmine ba" helplessly yake kallonta a hankali yace "Ohk fatima" dauke kai tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba lokaci lokaci ya kan juya ya kalleta, mikewa tayi daga karshe ta dau apple daya tace "Am going in" daga haka ta yi gaba ta bar sa wajen, ya bi ta da ido, lumshe ido yayi ya hade kansa da gwiwa, a hanya ta hadu da El-ameen ya mata murmushi yace "Princess!" D'an murmushin ita ma tayi ta wuce bata ce komai ba. Bangaren Ummanta ta nufa ta sameta xaune da baki da dama a babban parlonta, sallama tayi masu ta yi hanyar dakinta duk aka bi ta da kallo, mikewa Umma ta yi tayi excusing kanta ta bi bayanta, tana kokarin cire alkyabbarta ta shigo dakin, ta juya tana kallon uwar tata, Umma ta kamota ta xaunar gefen royal bed din dake dakin tace "Zahra!" Dago manyan idonta tayi tana kallonta tace "Na'am ummana" Umma tace "Why didn't you greet at the parlor" a hankali tace "Na fa yi sallama ummana" Umma tace "No da kin tsaya kin gaida su, they are ol here because of you daughter" sunkuyar da kanta tayi tace "Am sorry Umma" Umma ta rungumeta sosai jikinta lokaci daya hawaye ya taru idonta tace "It's OK sweetheart, kin kai ma su Ahmad din abincin kuwa" gyada kai tayi tace "Na kai" Umma tace "Good je ki gun Abba ki masa sai da safe, ko kin je?" tace "Naga yana da visitors ummana" Umma tace "Suna masauki yanxu, tashi ki je" tace "Toh ummana" mikewa tayi ta mayar da alkyabbar da ta cire suka fita dakin tare da umma, sai da ta fara karasawa cikin babban parlon ta durkusa ta gaida matan dake xaune, duk suka amsa suna kallonta da sha'awa, sannan ta mike ta fita, babban parlon Abbanta ta tafi sanin ya bar fada yanxu, ta gansa xaune kasa kan lallausan carpet din dake shimfide fruits gabansa daga gefensa Ya Abdul ne, sai yayyinta maza su hudu gaba, duk suka dinga kallonta har ta karaso gun Abba dake ta kallonta shi ma murmushi shimfide fuskarsa, mikewa xaune yayi yace "My princess" tayi murmushi tace "Abbana!" Ganin yanda yayyinta ke kallonta ta hararesu tace "Ni bana son kallon" dariya suka yi gaba daya har da mai martaba da ba kasafai yake dariya ba sai dai murmushi, da ganinsa kasan farin ciki ne karara tare da shi, ya Abdul kadai ne kansa a kasa sai dai lokaci lokaci ya kan dago ya kalleta, sun yi hira sosai da yayyin nata daga bisanni ta masu sai da safe har da Abba ta koma bangaren Umma. Washegari da ya kama Friday ana sakkowa juma'a, parlon mai martaba ya cika dam da 'yan uwa da abokan arxiki da suka taho nuna masa farin cikinsu na bayyanar tilon 'yar sa, haka kuma ranan da su Junaid xa su koma kenan kasancewar kwanan su uku a masarautan, Mai martaba sai kallon junaid da ko dago Kai bai son yi yake, can yayi gyaran murya yace "Ahmad?" Kallonsa junaid yayi sannan ya amsa, Mai martaba yace "Ka fadi duk abinda kake so nan duniya Ahmad in dai bai saba ma Shari'a ba kuma bai fi karfina ma na maka alkawarin yi maka shi koma menene" a baxata cewar sarkin ya xo ma junaid, ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, haka kawai gaban El-ameen dake gefensa ya dinga faduwa, junaid ya dago da kyar yana kallonsa cikin sanyayyen muryarsa yace "Bana bukatan komai ran ka shi dade, I helped her for Allah's own sake" kallonsa kawai sarkin ke yi daga bisanni ya juya yana kallon El-ameen dake kallon junaid yace "Kai fa Aminu?" Ido junaid ya xuba masa ya ji abinda xai ce, El-ameen da har lokacin gabansa bai bar faduwa ba cikin tsarkewar murya yace "Ina son ka min alfarmar bani aurenta ran ka shi dade, na maka alkawarin xan rike maka ita da amana...." wani mugun bugu xuciyar junaid yayi lokaci daya yaji kamar xuciyar ta bar aiki, mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido yayi murmushi yace "Na baka! Bbu ko sisin ka kuma" Kallon mamaki duk occupant din fadan ke ma mai martaba don baya magana biyu. El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace "You are blessed in'sha Allah son" kama hannunsa El-ameen yayi ya lumshe idonsa da ya kada ya kai lips dinsa, junaid ya lumshe idonsa da ya kada shi ma lokaci daya yana jin xuciyarsa kamar ba tasa ba. *Haske writers association* _Toh ga Captain Ahmad Junaid yayi gaba har ya kusa end_ Tnx for everything. My novel inteesar if am not mistaken yana da pages kusan dari biyu, my novel ikram had a hundred nd 15 pages or