Sashe 43
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai san da wani ido xai kalli Humainah ba, da kyar ya tura kofar daga karshe ya shiga, bbu kowa parlon sai kamshi me dadi dake tashi, ya karasa ciki jiki ba kwari ya xauna, Mumy ce ta fito daga daki tana kallonsa tace "Sai yanxu ka tashi?" Kasa kallonta yayi ga wani faduwa da gabansa yake don gani yake kamar Humainah ta gaya mata, ya dukar da kai ya gaisheta, tace "Meye haka kake kamar munafuki" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace "A'a kaina ke min ciwo Mumy" tace "Toh ga breakfast dinka can a dinning sai ka sha magani idan ka gama" mikewa yayi ya tafi dinning din ta bi sa da kallo, tabe baki tayi ta koma daki, tea kawai ya iya sha sai dube duben inda xai ga Humainah yake, mikewa yayi daga karshe ya tafi dakinsu, kwance ya sameta ita kadai fatima kuma ta tafi boko, mikewa xaune tayi ganinsa ya rufe kofar dakin tana ganin haka ta fashe da kuka tace "Ni wllh ka fita kar in kira maka Mumy" tsayawa yayi yana kallonta, tana share fuskarta tace "Ni dai ka fita" ganin ya nufota tsoro ya kamata ta fasa ihu tana kiran Mumy, still yayi yana kallonta, Mumy ta bude kofar dakin tana kallon ciki da mamaki tace "Meye haka?" Ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga kan gadon, Mumy ta kallesa tace "Me ya shigo da kai nan?" Rasa abun cewa yayi ya fara kame kame, can yace "Ni ban san..." Wani tsawa Mumy tayi masa tace "Get out!" Juyawa yayi ya fice daga dakin, Mumy ta kalleta tace "Ihun me kike ma mutane ke kuma" share fuskarta tayi a hankali tace "Ba komai" Mumy ta kusa second ashirin tana kallonta sannan ta juya ta fita daga dakin. Junaid kam part dinsa ya koma ya dau makullin motarsa ya fito ya tafi parking space ya dau motarsa ya fice daga gidan, hotel din jiya ya nufa yana gama parking ya fito ya hango El-ameen ya fito, kallo daya El-ameen yayi masa ya nufi gun motarsa dake ajiye har ya bude xai shiga Junaid ya bi sa da sauri yace "Hey..." Wani kallo El-ameen ya watsa masa yace "A haka xaka auri yarinyar ka kula da ita?" Junaid yayi tsaki ya xaga ya bude seat mai xaman banxa ya xauna, girgixa kai El-ameen yayi ya shiga motar shi ma, junaid yace "Kasan me frnd ina cikin damuwa wllh" El-ameen ya kallesa yace "Me ya faru kuma?" Dafe kansa yayi na kusan second goma sannan ya dago ya shiga gaya masa abinda ya faru bai boye masa komai ba, murmushi kawae El-ameen yake yana kallonsa can kuma ya fashe da dariya har da kyakyatawa, junaid ya tsaya kallonsa da mamaki lokaci daya ransa ya baci, bude motar yayi xai fita El-ameen ya tsagaita dariyarsa ya rikosa yace "Haba it's very funny mana, daga shan lipton? Seductive aka xuba maka cikin ruwan lipton din, its a plan, ba dai kace kayi trusting wannan khadijar ba kana tare da wahala," Xaro ido Junaid yayi yace "Seductive kuma?" El-ameen ya kuma fashewa da dariya yace "Of course, ita kuma warce aka turo maka taji maxa ta tsorata... Ohhh my God! Kai ban taba ganin makirci a xahiri irin na yan gidan nan naku ba" Junaid kallonsa kawai yake don kansa ya gama daurewa, El-ameen ya daga kafada yace "Allah ya taimakeka ka nuna mata kai din ba na wasa bane, da kawai sharri xa a maka ace kayi raping dinta you know daga nan ka kuma shiga wani case kila ma daga karshe Abba yace sai ka aureta, tunanin da Humainahn ma ta yi kenan kuma gwara da Allah ya kawo ta a lokacin don da komai xai iya faruwa" junaid ya rike kansa yace "Innalillahi......" El-ameen ya tabe baki yace "Allah ya kyauta! Ni dai am going to clinic Abba ya Kirani yanxu" junaid ya dago kai ya bude motar xai fita jiki a sanyaye, El-ameen ya d'an bude ido yace "But wait! ina xa ka yanxu? Uhn.... kar kuma pills din bai gama sakin ka ba kaje ka afka ma....." Kasa Karasawa El-ameen yayi ya dinga dariya, junaid ya hade rai yace "Wai mahaukaciyar?" Shi dai El-ameen bai ce komai ba sai dariya yake, Junaid ya dawo ya xauna yace "Look ko da ace na aureta yanxu me kuma xan ma mahaukaciya, infact ko ta samu lafiya sauwake mata xanyi ta tafi ta nemi yan uwanta frnd" El-ameen yayi shiru idonsa a kansa yace "Promise dat!" Shiru Junaid yayi shima yana kallonsa can yace "Promise what?" El-ameen yace "That tana samun lafiya xaka sauwake mata kuma baxa ka taba 'yar mutane ba" junaid bai ce komai ba can ya tabe baki yace "Do i need to, ba dai ni nayi niyyar yin hakan ba, ohk I promise" A hankali El-ameen yace "Kuma alkawari dai kaya ne" junaid ya masa wani kallo yace "Na fi ka sanin wannan" El-ameen yace "Good, yau Thursday sai ka fara shirye shiryen kai ta gidan ku on Sunday, I promise xan yi iya kan kokarina in ga everything goes smoothly" Junaid yace "But ni ban san wanda xai mata shiri me kyau ba irin na xamani" El-ameen yace "Ba sai kayi hiring a xo har hotel a mata ba" junaid yace "Ohk" bude motar junaid yayi ya fita ya nufi cikin hotel din El-ameen ya bi sa da kallo. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 32.... Yau ya kasance Saturday Junaid na xaune tare da El-ameen sai Jasmine da ake ma gyaran gashi cikin hotel room din, nurse din da ke kula da ita ma na xaune dakin, kyar El-ameen ya kafeta da ido yana kallon yanda kwararriyar hairdresser din ke mata gyaran dogon gashinta, da ta yi motsi xai xaro mata ido hakan yasa ta nutsu sosai duk da taki tsaida kan gu daya sai bin ta matar take, da ganinta kasan bata so, tsoron El-ameen dake gabanta yasa bata nuna hakan ba, shi kam Junaid wayarsa kawai yake dannawa, har bayan kusan minti talatin matar ta gama mata gyaran gashin, nurse din sai murmushi take tana kallon yanda gashin ke sheki ga tsayi, ita kanta hairdresser din sai kallon jasmine take da sha'awa bata taba kawowa mahaukaciya bace an dai ce mata bata da lafiya, El-ameen ya warce wayar hannun Junaid ganin bai ma san an gama ba, Junaid ya kallesa da sauri yace "What?" El-ameen yace "Your I don't care attitude xai kai ka ga halaka fa" Junaid ya hade rai yace "Shi gyaran gashin xan tsaya kallo kamar yanda ka ke kallo ko me?" Tsaki yayi ya mike yana kallon hairdresser din ya fiddo dubu biyar aljihunsa ya mika mata yace "Thanks madam" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Baxa a mata kunshi ba?" Ya juya ya kalli El-ameen, El-ameen ya kauda kansa, d'aga kafada yayi yace "A'a no need" matar tayi masu sallama ta fita daga dakin da jakar kayan aikinta. Sai a sannan Junaid ya kalli kan jasmine dake xaune har lokacin bata tashi ba sbda El-ameen, kauda kai yayi ya koma ya xauna yana kallon El-ameen yace "Look frnd ni ban san da warce xan hada ta mu tafi ba fa gobe... Am confuse" El-ameen yace "Kai baka san da warce xaka hada ta ba sai ni?" Tsaki Junaid yayi yace "Ni matsalata da kai kenan, cikin nurses din clinic din ku babu sa'arta??" El-ameen yace "Babu!" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen yace "Ba na ga kwanaki ka tsaya kula wata yarinya a mall ba har da karban numberta, just call her ka nemi favour wajenta, naga wayayya ce" Junaid yayi shiru yana kallonsa lokaci daya yana son tuno sunanta, can yace "Koh?" El-ameen ya d'aga kafada, Junaid yace "But ni ban taba kiranta ba fa, sai in ce mata me?" El-ameen yace "Ka fini sanin me xaka ce" Junaid ya dau wayarsa yana son tuna sunan da ya sa mata, can sunan ya fado masa yace "Yes Hafsat I think" numberta ya duba yayi dailing, bugu uku ta d'aga ya kalli El-ameen sannan ya mata sallama, amsawa tayi daga daya bangaren, yace "Hafsat?" Tace "yea" ya d'an shafa kansa yace "Ahmad Junaid, wanda kika ara ma motar ki kwanaki" tace "Ohk kwana biyu?" Yace "Alhmdllh, kina gida ne?" Tace "No ina school," yace "Which?" Tace "Al-qalam..." Yace "Alryt xan xo in same ki later, I will cal you idan na xo" tace "Ohk.." Sallama yayi mata ya katse wayar, El-ameen ya tabe baki ya mike ya karasa kusa da jasmine ya dagota sanin saboda shi ne taki tashi, ae da sauri ta mike ya dawo da ita kusa da su, ya dauki ragowar Irish dinta ya ajiye mata gabanta. Da yamma El-ameen na office Junaid ya xo ya samesa, ya ja kujera yace "Na je na sameta, i've explain everything to her and tace babu damuwa, gobe around Eleven xa mu tafi saboda sai ta fara xuwa makaranta" El-ameen ya tabe baki yace "Ohk" Junaid yace "I prefer ta sa hijab then veil" El-ameen yace "Ohk, sai ka je kasuwa ka siyo mata sabo har kasa milk colour tunda kalan gold ne kayan" Junaid yace "Ka raka ni mana..." El-ameen yace "as you can see am busy, idan tsoron mutanen kasuwan kake sai ka ba nurse din dake wajenta kudi taje ta siyo kai sai ka tsaya da ita kafin nurse din ta dawo" Junaid ya mike yace "Ohk" sannan ya juya ya fita, bin sa da kallo El-ameen yayi yana girgixa kai, can yayi murmushi ya ci gaba da abinda yake. Washegari lahadi junaid ya rasa me ke masa dadi, bai san yanda Mumy xata dauki jasmine a matsayin warce yake shirin aure ba idan aka gano bata da hankali, Karfe takwas da wani abu ya shigo parlon Mumy, Humainah ce ke ta goge goge a parlon, tana ganinsa tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, tun daga incident din ranan take avoiding dinsa, dakin Mumy ya tafi ya sameta tana gyaran dakin, ya gaidata ta amsa tare da cewa "Jiya Karfe nawa ka dawo gidan nan?" Ya shafa kansa yace "Tara saura, naga kamar kin yi bacci ne shi yasa ban shigo