Sashe 31
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
masa yayi gaba ya bar sa a wajen. Junaid ya dinga dariya ya bi bayansa, a waje suka ga yarinyar tsaye bakin motar ta, tana ganin sun fito ta nufe su, Har Junaid xai shiga mota ya tsaya, ta karasowa cikin sakin fuska tace "Am really grateful, Allah ya saka da khairan" xai yi magana yaji El-ameen ya warce ledan hannunsa ya xaga ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, Junaid ya wara ido ya bi motar da kallo, haka ma yarinyar ta bi motar da kallon mamaki, can ta maido da dubanta ga Junaid ta kirkiri murmushi kawai ta juya tace "Sai da safe" ta bar wajen, Junaid ya sauke ajiyar xuciya sai kuma ya d'aga kafada ya bi bayanta, kusan a tare suka shiga motarta, ya kalleta yace "Amm drop me plss idan ba damuwa, abokina ya tafi da motar" ta gyada masa kai tace "Alryt!" Sai da suka hau kan titi sannan tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, ta bude ido tace "Ohh it's very far, mu nan kusa muke, kaga kafin in kai ka in dawo dare xai yi kuma Mum xata min fada ne, but nevertheless bari kawai inyi driving xuwa gida idan ya so sai ka tafi da motar ko gobe sai ka maido min" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Baxa ace komai a gidanku ba" a hankali tace "I will explain everything to mum" yace "Toh nagode" cikin mintunan da basu wuce goma ba ta iso anguwarsu tayi parking kusa da gate din wani kantamemen gida ta juya tana kallonsa tace "Nan ne gidanmu" yace "Ohhk" bude motar tayi ta fito ta bude back seat ta kwashi kayanta ta rufe tana kallonsa tace "Tohm sai da safe" bude motar yayi ya fito ya dawo driver seat yace "Ohk, alryt! Tnx a lot, but sai da yamma xan maido maki motar don da safe nake fita aiki" tace "Alryt bbu damuwa" har ta fara tafiya yace "Ur Name?" Ta juyo tana kallonsa tace "Hafsat!" Ya gyada kai yace "Nyc name, am Ahmad Junaid!" Ta d'an yi murmushi ta gyada masa kai sannan ta juya ta nufi gate dinsu. Tada motar yayi yayi reverse ya bar anguwar. Sai da ya fara tsayawa gun masu saida fruits ya kuma siya ma Mumy wani fruits din sannan ya kama hanyar gida. A parking lot yyi park din motar sannan ya fito ya nufi part din Mumy, Bbu kowa parlon ya ajiye ledan fruits din ya shiga bedroom din Mumy, ya sameta kwance ya karasa ya xauna gefenta yace "Mumy na dade ko, kiyi hakuri pls ga fruits din can parlor" tace "Ohk na gode" mikewa yayi yace "In kawo maki?" Ta mike ita ma tace "A'a bar shi kawai ban jin xan iya sha kuma bari in sa a fridge" fita tayi daga dakin ya bi bayanta, ya bude bedroom din fatima ya sameta kwance tana waya Humainah kuma tayi bacci, ya karasa dakin yana kallon Humainah, murmushi yayi a xuciyarsa yace "Fitinanniya" ya juya kawai ya fita, a parlor Mumy tace "Gobe idan ka dawo gun aiki wai xaka kai Humainah gidan Aysha, wai baxa ta xauna ba" shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Toh Mumy kar Abba kuma yayi magana" tace "Ae kwana biyu kawai xata yi ka koma ka daukota" bai kuma cewa komai ba, har Mumy ta xuba fruits din cikin fridge sannan yace "Sai da safe Mumy" tace "Allah ya tashe mu lafiya, kayi addu'a kafin ka shiga" yace "In'sha Allah Mum" daga haka ya fice daga parlon. Yana gama shirin kwanciya ya jawo wayarsa ya wani hade rai yayi ma El-ameen transfer din dubu talatin da biyar ya jefar da wayar yayi kwanciyarsa. Sorry for the short Chappy sisters, I will update you guyz ltr. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 22..... Washegari da safe Junaid ya rasa yanda xai fara ce ma Mumy xai kai Humainah gidansu El-ameen kamar yanda suka shirya, har ya gama breakfast bai samu courage din gaya mata ba don yasan dole xata zargi abu, Mumy tace "Kana kallon lokaci ma kuwa" da sauri ya mike daga dinning ya dau hularsa da waya yace "Am off Mum" tace "Allah ya tsare, ka shiga gaida Abban ka?" yace "Eh but yana bacci" daga haka ya fice, Hajiya ya gani tsaye da Umma a bangaren Umman suna kallon bakon motar dake ajiye parking lot suna kus kus, duk a tunaninsu sabuwa ce, ko kallonsu bai yi ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana warming motar ya hango Khadija a balconynsu tana shara, y'afito ta yayi, ta ajiye broom din hannunta ta taho, su Umma suka bi ta da harara, gaishesa tayi, yace "akwai maganar da zamu yi dake a waya, you make sure you are alone while picking my call kin ji" tace "Alryt big bro" daga haka ya rufe motarsa, ta koma balcony. Karfe sha daya El-ameen na xaune office dinsa rike da wayarsa yana jujjuayawa da ganinsa kasan ransa a bace yake, kwafa yayi ya ajiye wayar yana tunanin walakancin da xai ma Junaid, shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya ya kasa cire hannunsa a patient din Junaid, kila don ya fara tausayin yarinyar ne, sake daukar wayar yayi ya kira Junaid for the 5th time, yanxun ma har ya gama ring bai daga ba, El-ameen ya fuzar da iska ya ajiye wayar, toh yanxu ina xae samo Wanda xai kai can gidan ta xauna da ita gashi Karfe sha biyu mama jummai xata tafi, tsaki ya ja ya jawo files din gabansa, why is he even bothering his self this much, tayi ta xama ita kadai a gidan after all ba shi ya ajiyeta ba, kwankwasa office dinsa aka yi ya daga kai yace "Come in" wata nurse ta shigo tace "Sir kana da bakuwa a waje" ya sauke kafarsa daga kan table yace "is she a patient?" Ta girgixa kai tace "I don't think so" yace "Ait, let her in" juyawa tayi ta fita ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tare da bakuwar, da sallama ta karaso tana murmushi tace "ina yini ya El-ameen" ya sauke ajiyar xuciyar relieve yace "Lafiya khadija," ta xauna saman table dinsa tace "Ya Ahmad yace in xo office in same ka" yace "Ya maki bayani ne?" Tace "Eh daga wajensa ma nake yanxu" kallon agogo yayi ya mike ya dau makullin motarsa yace "Amma Hajiya baxa ta neme ki ba?" Tace "Gidan kawata nace mata xa ni" a tare suka sauko reception, ya kalli nurses din yace "If MD shud ask of me tell him I was called for an emergency" suka amsa masa da yes sir, sannan ya fita khadija na biye da shi duk suka bi sa da kallo, front seat khadija ta bude ta shiga, shi ma ya shiga ya tada motar suka bar haraban hospital din. Sai da suka yi nisa tace "Yaya kai kuma ina ka samo mahaukaciya?" Kallonta yayi, yayi murmushi yace "Tsarin da ya maki kenan?" Ta d'an bude ido tace "Ehh ca yayi min taimakon ta kake, a hanya ka tsince ta" dariya El-ameen yayi yace "Gaskiya ne, amma ae shi ya ban kwarin gwiwan taimaka mata" khadija tace "Toh Allah ya baku lada duka" yace "Ameen," tace "Toh amma Yaya bata ma mutum komai, ni tsoro nake ji" yace "Bata komai yanxu, ta d'an saba da mutane, iyaka yanxu kawai xuwa xa kiyi ki xauna da ita, duk barnar da kika ga xata yi ki hanata, kar kuma ki bari ta fita, sai d'an potatoe da xa ki soya mata ki cika mata ketchup a ciki," a hankali khadija tace "Toh, amma ni dai ina jin tsoro" dariya yayi yace "Ke bata komai, you will like her" suna isa gidan yayi parking a waje ya fita ta bi bayansa, da ganinta kasan a tsorace take, dariya kawai yake har suka shigo parlon, bbu kowa parlon sai ita kadai ga 'yar jakar mama jummai da ta hada kaya duk ta watsar da kayan a parlon, da alamar mama jumman na kitchen, khadija ta labe jikin kofa sai faduwa gabanta yake tana leko parlon, karasowa kusa da ita El-ameen yayi ya fixge jakar yace "Ke idan baki yi barna ba baki ji dadi ba ko" daukar kayan tayi ta mika masa, ya fixge ya ajiye ya xauna ya jawo ta gabansa yace "look. I've brought a new frnd for you, hope xa ku saba da wuri, she's khadija by name" kallonsa kawai take ko kiftawa bata yi, yayi murmushi ganin yanda yayi mata maganar kamar wata me hankali, a hankali ya d'agota ya xaunar da ita gefensa ya juyar da kanta yana nuna mata khadija da taki karasowa murya can kasa yace "A frnd jewel, ur mate" kauda kanta tayi ta xamo kasa xata ci gaba da birkita kayan da take, yayi mata tsawa, da sauri ta dawo jikin kujera tana shisshigewa jiki a tsorace, sosai hakan ya ba khadija da ta kasa daina kallonta dariya, wani tausayinta ya rufeta ganin irin kyanta amma wai ba hankali, mama jummai ta fito tace "A'ah Sannu da xuwa Ahmad, har na fidda ran tafiya yanxu da naga baka xo ba" yace "Warce xata xauna da ita na je daukowa mama, kin ganta can, kanwar Junaid ce" Mama ta kalli khadija tace "Allah sarki, sannu yarinya karaso mana" yayi dariya yace "Wai tsoronta take fa" mama tace "Yo ae ita bata komai wllh" da kyar khadija ta yrda ta shigo tana kallon yarinyar da ita ma ta bi ta da ido, Mama jummai tace "Amma nan xata dinga kwana da ita koh?" El-ameen yace "A'a gaskiya xuwa bayan magrib xata koma gida" "Toh wa xai dinga kwana nan da ita" cewar mama jummai cike da mamaki, ya d'an yi shiru sannan yace "Xan dinga kwana nan ko kuma junaid" mama jummai ta girgixa kai tace "A'a wannan ba mai yiwuwa bane, ko kuma kawae in tafi da ita in dai xa ku yrda wannan ba wani abu bane a gu na" Shiru El-ameen yayi yana kallonta sai kuma yace "Saboda me baxai yiwu ba mama?" Ta xauna tace "A