Sashe 67
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
him, infact love him ma dai" ita dai bata dago ba bata kuma ce komai ba, ya dade xaune yana bata magana masu kwantar da hankali, daga bisanni yace "Kin ji Hafsat?" Hawaye na bin kuncinta ta gyada masa kai alamar toh, yayi murmushi ya mike yace "Toh Allah bada xaman lafiya" daga haka ya fita, El-ameen kadai ya gani xaune parlor, El-ameen na ganinsa ya mike ya nufesa yace "Da kai aka hada baki aka min auren nan koh Ahmad" Junaid yace "Toh ya xa kayi da ni" daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. Ko da junaid ya koma gida dakin Jasmine ya fara shiga yaga har tayi bacci, rage Acn dakin yayi ya sa mata blanket ya dawo dai dai kanta ya durkusa yana kallon fuskarta murya can kasa yace "Good nyt dear" ya fad'a tare da lumshe idonshi yana bud'esu a hankali, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya fita, dakinsa ya shiga yayi wanka ya canxa xuwa pyjamas dinsa, ya jima xaune gefen gado daga karshe ya fita ya shiga dakin Humainah. Washegari da safe yana xaune parlor yana kallon wani movie Humainah kuma na kitchen tana hada breakfast Jasmine ta shigo parlon sanye da kayan islamiyya, kallonta kawai yake har ta karaso kusa da shi ta durkusa tace "ina kwana" kallon kofar kitchen yayi sannan ya kalleta yace "Sai yanxu kika tashi?" Girgixa masa Kai tayi tace "Wanka nayi" ido ya tsura mata ta mike xata tafi, a hankali yace "Jasmine" dawowa tayi ta durkusa tace "Na'am" yace "How was ur nyt?" Tace "Alhmdllh" yace "baxa ki islamiyya ba yau!" Ta kallesa da sauri tace "fashi?" Shiru yayi kafin yace "Yes for only today xa mu fita ne" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi sama ya bi ta da ido. Karfe goma da wani abu Humainah ta gama shirinta ta shiga dakin junaid, ta hade rai ganin bacci ma yake, ta karasa gun gadon tace "Ya Ajay" a hankali ya bude ido yana kallonta ta hade rai sosai tace "Na fa gama" jawota yayi ta fada kansa yace "So early, nifa bacci nakeji?" ya fad'i yana lumshe ido, Ta turo baki tace "Dubi agogo fa" ya kalli agogon yace "Toh ai jiya da daddare ni ban yi bacci ba" kwace kanta tayi tace "Ni na hanaka" rikota yayi yace "Eh mana" murmushi kawai tayi tace "Ni dai ka tashi ka shirya ya Ajay" yace "Toh naji hada min ruwan wanka" mikewa tayi ta shiga bathroom din, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Na hada" yace "Toh mu je ki min" ficewa tayi daga dakin da sauri, yayi dariya yace "Ashe bbu inda xan kai ki kuwa" sha biyu saura Junaid ya fito bayan ya shirya cikin kananun kaya, ya shiga dakinta ya ganta xaune gaban mirror yace "Toh mu je" ta mike cike da jin dadi ta dau hijab dinta da hand bag suka fita, sai da ya ga ta sauka downstairs sannan ya shiga dakin Jasmine ya sameta tana bacci, tada ta yayi ta mike xaune tana kallonsa yace "Kafin in dawo ki shirya kin ji" kai ta gyada masa ya juya ya fita, ana kiran azahar ya isa gida Humainah ta fice da sauri daga motar bayan yayi parking ta nufi cikin gidan, tabe baki yayi ya bude motar ya fito yayi part din Mumy shi ma, ko minti goma cikakke bai yi gidan ba don duk hankalinsa na kan Jasmine dake gida ita kadai, Mumy na lura da shi ita dai bata ce komai ba har ya bar gidan, Humainah duk ta ji kamar ta bi sa tunawa da tayi gida xai koma. Yana isa sai da yayi sllh sannan ya shiga gidan, ya kusa minti biyar a parlor kafin ya haura sama har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude dakinta, durkushe ya ganta a dakin daure da towel alamar fitowarta daga wanka kenan, tana ganinsa tace "Captain Kaga towel din ya rike earring din, yaki ya cire" kin karasawa yayi dakin har sai da ta kuma kiransa, ya karaso ya durkusa shima ya shiga kokarin cire mata dan kunnen daga jikin tawul din, haka kawai hannunsa ke rawa ta daga ido tana kallonsa tace "Captain" bai ce komai ba ya kuma kasa cirewa, rike hannunsa tayi tace "Are you sick" bai kalleta ba bai kuma ce komai ba, hakan yasa ta cire dan kunnen gaba daya daga kunnenta, sai a snn ya daga ido yana kallonta, tace "Na cire" mikewa yayi ya fice daga dakin. Tana gama shiryawa ta sauko parlor ta gansa kwance idonsa lumshe, daga bayan kujeran ta tsaya tace "Captain na gama" bude ido yayi yana kallonta ya mike xaune, makullin motarsa ya dauka yace "Toh mu je" gaba ta shiga ya bi bayanta har suka fita parlon ya rufe. Front seat ya bude mata ta shiga sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, sai da suka dau hanya sannan tace "Captain ina xa mu?" Bai tanka ta ba hakan yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi yayi horn bakin gate aka bude gate din ya shiga yayi parking, kallonta yayi ta sunkuyar da kai, ya bude motar ya fita yace "Come down" bude motar tayi ita ma ta fito ya shiga gaba ta bi bayansa, ring din bell yayi ba a dau lokaci ba aka bude, murmushi tayi ta basu hanya tace "Sannun ku da xuwa...." Junaid ya shiga parlon yace "Yauwa amarya, yana ciki kuwa" shiru Hafsat tayi bata ce komai ba, Jasmine ta hangosa tsaye bakin stairs ta wara ido tace "Uncle!" Da gudu ta karasa cikin parlon daga Junaid har Hafsat suka bi ta da kallo, tana isa gun stairs din ta rungume sa, murmushi El-ameen yayi ya janyeta jikinsa, Hafsat ta kalli junaid da ya dauke kai, ita ma ta sunkuyar da kai, kama hannunts El-ameen yayi suka dawo parlon tace "Uncle ban san nan captain xai kawo ni ba" junaid ya fiddo waya kamar xai yi kira ya juya ya fice daga parlon, Jasmine tace "kuma Uncle yace min kayi aure da gaske ne?" Wara ido yayi yace "uhn! He's lying" ta langwabar da kai tace "Ohh captain! Why him" Juyawa tayi ta kalli Hafsat dake tsaye har lkcn bakin kofa ta matsa kusa da shi a hankali tace "Who's she?" Satan kallon Hafsat yayi yace "My sister" mikewa tayi tace "Ohk let me greet her" kafin yace komai har ta isa gun Hafsat tace "Anty ina yini?" Hafsat ta d'an yi murmushi tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Jasmine na murmushi tace "Ke sistern uncle ce koh?" Kai Hafsat ta gyada mata, El-ameen ya mike yace "Xo ki xauna in kawo maki drink ko baki so" dawowa parlon tayi tace "Ina so uncle" fridge ya nufa Hafsat kuma ta nufi kitchen, hollandia drink ya dauko mata da goran ruwa daya sai glass cup ya dawo kusa da ita ya xauna ya bude drink din ya xuba mata ya sha kadan ya bata ta wara ido ta karba tace "Thank you uncle" Hafsat ta fito daga kitchen rike da food warmers da plate a tray ta shigo parlon ta durkusa nan kusa da su tace "Ga abinci!" Jasmine ta kalli El-ameen, bude abincin Hafsat tayi ta dibar mata ta sa spoon ta mika mata, karba Jasmine tayi tace "Na gode Anty" murmushi Hafsat tayi mata ta mike ta bar wajen, Jasmine ta sauko kasa tana kallon El-ameen tace "I like her!" Murmushi yayi ya shafa kai bai ce komai ba, spoon din ta dauka ta fara cin abincin tace "Uhnn akwai dadi" El-ameen ya karbi spoon din ya debi abincin shi ma ya ci, mikewa Jasmine tayi da sauri ya kalleta yace "What?" Ta xaro ido tace "Ina captain toh?" Kofa ta nufa da sauri El-ameen ya bi ta da kallo, tana fita ta gansa xaune waje, tace "Baka shigo ba captain" mikewa yayi yana mata wani kallo yace "ina takalmin ki?" Kallon parlor tayi yace "Tafi ki dauko...." Ta marairaice tace "Are we going?" Wani mugun kallo yake mata xai yi magana El-ameen ya fito, kamar xata yi kuka tace "Uncle wai tafiya xa mu yi" El-ameen yace "A'a mu je ki ci abincin ki" juyawa tayi ta koma parlon, El-ameen ya d'aga ma junaid hannu yana murmushi yace "In xaka shigo ka shigo malam" daga haka ya koma parlon, xaunawa Junaid yayi ya dafe kansa, can ya mike ya sauka daga balcony din ya nufi motarsa ya shiga ya danna horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, Jasmine tace "Uncle ya tafi" El-ameen yace "Ci abincin ki" a hankali tace "Toh" ta ci gaba da cin abincin ta, yana nan xaune har ta gama ta mike tace "Na gama uncle ka tafi da ni gida" shiru yayi yana kallonta, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Ka ji?" Yace "Nan ba gida bane?" Bin parlon tayi da kallo a hankali tace "Gidan Captain xaka kai ni" hade rai yayi yace "ina aiki a sama sai na gama" daga haka ya haura sama ya bar ta wajen, mikewa tayi ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, ko minti biyar ba ayi da tafiyarsa sama ba, Hafsat ta sauko tace "Har kin gama" gyada mata kai tayi, Hafsat tace "Toh taho mu je sama" ba musu Jasmine ta nufi stairs suka haura sama a tare Hafsat ta shiga da ita dakinta ta nuna mata gado ta xauna, sannan ta kunna mata kallo. Har bayan la'asar Jasmine na dakin tayi rub da ciki kan gado tana kallo, Hafsat kuma na ta danne danne a laptop aka bude kofar dakin duk suka juya kallonsa, karasowa cikin dakin yayi yana kallon Jasmine yace "Kin yi sllh" gyada mata kai yayi, ya d'an saci kallon Hafsat suka hada ido ya dauke kai da sauri, Jasmine tace "Anty ce kawai ya rage tayi sallah" [3/19, 9:25 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 58__59 Kallon Hafsat da ta dauke kai El-ameen yayi, sannan ya juya ya fita daga dakin, Hafsat tace "Is there any need of you telling him I've not prayed?" Jasmine ta wara ido