Sashe 54
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
din ta bi sa da kallo yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, ajiyar xuciya ta sauke a hankali ita ma ta kwanta, juyowa yayi ta mike xaune da sauri kamar xata yi kuka, yace "Ki kashe wutan nan da kika kunna" girgixa masa kai tayi tace "Plss ya Ahmad bana son duhu" mikewa xaune yayi tana ganin haka ta kashe wutan da sauri tace "Oya yi hakuri kwanta na kashe" dariya ta basa ya koma yayi kwanciyarsa, bayan kusan minti ashirin yaji ta birgino a hankali gefensa ta kwanta. Da asuba ya tasheta yin sllh ya fita daga dakin xuwa nasa, yau ma kamar jiya daga gida aka kawo masu breakfast, tea kawai junaid ya sha yayi kwanciyarsa a parlor yana jiran xuwan El-ameen don ya kirasa yace suna hanya, Karfe goma saura El-ameen ya shigo compound din da motarsa, mikewa junaid yayi ya nufi kofa ya bude, El-ameen ne ya fara fitowa ya xaga ya bude mata side din da take ta fito, sanye take da atamfa da hijab dinta fari har kasa, kallonta junaid yake ko kiftawa bai yi, El-ameen ya rufe motar ya bude baya ya fiddo jakar kayanta yana kallonta yace "Mu je baby" kallon gidan take ba tare da ta yi motsi daga inda take ba, yayi murmushi ya shiga gaba ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar me tausayin kasa, ya juya yaga tana biye da shi ya ci gaba da tafiyarsa, kallonsu junaid yake har suka iso balcony ya lumshe ido ya bude ya basu hanya, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine ya ga ta ki karasowa, yace "Come on mana" a hankali ta shiga tahowa Junaid ya bi ta da kallo har suka shiga parlon, juyawa yayi ya bi bayansu, El-ameen ya nuna mata kujera ta xauna bayan ya ajiye kayanta da ke hannunsa shi ma ya xauna yace "Baby ba ki gaishesa ba" ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallon junaid tayi da fararen idonta a hankali tace "Ina kwana" kasa amsawa yayi ya d'an mata murmushi kawai, sosai haskenta ya kara fitowa da gani kasan ba karamin kulawa take samu gun Dr Sumayya ba, Humainah ce ta sauko parlon jin shigowar mota, kallonsu ta shiga yi da d'ad'd'aya da d'ad'd'aya daga inda take tsaye duk da ba ganin fuskokinsu take ba, El-Ameen ya hade rai, ta karaso cikin parlon idonta ya sauka kan jasmine still tayi gabanta yayi mugun faduwa tana kallonta, Junaid yace "Amm.... Kin ganta she will keep you accompany ana kiranta da Baby...." Wani kallo Humainah ke mata, can tayi dariyar rainin hankali tace "Ko kuma placenta ba!" Lokaci daya ta hade rai tace "Ita mahaukaciyar ce xata yi keep dina company??" Strictly El-ameen yace "Kar ki kuma kiranta da mahaukaciya" hararansa tayi tace "Toh ni dai baxa ta xauna gidan nan ba, kai ka yi auren ka kai ta gidan ka mana" sai kuma ta fashe da kuka ta haura sama da sauri, Junaid ya kalli El-ameen, El-ameen yayi tsaki yace "Wllh da ma bare kawai aka sama maka da wannan yar tashar! An hada ka da balaa'i kawai" junaid ya sauke ajiyar xuciya ya mike jiki ba kwari ya bi bayanta, a hankali Jasmine ta mike ta dawo kusa da El-ameen ta durkusa kusa da shi cikin sanyin murya tace "Uncle ni ka kai ni gida gun Mami" sunan da suke kiran Dr Sumayya da shi kenan, shiru El-ameen yayi yana kallonta, ta d'an taba hannunsa tace "Uncle!" Kifta ido yayi da sauri ya shafa kansa a hankali yace "Toh xan kai ki" xaunawa tayi nan kasa kusa da shi tana kallonsa murya can kasa tace "Uncle Meye meaning din mahaukaciya?" Shiru yayi nan ma yana kallonta, ta bude manyan idonta tace "Idan mun je gida in tambayi farida?" Murmushi ya mata hade da gyada mata kai. *Haske Writers association* [1/14, 9:15 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 46..... Kwance junaid ya sameta tana kuka a dakin, ya karasa ya xauna kusa da ita ya dago ta, turasa ta shiga yi cikin kuka take cewa "Ni ka kyaleni, ka kyaleni" a hankali yace "Listen to me plss Humainah, ba fa mahaukaciya bace" ta fashe da matsanancin kuka tace "Nace ka kyaleni ni dai" saketa yayi yana kallonta, ta koma ta kwanta tana ci gaba da kukanta, mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma parlor, El-ameen dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Junaid ya xauna ya shafa kansa yace "Shknn you can go Idan tafiya xaka yi" El-ameen yace "Toh gimbiyar taka ta yarda kar in tafi in bar yar mutane ta kasheta kana kallo" Junaid yace "In xaka tafi kayi tafiyar ka kawai" mikewa El-ameen yayi yana kallon Jasmine yace "Baby xaki tsaya nan har in dawo kin ji" kallonsa kawai take, ya durkusa kusa da ita yace "Kin ji?" Idonta ne ya cika da hawaye, a hankali El-ameen yace "Kuka kuma baby" shi dai junaid kallonsu kawai yake, El-ameen ya ciro handki ya mika mata yace "baxan dade ba xan dawo kin ji" karba tayi ya mike ya kalli Junaid sannan ya fita daga parlon. Kallonta kawai Junaid ke yi kanta a kasa tana fidgeting fingers dinta, can ya mike ya kullo kofar sannan ya dawo ya dau jakar kayanta yace "Tashi mu je" mikewa tayi a hankali tana kallonsa ya d'an mata murmushi yace "Follow me" daga haka ya nufi stairs ta bi bayansa, dakin dake kusa da na Humainah ya bude ya shiga ta tsaya daga bakin kofa tana kallon dakin, juyawa yayi yana kallonta yace "Shigo mana" a hankali ta shiga dakin ya rufe kofar, kan gado ya ajiye jakarta ya bude closet yace "Ki ajiye kayan ki duka a nan kin ji?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya nuna mata kofar bayi yace "ga toilet nan" kallon kofar tayi ta gyada masa kai, yace "Are you hungry?" Girgixa masa kai tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kunna mata tvn dakin yace "Ki xauna kiyi kallon ki toh" ta gyada masa kai ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofar, da sauri ta mike ta nufi kofar ta bude, yana tsaye bakin kofar Humainah ya juyo yana kallonta, dawowa yyi yace "Ya aka yi?" Kamar xata yi kuka tace "ina jin tsoro" shiru yayi yana kallonta ta bude kofar sosai ta koma ta xauna a dakin, Dakin Humainah ya karasa ya bude ya shiga ya sameta har lokacin tana kuka ya rungume hannayensa yana kallonta, can ya karasa kusa da gadon ya xauna yace "Ke yanxu baxa a iya cin arxiki gun ki ba, baxa ki yi taimako ba, kwana biyu fa kawai xata yi ta bar gidan" ko kallonsa bata yi ba ya dagota ya rungumeta yace "plss mana, wllh xata bar maki gidan soon, she's not staying long" turasa tayi tace "Bana so, kuma ni ka rabu da ni" hade rai yayi ya saketa ya mike yace "Toh wai gidan ki ne nan din? Ko a kanki take xaune" dago kai tayi tana kallonsa, ya watsa mata wani kallo ya juya ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta fashe da har da shessheka. Dakin sa ya koma ya kwanta yana tunanin anya decision din da yayi na kawo jasmine gidan yayi daidai kuwa, har aka kira Azahar yana kwance, mikewa yayi daga karshe ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, nan dakin yayi sllh yana xaune kan darduma bayan ya idar aka danna bell din gidan, mikewa yayi ya fita har lokacin dakin da jasmine take a bude yake, parlor ya sauka ya bude kofa, fatima da khadija ne bakin kofar rike da flask din abinci, gaishesa suka yi ya karba yace "Mun gode, ku gaida mutan gidan," daga haka ya kulle kofar ya dawo cikin parlor, plate ya dauko a kitchen ya dibi couscous din dake cikin flask din ya bude na miya ya diba sannan ya rufe ya dau goran ruwa da cup da spoon ya haura sama, dakin da jasmine ke ciki ya shiga, kwance ya ganta a kasa ta takure waje daya tana bacci, ya shigo dakin ya ajiye abincin hannunsa yace "Jasmine" sau uku yana kiranta ganin bata tashi ba ya durkusa gabanta ya d'an taba ta, bude ido tayi ta mike xaune da sauri ganinsa, yayi mata murmushi ta sunkuyar da kai, yace "Me yasa baki kwanta kan gadon ba" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauko darduma ya shimfida a kasa yace "Dawo nan" mikewa tayi ta xauna kan darduman ya ajiye mata abincin da ruwa a kai yace "ga abinci ki ci" kai ta gyada masa, yace "Toh ci mana" a hankali ta dau spoon din da dibi abincin ta kai baki tana kallonsa, murmushi ya mata yana kallon yanda take tauna abincin, yace "You like it?" Kai ta gyada masa, ya mike yace "Toh maxa ki cinye kafin in dawo" daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Ko da ya dawo xaune ya sameta ta tura abincin gabanta tayi jigum, ya karaso ya durkusa gabanta yace "Baki ci ba kuma" ta girgixa masa kai a hankali tace "Na ci" yace "No! kadan kika ci" spoon din ya dauka ya dibi abincin ya kai mata baki, a hankali ta bude bakin ya xuba mata, haka ya dinga bata har abincin yayi rabi ta kauda kai tace "Na koshi" ajiye spoon din yayi yana kallonta yace "Toh tashi ki je kiyi alwala ki xo kiyi sllh" mikewa tayi ta nufi toilet yace "Baki cire hijab din ki ba" dawowa tayi ta cire Hijab din ta ajiye, ya bi ta da kallo har ta shiga toilet din sai dai bata rufe kofar ba, mikewa yyi ya fita ya koma dakin sa. Lokaci lokaci ya kan lekota, tausayinta kawai yake ba kadan ba barin yanda ya lura duk a tsorace take, ana kiran sllh magrib ya shigo dakin bai ganta ba, kiranta ya shiga yi amma shiru ya juya ya fita ya sauko downstairs, kitchen ya sameta tana wanke d'an plates din da aka bata, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, da sauri ta juyo a tsorace, wara ido yayi yace "Uhum!" A hankali tace "washing nake yi" murmushi yayi mata