Sashe 15
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma ta matso a hankali ta lashe ketchup din, El-Ameen ya wara ido yana kallonta, sai kuma ya saka dariya, murmushi junaid yyi yana ci gaba da danna wayarsa, sae tsotsan ketchup din take a baki, El-Ameen ya kuma dangwala ya kai bakinta ta kuma lashewa, rike kanta yayi ya tura mata dankalin a baki ta fito dashi ya fadi kasa, ya hade rai yace "I will slap yhu fah" kallonsa kawae take ko kiftawa babu, ya dauki wani dankalin ya dangwali ketchup ya kuma kai mata baki, lashewa ta kuma yi ta bar masa dankalin tana tsotsan bakinta, yayi murmushi yana kallon Junaid yace "this shows tana son ketchup lkcn da take da hankali" shi dae junaid bae ce komae ba, El-Ameen ya dinga dangwalan tomatoe din yana kai mata baki tana lasa, exotic drink ya bude ya juya yana kallon Junaid yace "Get me cup plss a kitchen Captain, kaga dai patient dinka nake feeding" Junaid bai ce komai ba ya mike ya nufi kitchen ya dauko cup din ya kawo masa, ya karba ya tsiyaya drink din ya dauka ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri, ya juyo da ita ya rike kanta ya kai cup din lip dinta, kadan ta kurba ta cire bakinta tana yamutse fuska, xae kara bata ta sa hannu xata karbi cup din ya sake mata, ta dade tana kallon cikin cup din kafin ta kifar da lemon nan tsakiyarsa, El-Ameen ya mike da sauri ya bar wajen cikin tsawa yace "Kehh!" Tsorata tayi sosae ta dinga shisshigewa jikin kujera, ya karasa kusa da ita ya duka ya mata knock a kai yace "kika sake min irin haka sae na tsula maki bulala" Murmushi Junaid yayi yana shafa kansa, El-Ameen ya dago ta ganin drink din duk ya bata kayan jikinta, tsaye ya bar ta nan wajen ya fita xuwa ya kira Mama, ta juya tana kallon Junaid dake kallonta, ya sakar mata murmushi ta dauke kai ta durkusa wajen ta jawo ledan take away din da Irish din ke ciki ta dauki wanda yake bata ta ajiye gefe, ta bude wanda bae taba ba ta tsura ma dankalin ido, kifarwa tayi a kasa, Junaid ya mike da sauri yace "Noo! Me yasa kika xubar" kallonsa tayi kafin ta maida hankalinta kan abinda take, ta dauki take away din da ya fara bata ta juye cikin na wanda ta xubar a kasa sannan ta mike tsaye, tattare gown din jikinta tayi ta juye dankalin a rigarta ta jefar da take away din, Junaid ya langwabar da kai yana kallonta ya ma rasa me xae ce mata, El-Ameen ne ya shigo Mama na biye da shi a baya yana mata magana, tsayawa yayi daga bakin kofa ya bude baki ganin barnar da tayi, tana ganinsa tayi kusa da Junaid ta tsaya rike da rigarta da ta juye dankali ciki tana kallonsa, El-Ameen ya karaso palon da sauri cikin fada yace "Whatt! junaid kana kallonta ta xubar min da abincin da xan ci?" Bai jira cewar Junaid ba ya nufeta, sake rigarta tayi dankalin ya xube gaba daya kasa tayi bayan junaid da sauri, har wani bari jikinta yake, Junaid ya dakatar da shi da sauri yace "Hey, Look Dr, naga in tana da hankali ae baxata yi haka ba, have you forgotten mahaukaciya ce kamar yanda kake kiranta, wannan ae xalunci kawae kake ma patient din taka, ba dae yunwar Irish kake ba, kar ka damu I will get yhu enough idan muka fita" El-Ameen yyi masa wani irin kallo yace "Da'alla my frnd ba kana kallonta ba ka kyaleta, Better tunda dai xaka siya min wani, but wnn ae iskanci ne ba rashin hankali ba, don bata da hankali sae ta dinga sa mu aiki?" Junaid yace "naji xan gyara wajen is that all" Mama dake tsaye palon tana kallonsu tayi murmushi tace "xan gyara wajen bokon turai, kasan sae a hankali, kuma ma wllh hauka me tsafta take yi bata da kaxanta ko kadan" El-Ameen yayi kwafa yana kallonta ganin yanda take lekosa daga bayan Junaid yace "Ni nasan maganin ki ae, kina wani leko ni da Idanuwan nan naki" Junaid ya d'an tabe baki ya koma ya xauna, Mama ta nufi kitchen don dauko abinda xata gyara wajen. karasawa gabanta El-Ameen yyi ya kama hannunta ta fasa ihu, kunnenta ya ja ta nufi sama da ita, Junaid ya bi su da kallo sannan ya girgixa kai a hankali ya jinginar da kansa jikin kujera. Bayi El-Ameen ya shiga da ita ya wanke mata hannayenta sannan ya fito da ita ya xaunar gefen gado sai kallonsa take, wani kayan ya ciro mata ya ajiye gefen gadon, yana kallonta yace "ki daina kallona haka keh, kuma kika kuskura kika tashi a nan sae na xane ki, clear?" ita dae kallonsa kawae take, sae ta basa dariya ganin irin kallon, ya rungume hannu yace "Uhhn! Halan dai kin san ni ne?" murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Mama jummai yace ta tafi ta canxa mata kaya bayan ta gama gyara gun da ta bata, mama tayi shiru sae kuma tace "Naga idonta biyu fa" El-Ameen yayi dariya ya xauna yace "ae bata komae mama, shi yasa nace ki tafi ki canxa mata, kar ki samu damuwa bbu abinda xata maki, tana da nutsuwa sosai" mama jummai bata musa ba ta nufi sama cikin rashin kuxari. Tana nan xaune inda El-Ameen ya bar ta a dakin ta sameta, kin rufe kofar Mama jummai tayi in case, ta karasa kusa da ita tana d'ari d'ari ta dauki blue gown din da ya fiddo mata, a hankali mama jummai tace "Baiwar Allah kaya xan canxa maki kin ji" ko kallonta bata yi ba, hakan ya kuma tsorata mama jummai, juyawa tayi a sanyaye ta koma Palo tana kallon El-Ameen tace "D'an nan wallahi tsoro nake ji ni kam, kaga sae tana bacci nake shiryata" dariya yayi ya mike ya nufi stairs din suka koma sama a tare, junaid ya bi su da kallo. Xaune suka tar da ta har lkcn sae dai wannan karan windon dakin ta tsura ma ido, El-Ameen ya karasa kusa da ita, ta juya da sauri tana kallonsa, kayan ya dauka ya mika ma mama jummai yace "Gashi mama" karasawa tayi ta karba, ya dago ta yana kallonta ya hade rai yace "Mama xata canxa maki kaya yanxu, stay still kin ji" ita dae kallonsa kawae take, ya juya ya kalli Mama jummai yace "Toh karaso Mama" a hankali ta karaso kusa da su, hannunta na rawa ta kai kan maballin rigar xata cire mata, ta fasa wani ihu tayi bayan El-Ameen da sauri, cikin sakwannin da basu wuce uku ba sae ga mama jummai can bakin kofa a mugun tsorace bayan ta sake kayan hannunta nan gabansu, dariya sosai El-Ameen yake yana kallonta yace "Mama baxa fa ta maki komae ba wllh" tace "A'a d'an nan nafi gane tana bacci wllh" a tsorace take maganan daga haka ta juya ta koma kasa, murmushi yayi ya juya yana kallon ta bayansa, dawo da ita yayi gabansa, ya kusa minti biyu tsaye kamar me naxari sai kuma ya leka rigar jikinta don ganin ko akwai kaya a ciki yaga akwai vest, rufe idanuwansa yyi a hankali ya balle dogon rigan jikinta snn ya fara cirewa idonsa kulle, ajiyewa yayi bayan ya cire har lkcn idonsa na rufe ya duka a hankali ya shiga laluban kayan da Mama jummai ta yar a kasa, yana tabawa ya dauka sannan ya mike, lalubawa yayi yaji bata wajen kuma, ae ba shiri ya bude ido da sauri yana waige waigen inda xae ganta, tsaye ya ga perfect fair figure dinta can jikin window, daga ita sai white vest da ya kusa cinyarta, vest din ya kamata sosai kasancewarsa very elastic, gaba daya shape dinta ya fito ga long fresh legs dinta da bbu tabo ko daya, kamar xaka latsa ta jini ya fito tsabar haske, juyawa yayi da sauri kamar wanda ya ga abun tsoro ya nufi kofa da hanxari, ko me ya tuna kuma sae yyi still bakin kofar ya kusa 3 mins kafin ya juyo a hankali ya dawo dakin ya nufeta ba tare da ya kuma kallon jikinta ba, hannunta ya kama yana kallon fuskarta ya shiga sa mata rigar hannunsa, yana gamawa ya xaunar da ita gefen gado ya hade rai ya dunguri kanta yace "Don't try dat again" cup ya dauka ya dauraye yayi mata diluting drugs dinta da ruwa sannan ya dawo kusa da ita ya rike kanta ya kai cup din bakinta, kauda kai tayi da sauri, yayi mata tsawa ita ma ta fasa masa ihu, rike kanta yyi ya tura cup din bakinta har sai da ta bude ya xuba mata, sae da ya tabbatar ta hadiye sannan ya kyaleta tana yatsinan baki tana komawa baya, jinin da ya gani bakinta yasa ya tsura ma lips din ido, handkerchief ya ciro aljihunsa ya goge mata bakin yace "Sorry!" Mayar da handki din yayi ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin ya ja kofar. Palo ya sauko ya ga ba Junaid, ya kalli mama dake xaune yace "Mama Junaid fa?" Tace "Ya tafi wai" shiru yayi bae ce komae ba, can yace "Ohk xan tafi yanxu, da daddare xan dawo, bacci xata yi yanxu" tace "Toh Allah ya kai mu, Allah kuma ya bata lafiya" yayi murmushi yace "Ameen" sannan ya fita. *Haske Writers Association* *Captain_Ahmad Junaid*