Sashe 48
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Morning jasmine, how you?" A hankali tace "Am fine, and you?" Shiru tayi da sauri kamar me naxarin abinda tace, can ta runtse ido ta dafe kanta ta durkusa wajen, ya sauko da sauri yana kallonta, ta kusa minti biyar a haka shi dai bai dagota ba bai kuma san ma me xai ce mata ba, mikewa tayi a hankali tana rike da kan ta juya ta bar wajen ya bi ta da ido, xama tayi kan kujeran da ke kusa da gadonta ta kifa kanta ta inda ba ciwo, komawa yayi ya xauna har lokacin yana kallonta. El-ameen ne ya shigo dakin bayan an idar da sllhn Asuba, ya samu Junaid xaune kan darduma, ya ajiye ledan hannunsa ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "Good morning captain, ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh" kallon magungunansa El-ameen yayi yace "Jiya baka sha drugs din ka ba ashe?" Junaid bai ce komai ba El-ameen ya tabe baki ya mike yana kallon jasmine dake xaune har lokacin kan kujera kanta kife kan gado, karasawa yayi yana kallonta ya ga bacci ma take a haka, ya dan duka yace "Hello!" Bude ido tayi da sauri tace "Hi" murmushi yayi yace "Good, tashi kiyi sllh" dago kai tayi da sauri tana kallonsa tace "Sallah?" Ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa kamar bata taba jin Kalmar ba, shi dai Junaid kallonsu kawai yake, El-ameen yace "Am coming" daga haka ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo tare da wata nurse rike da hijab, ya kalli nurse din yace "Ki rakata bayi, ki gwada mata yanda xata yi alwala" nurse din ta kalli jasmine sannan ta kallesa tace "Ban gane ba sir" Yace "Yes alwala xaki yi tana gani tana bin ki" nurse din ta kuma kallon jasmine dake kallonta ita ma ta ajiye hijab din hannunta tace "Toh sir" El-ameen ya kalli Jasmine yace "Tashi ki bita kiyi duk abinda tayi kin ji" mikewa tayi tana kallonsa ya gyada mata kai yace "Yes follow her" tace "I should follow her?" Murmushi yayi ganin yanda take catch up da sauri yace "Yes follow her" kamar me tausayin kasa haka ta dinga bin nurse din a baya har suka shiga toilet din, nurse din ta rufe kofar tana kallonta tace "Do you want to urinate?" Kallonta kawai Jasmine take kamar me naxarin word din, a hankali tace "Urinate?" Matar ta gyada mata kai, girgixa mata kai tayi, matar ta dau kettle daya ta mika mata ita ma ta dau daya tace "Kiyi duk yanda ki ka ga nayi" a hankali Jasmine ta durkusa tana kallon nurse din runtse ido tayi jin xafi a kneel dinta, nurse din dai sai kallonta take har ta bude idon, sannan ta yi bismilla ta fara alwalan tana kallonta, jasmine ta wanke hannunta ita ma kamar yanda ta ga n urse din ke yi, haka tayi ta kwaiwayon ta har suka kare alwalan nurse din ta fito tana biye da ita a baya, har lokacin junaid na xaune kan darduma, El-ameen ma na xaune yana jiran fitowar su, mikewa yayi yana kallon junaid yace "Pray mat malam" junaid ya tabe baki ya mike ya koma kan gado, El-ameen ya shimfida ya kuma dauko wani ya shimfida a baya, ya dau hijab ya mika mata yace "Ki saka" karba tayi tana kare ma Hijab din kallo, ya mata alama da tasa, kokarin sakawa ta shiga yi ta kasa don bata san ma yanda xata saka din ba, ya karaso yana murmushi ya karba ya saka mata, Junaid ya kauda kai hade da tabe baki, El-ameen ya nuna mata inda xata tsaya kan darduman yace "Kiyi duk yanda kika ga nayi" shiru tayi tana kallonsa, yace "Kin ji?" A hankali ta gyada masa kai, ya koma darduman gaba ya tada sllh, haka ta dinga binsa sllhn tana yin duk yanda taga yayi da kyar sbda kneel dinta, har suka idar ya juya yana kallonta, jini ya gani Hijab dinta ya dawo kusa da ita da sauri yace "Ohh!" Hannu yasa xai daga hijab din ta koma baya sauri tana masa wani kallo, komawa baya yayi cikin sanyin murya yace "Yi hakuri," mikewa yayi ya fita, ta juya tana kallon Junaid da ke kallonsu, dauke kanta tayi tana nan xaune har El-ameen ya dawo da nurse, nurse din ta duka kusa da jasmine tace "Sannu" daga hijab din tayi tana kallon kneel din, kayan aiki El-ameen ya miko mata nan ta fara gyara mata wajen, rufe idonta tayi da ganinta kasan daurewa kawai take, El-ameen ya durkusa kusa da ita yana mata sannu, har nurse din ta gama, a hankali ta bude idonta da ya kada, yace "Sannu" ta kallesa sannan ta sunkuyar da kanta, mikewa nurse din tayi ta fita da kayan aikin, tashi yyi ya dauke darduman da yake kai ita ma ta mike ta dauke dayan, Junaid ya dauke kai tun kan su kallo inda yake, ledan da El-ameen ya shigo da ya nufa ya bude ya fiddo da sabbin toothbrushes da toothpaste, ya ajiye ma junaid daya ya bude daya ya matsa toothpaste ya mika mata yace "Tafi ki wanke bakin ki" karasowa tayi ta karba tana kallonsa, murmushi yayi sanin bata gane ba kenan, yace "Follow me" da sauri tace "Follow her" dariya ta basa yace "No, follow me dai" daga haka ya shiga toilet ta bi bayansa, yana kallonta yayi mata alama da hannu da ta wanke baki da brush din, saka brush din tayi a baki ta tsaya, yace "Toh wanke bakin" tsotsan toothpaste din tayi ta cire brush din tana yamutse fuska, yace "No ba haka ba" ya mika mata hannu alamar ta basa ta mika masa ya kai brush din baki, nan ya shiga gwada mata yanda xata yi sannan ya mika mata, yanda taga yayi haka tayi yana kallonta har ta gama sannan ya nuna mata gun xuban ruwa yace "Wash ur mouth," karasawa tayi tana kallon wajen, yayi murmushi ya karaso ya bude mata ruwan ya tara da hannunsa ya kai bakinsa ya kuskure ya xubar sannan ya kalleta yace "Haka xa ki yi" tara hannunta tayi ita ma, ya tsura ma fararen hannun nata ido har ta kai ruwan baki ta kuskure kamar yanda ta ga yayi" murmushi ya mata yace "Good gal" juyawa yayi yace "Mu tafi" ta bi bayansa suka fito, bai yi mamakin rashin ganin junaid dakin ba, yana lafiya ma ya aka kare bare yanxu, kujera ya nuna mata ta xauna yace "Am coming" sannan ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Ba a dau lokaci ba ya dawo da bowl me dauke da apples, ya jawo table karami ya ajiye kusa da ita sannan ya daura bowl din kai yana kallonta yace "Eat" kallon bowl din kawai take, can ta sa hannu ta dau apple daya a hankali ta kai bakinta, bude kofa aka yi duk suka juya, gabansa ya fadi ganin Abbansa, Abba ya karaso dakin yana kallon gadon junaid yace "Where is my patient" El-ameen yayi saurin cewa "Ya d'an fita ne yanxu Abba" Abba yace "Ya fita da sassafen nan ya je ina?" El-ameen da gabansa ke faduwa yace "Ina jin ya fita ne, no cewa yayi xae fita ya sha iska" wani kallo Abba ke masa sannan ya kalli Jasmine dake kallonsa yace "Bana son in sake shigowa in ga yarinyar nan a nan Ahmad" kallon Abban nasa yayi a sanyaye yace "Toh Abba" Abba yace "Mutumin banxa kawai, kuma maxa kaje ka dubo min patient dina yanxu" daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine, murmushin karfin hali ya sakar mata yace "Eat your apple" sunkuyar da kanta kawai tayi, ya juya a sanyaye ya fita daga dakin. Babu inda bai duba ba a asibitin amma bai ga junaid ba, abun yayi mugun basa mamaki kar dai gida ya wuce, dawowa sama yayi bai kuma yi gigin xuwa gaya ma Abba bai gansa ba don yasan baxai ji da dadi ba, office dinsa ya fara tafiya ya dau makullin motarsa sannan ya tafi ward din da jasmine take ya ganta har lokacin rike da apple din bata ci ba, ya karasa kusa da ita yace "Eat mana jasmine" bata kallesa ba ya kama hannunta xai dago ga ta fixge hannun tana masa wani kallon da ya fadar masa da gaba ya d'an koma baya a hankali yace "kiyi hakuri" ya gane bata son a taba ta kenan, mikewa tayi tsaye, ya fara tafiya yace "Mu je" har ya isa bakin kofa ya juyo yaga bata biyosa ba, yafito ta yayi sai gashi ta fara tahowa, Suna tafe yana juyowa yaga ko tana binsa har suka fito haraban hospital din ya nufi parking space da ita, gaban mota ya bude mata ya mata alamar ta shiga, still tayi tana kallon motar kamar warce ta tuno abu, can kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, accident dinsu na jiya ne ya fado masa lokaci daya ya gane abinda yasa taki shiga, girgixa mata kai yayi yace "babu abinda xai faru jewel, shiga" kin shiga motar tayi still, ya xaga ya bude driver seat ya shiga ya tada motar kallonsa kawai take daga waje, can ta fara kalle kallen asibitin, a hankali ta shiga daga karshe yayi murmushi ya rufo motar, yana gama warming ya ja motar suka bar haraban asibitin bayan an bude masa gate, driving kawai yake ba tare da yasan inda xai kai ta ba, duk tausayinta ya cika shi, a hankali yace "Ina xan kai ki Jewel?" Kallonsa tayi ba tare da ta ce komai ba, Kanwar Abbansa ce ta fado masa kawai ya yanke shawarar kai ta can gidan, Karfe takwas da wani abu suka isa gidan, ya bude motar ya fito ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, yana gaba tana biye da shi a baya suka shiga gidan, bbu kowa parlon ya nuna mata kujera ta xauna, cousin sis dinsa ta fito daga kitchen da mamaki take kallonsa tace "Toh fa, yaya daga ina haka?" Yayi murmushi yace "Gida, kira min Mumy" daki ta tafi tana cewa lallai yau akwai ruwa da kankara, Hajiya salmah Kanwar dad dinsa ta fito parlon tana