Sashe 82
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kuka tace "Ae dama nasan jikana yaron kirki ne, Allahu Akbar, xaka aikata fiye da haka ma don k'akan ka ka gado " sunkuyar da Kai Junaid yayi ya kasa ci gaba don dama yanda yake bada labarin kamar bai son yi, Aminin sarki ne yayi Encouraging dinsa da ya ci gaba don sarkin kasa cewa komai yayi banda ido da ya tsura masa, Zahrah kam banda kuka babu abinda take jikinta yayi sanyi ba kadan ba, ita kanta Mumy hawayen ne ke sakko mata, cikin sanyin murya junaid ya ci gaba yace "I had to take her away..... muka bar gidan and....." shiru yayi kafin ya fadi yanda suka yi hatsari bayan barinsu gidan wanda shi ne dalilin dawowan hankalinta sai dai kuma tayi losing memory ta mance komai, bai boye yanda ya janye jikinsa daga lokacin bisa umarnin da iyayensa suka basa, ya fadi yanda ya bar ta da El-ameen bai kuma bi ta kanta ba, El-ameen kuma ya kai ta gidan Course mate dinsa tayi kusan wata biyu a can, a watannin ta biyu a gidan sau daya yace yaje daga nan kuma bai sake komawa ba, har aka yi aurensa da Humainah, ya fadi shawarar da El-ameen ya basa da yanda ya amince ya maidata gidansa da xama gaba daya ya kuma sa ta a islamiyya, bai boye irin matsalolin da suka dinga fuskanta da Humainah a kanta, ya kuma fadi dalilin sa na sakin Humainah, bai rufa komai ba kan irin xaman da suka yi da Zahrahn bayan barin Humainah gidan har ya kai karshen labarin da fadin dalilin dawowar memory dinta, sai da idon kowa ya kawo a parlon, ya kusa minti biyar kansa a kasa kafin ya dago a hankali, hawaye ne cike idonsa ya mike ya isa gun Mumy ya durkusa ya daura kansa a kafarta a sanyaye yace "Ki gafarceni Mumy, nasan nayi disobeying din ki, na kuma boye maki abinda nayi which I wasn't suppose to ko da kuwa baxa kiyi supporting dina ba shi yasa komai bai tafi min dai dai ba, forgive me plss Mumy....." Hawaye kawai Mumy take bata iya ta ce masa komai ba, ya mike ya isa gun Abbansa shi ma ya durkusa gabansa hawaye na sakko masa yace "Ka yafe min Abba, I know I... I failed you....."Jin Abba bai ce komai ba yasa shi mikewa a sanyaye, tashi sarki yayi ya taka har gabansa ya dafa sa sai kuma ya rungumesa yace "They will all forgive you in'sha Allah son, sannan ina me umartarka da ka mayar da matarka ka nemi gafararta....." Daga haka ya sake sa ya isa gaban Abba yace "Ina neman alfarmar ku yafe ma Ahmad duk abinda ya maku a kan Zahrah...." Murmushi Abba yayi ya mike yace "Bai min komai ba mai martaba, Allah ya basa ladan abinda yayi, ina alfahari da kasancewarsa d'ana, yasan ba lallai in sauraresa ba a lokacin shi yasa yayi komai gaban kansa, Allah ya biyasu gaba daya da abokin nasa, is good thing sun riketa amana, ta kuma samu lafiya ta dalilin su, I am proud of them....." Mikewa Mumy tayi a sanyaye xata fita Sarki yace "Toh Hajiya bamu ji kin ce kin yafe masa ba, ina nema masa wannan alfarmar don Allah" murmushi kawai tayi, Hajja da baki ya ki rufuwa tace "Yo wa ya sani ko bakin ciki take masa kamar yanda matan ubansa ke masa, ni dama tun ran da Amadi ya kawo yarinyar gidan na daura ido na kanta na ji ta kwanta min toh tunda yan gida suka ce mahaukaciya ce basu san xance ba ina ni ina magana ace don ba ni na haifesa ba" kallonta kawai junaid yake haka ma El-ameen dake murmushi, sarki yayi murmushi shi ma yace "Da fatan mun kafa xumunci kenan har illah maa'sha Allah" Hajja ta mike da sauri tace "toh ni makka xaka kai ni, shekarana uku rabona da can wllh" 'yar dariya sarkin yayi yace "Kina da kujeru biyar wannan shekarar Idan Allah ya yarda" shewa tayi tace "Allah yayi maka albarka...... Sai mu je tare da Humainah da kawayena Uku" kofa junaid ya nufa xai fita daga parlon sarki ya kirasa, juyowa yayi yana kallonsa, sarkin yace "Ina gayyatar ka masarautar mu tare da El-ameen, ur labours will not go in vain" Shiru Junaid ya d'an yi sai kuma yayi kasa da kai yace "Sai na dau excuse gun aiki idan Allah ya yrda" Kai kawai sarkin ya gyada masa, Satan kallon Zahrah yayi ya juya ya fice, kamar warce aka tsikara ta mike ta bi bayansa da sauri. *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 77...... Bin bayansa Zahrah tayi, ya ki tsayawa ita ma bata ce ya tsayan ba ya nufi part din Mumy, yana bude kofar ta ja ta tsaya tace "Amm... Ahmad Junaid!" Lokaci daya ya juyo ya sauke idonsa kanta yace "Yess!" Wani mugun kwarjini ya mata ta kasa cewa komai sae kallonsa take, daga kasa har sama ya kalleta sannan ya juya yayi shigewarsa parlor, still tayi gun kamar warce ruwa ya cinye, duk wannan abun El-ameen na tsaye balcony yana kallonsu, juyawa tayi suka hada ido da shi, hawaye ne ya ciko mata ta sauka daga balcony din da sauri ta nufi gunsa tana kallonsa lokaci daya hawayen idonta ya silalo tace "kaga abinda yayi min koh?" Murmushi El-ameen yayi ya buda ido yace "Yea! Haka nan yake! but idan ya sauko xa ki ga he is the sweetest guy you never expect.... He's still angry at you ne shi yasa" a sanyaye tace "But he shud have listen to me..... He's a sadist I notice" dariya sosai El-ameen yayi ta turo baki, tace "I just have to make him forgive me before leaving that's all!" El-ameen ya d'age gira yace "Go in ki samesa...." Shiru tayi sai kuma a hankali tace "In je?" Gyada mata kai yayi ta juya ta koma part din Mumy, tafiyarta kawai yake kallo har ta isa kofa ta murda a hankali ta tura ta shiga, durkushe ta gansa a parlon kusa Humainah dake kwance kan doguwar kujera idonta lumshe, tsaye tayi bakin kofar ta kasa karasowa, kallo daya yayi mata ya dauke kai, Dakewa tayi ta karaso parlon cikin rashin kuxari, dai dai lokacin da Humainah ta mike xaune da sauri, ya mike ya xauna gefenta yana kallonta ganin yanda ta rame, hannunta ya rike kamar bai son magana don bakinsa kadai yayi motsi yace "What wife!" Ta dafe kanta bata ce komai ba, can ta d'ago da kyar tace "Amai nake ji" mikewa yayi ya daga ta suka bar parlon, ita ko lura da Zahrah da tayi still tana kallon ikon Allah bata yi ba har ya shiga da ita daki, Zahrah taji ta ma kasa tsayuwar, tunda take bata taba jin abinda ta ji a lokacin a xuciyarta ba, kawai ji tayi hawaye ya cika idonta, ta juya da sauri har tana neman faduwa ta fice daga parlon. Bata ko kalli El-ameen dake tsaye har lokacin ba ta tafi can karkashin bishiya tayi xamanta gun ta fashe da kuka, juyawa El-ameen yayi ya koma parlon Abba, drinks ne da ruwa gabansu mai martaba kuma ga dukkan alamu hajja ce ta debo masu, yana shiga tace "yauwa tafi ka kira Amadin su yi sallama da Sarkin wai xa su koma" fita ya kuma yi ya tafi part din Mumy, khadija da fatima ne parlon don dama suna ganin shigowar junaid suka shiga daki, amsa gaisuwar fatima yayi yace "Ina Junaid din?" Khadija tace "Yana daki" yace "Tafi ki ce masa Abba na kiransa" mikewa tayi shi kuma ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba Junaid ya fito ya karasa gun El-ameen, El-ameen yace "Hope ka saurareta dai yanxu?" Girgixa kai yayi yace "Bani da lokacin ta, bana kuma bukatan godiyar da xata min ko hakurin da xa ta ban, don Allah nayi mata ba don ita ba wllh" Murmushi El-ameen yayi yace "Gaskiya ne" Junaid ya shiga parlon Abba, nan dai suka yi sallama da mai martaba dake sauraren xuwansa da El-ameen nan da kwana biyu, Zahrah na ganin fitowar Abbanta ta mike ta nufi gate da sauri, Ummi ta bi bayanta ganin mood dinta, Abdul ma bin ta yayi da kallo, har bakin mota Hajja da su Abba suka raka mai martaba, sai surutu take masa kamar irin ta san sa da can, junaid dai na biye da su a baya, lokaci lokaci mai martaba kan juyo ya kallesa, ita ko Zahrah can wani mota ta tafi ta tsaya a baya Ummi sai tambayarta take meyasa mood dinta ya canxa amma ta ki cewa komai, a hankali junaid ya dinga bin wajen da kallo ganin bai ganta ba, har cikin motar dake gabansu sai da ya kalla bbu ita, El-ameen dai na tsaye rungume da hannayensa yana kallonsa, tsaf ya gane me yake nema, kawai yayi murmushi, Mai martaba kansa sauraren Hajja kawai yake amma rashin ganinta ya sa ya fara waige waige shi ma, can dai yace "Ina Zahrahn ta xo ta shiga mota" Ummi ce tace "Toh kinji Abba na neman ki ma, ki taho mu je" ba musu Zahrah ta fito daga bayan motar sai dai duk jikinta a sanyaye, satan kallonta Junaid ya dinga yi har ta iso gun motar da suka taho da, Hajja ta jawota ta rungume tace "Kice ma Uwar ki ina nan xuwa, xata yi babbar bakuwa don tare xamu taho da su Amadi, Allah ya maki albarka ni dama tun farkon ganin ki kika kwanta min don akwai ni da tausayi" kai kawai Zahrah ta gyada mata ta bude bayan mota ta shiga Ummi ma ta shiga, junaid bai fasa mata kallon sata ba, ita ko bata ko kalli su waye a tsaye gun ba, tana shiga motar ta rufe ido, bata kuma bude ba sai da taji tashin motar da fatan kai wa gida lafiya da su Hajja keyi masu, ta kalli tagar motar suka yi ido hudu da junaid, dauke kai tayi da sauri, can kuma ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma, d'an murmushi ta kirkira ta daga masa hannu a hankali, shi ma ya mayar mata da murmushin, driver