Sashe 87
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
hannayensa yace "Throw back! That period I do call you jewel, while captain call you Jasmine," ganin kallon da take masa na rashin fahimta yayi murmushi yace "Rayuwar ki na kwanakin baya ne..... Watch it.. You might like it" shiru tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai assuringly, a hankali ta sauke kanta kasa yace "Let go" ba musu ta bi bayansa tana jujjuya disc din hannunta, xaune suka tarda su junaid, ta xauna gefen Ummi, El-ameen kuma ya tsaya suna jiran a kira su, lokaci lokaci ta kan juya ta kalli junaid kuma duk kallon da xata yi masa sai sun hada ido alamar shi ma kallon nata yake, can dai ya mike yace ma Abdul xai siyo ruwa ya bar wajen, bai kuma dawo ba sai da aka fara announcing jirginsu ne next din tashi, hannu kawai ya daga ma su Abdul ya shiga tafiyarsa, bin sa da ido Zahrah tayi, can ta kalli El-ameen dake kallonta ta d'aga masa hannu ta juya da sauri ta bar gun. Har suka sauka kt bbu wanda yace komai tsakanin junaid da El-ameen, taxi El-ameen ya tsayar masu ya kallesa alamar ya shiga, a karo na farko junaid yayi magana yace "Ae tafiyar mu ba daya bace, ka tafi xan samu wani" kallonsa kawai El-ameen yake can kuma ya shiga taxin da kayan tsarabarsu ya fadi ma driver din inda xa shi drivern ya ja motar suka bar junaid tsaye, kalle kallen inda zai xauna ta dalilin jirin da yake gani junaid ya shiga yi, can ya samu dakali ya xauna ya rike kansa, ya kusa minti goma xaune kafin ya mike da kyar daga karshe ya samu wani taxin ya shiga. Biyar saura ya shiga gida har lokacin yana ganin jiri, part din Mumy ya nufa, bbu kowa parlon ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta Hisnul Muslim a hannunta, kallonsa ta shiga yi har ya karaso gabanta ya durkusa ya daura kansa kan kafarta, ita dai kallonsa kawai take, dumin da taji a kafarta ya sa ta dago kansa tana kallo, hawaye ta gani fuskarsa, da mamaki tace "Me ya faru?" Kasa ce mata komai yayi sai hawaye, nan da nan hankalinta ya tashi tace "Ahmad!" Mayar da kansa yayi kafarta ta sauko kasa hankalinta ya tashi sosai tace "Talk to me son, me ya faru" rasa abun da xai ce mata yayi kawai ya rungumeta cikin sanyayyan muryarsa yace "Nothing mum, just forgive me plss" ji tayi hankalinta ya kwanta, a sanyaye tace "I've done that since son" a hankali ya xame jikinsa kansa a kasa yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya fita daga dakin ya koma part dinsa yana shiga ya rufe kofar yasa makulli ya hade kansa da kofar wasu sabbin hawayen na xubo masa, ya kusa minti talatin tsaye kawai kuma ya bude kofar ya fice, can gidansa ya nufa cikin a dai daita, yana sauka ya ba sa kudin sa ya shiga gidan, ya kusa minti goma tsaye parlor sannan ya haura sama, dakin da Zahrah take ya fara budewa, hular ta ne kwance kan gado da ribbon sai zaninta, gadon na nan yanda yake tun daren da ya shigo ya tada ta bayan yaji an shigo gidan, karasawa cikin dakin yayi a sanyaye ya dau hular da ribbon yana kallo, juyawa yayi yana kallon takalminta dake ajiye a kasa daga kusa da gadon, ya kalli gaban mirror dake dauke da kayan shafanta, sai Qur'aninta dake ajiye daga gefe, xaunawa yayi gefen gadon ya lumshe ido ya rike kansa da yayi masa nauyi. A can masarautan bauchi kuwa tunda Zahrah suka dawo take kuka a dakinta bayan ta kulle kanta, bbu wanda ta saurara ta bude kofar har kusan goma na dare, mikewa tayi xaune da sauri tana kallon disc din da El-ameen ya bata da ta ajiye gefenta, dauka tayi ta mike ta nufi inda laptop dinta ke ajiye ta dauka ta dawo ta xauna gefen gado ta bude ta kunna. *Haske writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ Still Zahrah tayi ganin kanta xaune a wani parlor kasan rug, doguwar riga ce jikinta da hula a kanta, Junaid ta gani tsaye parlon yana danna waya can ya karaso ya xauna kujera, gani tayi ta juya tana kallonsa, shi ma kallon nata yake can ya ci gaba da dannar wayarsa, wata dattijuwa ce ta shigo parlon tana isowa gabanta ta xauna ta ajiye plate din hannunta me dauke da potatoe da ketchup, dattijuwar ta dau potatoe daya ta dangwala da ketchup din ta kai mata baki, taga ta karbe daga hannunta tana jujjuyawa can ta Kai baki ta lashe sannan ta mayar mata, tuni hawaye ya cika idon Zahrah, Junaid dai kallonsu kawai taga yake, dattijuwar ta jawo ta jikinta ita ko tayi lamo, saukowa junaid yayi ya dau dankalin ya kai mata baki ta kauda kai da sauri ta dinga shigewa jikin dattijuwar, ya tabe baki ya ajiye, Suna ta xaune a haka sai ga El-ameen ya shigo parlon, kallonsa kawai Zahrah take ko kiftawa bbu, farar 3 qtr ne jikinsa sai blue polo kallo daya yayi ma junaid ya karaso ya durkusa gabansu ita da dattijuwar ya ajiye ledan hannunsa, ba a dau lkci ba dattijuwar ta mike bayan ta xaunar da ita ta bar wajen, taga El-ameen ya xauna gabanta ya dago kanta yana kallon fuskarta ita ma kallon nasa take, Junaid dai bai ko kallesu ba waya kawai yake kallo, murmushi me kyau El-ameen ya mata taga ya lakaci hancinta ita dai idonta na kansa, dankali ya dauka ya dangwali ketchup ya kai mata baki ta kauda kai, hade rai taga yyi ya rike kanta ya kai dankalin bakinta, a hankali ta ga ta fito da harshe ta lashe ketchup din, dariya ta ga ya fara yi yana kallon junaid da yaki kallon inda suke, Zahrah bata san lokacin da tayi murmushi ba hawaye na sakko mata, taga ya kuma dangwala ya kai mata ta lashe, xaro ido tayi ta rike breathe ganin ya kai dankalin baki, sai kuma ya kalli Junaid da sauri yaga ba kallonsu yake ba, sosai jikinta yayi sanyi ta kasa daina kallonsa wasu sabbin hawayen na xubo mata, gani tayi junaid ya mike ya fice daga parlon, El-ameen ya jawo ledan da ya shigo da ya bude ya fiddo da magunguna da hollandia yoghurt, ya jawo cup din dake wajen ya bude drink din ya xuba ciki sannan ya dauka ya kai mata baki ba musu taga ta bude bakin tana sha har ta kauda kanta daga karshe, kadan ya sha ya ajiye cup din ya mike ya bar wajen, gani tayi ta jawo cup din ta juya upside down, drink din ya malale a gun har a jikinta, El-ameen ya karaso wajen yana kallonta, can ya hade rai ya durkusa ya ja hancinta, hannu tasa ita ma tayi yanda yayi sai kuma ta ja nasa hancin shi ma, murmushi Zahrah tayi ta lumshe ido, can ta bude a hankali, magani taga ya kada a cup ya kai bakinta, ba musu ta bude ya juye mata, ta shiga yamutse baki ya ciro handkerchief a aljihunsa ya goge mata bakin ya mayar sannan ya mike, Datijjuwar daxu ta ga ta dawo, shi kuma ya bar parlon, dattijuwar ta daga ta bayan ta dauke cups din gun suka bar parlon. Haka Zahrah ta dinga kallon irin rayuwar da tayi a baya, duk jikinta yayi sanyi sosai banda hawaye bbu abinda take, wani gun tayi murmushi wani kuma tayi dariya, tunanin da me xata biya dattijuwar nan ta dinga yi, har inda take xata so a kai ta, wani tausayin El-ameen ta ji dinga ji har cikin ranta, ashe haka yayi hidima da ita, ta ga dai kafin ta ga kanta tare da Junaid sau daya ta ganta da El-ameen sau goma, kuma taga junaid da ya shigo bai wuce minti biyar sai taga ya fita kuma kullum fuska a daure barin idan El-ameen na gun, a wani gu ne ma da El-ameen baya parlon taga ya xauna gabanta har ya dago kanta yana kallonta, can kuma ya mike ya koma kujera, gajiya Zahrah tayi daga karshe ta kashe laptop din ta koma ta kwanta a sanyaye, kasa bacci tayi daren ranan tunanin El-ameen take? na junaid ne? Duk ta kasa tantancewa da kyar ta samu bacci ya dauketa sai dai har asuba mafarkan junaid kawai take, tana idar da sllh bayan ta tafi ta gaida Abbanta da Umma ta tafi bangaren Kilishi ita ma ta gaida ta, Ummi ta shiga nema ta ganta bedroom din Kilishi ta ja ta suka fita ta koma part dinta da ita, Ummi tace "Ohh sis bacci fa xan koma" suna shiga bedroom Zahrah ta xaunar da ita ta ciro laptop dinta dake charge ta ajiye gaban Ummi tace "Idan kin gama kallon nan akwai tambayar da xan maki" daga haka ta kunna mata ta fice daga dakin, da farko Ummi kamar ta kashe laptop din tayi kwanciyarta sai dai hango yar uwarta da tayi a xaune ya sa ta bude ido daga nan kuma ta maida hankalinta gaba daya kai. Takwas saura Ummi ta fito parlor ta samu Zahrah kwance idonta lumshe alamar bacci take, jiki a sanyaye ta karasa ta xauna kusa da ita ta dafa ta cikin sarkewar Murya tace "Sister!" Bude ido Zahrah tayi da sauri tace "Ahmad!" Sai kuma ta maxa ta mike xaune tana kalle kalle, kallonta kawai Ummi ke yi, murya can kasa tace "Ahmad?" Zahrah da duk ta daburce lokaci daya tace "Ohh, Ummi, kin gama kallon ne" Ummi ta share hawayen fuskarta tana murmushi tace "Yeah and I love it Zahrah, I love it... Xan kai ma su Abba su ma su kalla...." Tana magana ne hawaye na xubo mata, Zahrah da ita ma hawayen ya cika idonta a hankali tace "but ina son in maki tambaya!" Ummi ta kalleta tayi mata murmushi tace "Ina jin ki My sis" Zahrah ta sauke idonta kasa tace "Between the two of them, waye ya ci ace baxan mance ba har karshen rayuwata, nd who deserve me?" Kallonta kawai Ummi ke yi, can tayi murmushi a hankali tace "My Dad! El-ameen... He soo deserve you sis, he gave