Sashe 24
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 2 min read
dagota yace "Tashi ki sha magani" kara ta saki ta boye fuskarta jikin junaid tana shishshige masa kamar xata shiga jikinsa, El-Ameen ya mata wani tsawa, jikinta na rawa ta rike Junaid tana ihu, janyeta El-Ameen yayi ya hade rai yace "Keehh" cup din ya kai bakinta ta ki budewa, ya mata wani rankwashi ta kwala ihu, da sauri ya jawota ya juye maganin bakinta ya rufe hancinta, sae da ya tabbatar ta shanye su gaba daya sannan ya cire hannunsa hancinta, lkci daya duk ta amayo maganin jikinsu gaba daya su ukun, daga nan ta dinga amai gashi bata ci komai ba, El-Ameen ya mata wani tsawan da ya rikitata ta fasa ihu xata mike ya fixgota da karfi ta fado kansa ya rungumeta tsam jikinsa, sunkuyar da kai junaid yayi jin wani abu da bae taba ji ba a xuciyarsa a lkcn, a hankali ya shiga cire shirt din jikinsa da ya baci da amai, Mama jummai dake tsaye daga bakin kofa cike da tausayinta taji kamar tayi mata hawaye duk ita ma jikinta yayi sanyi, mikewa junaid yayi har lkcn bae kallesu ba ya haura sama, El-Ameen ya bi sa da kallo, a hankali ya d'ago kanta jin ta sakar masa jiki gaba daya ya ga bacci tayi, kamar me rada yace "Jewel!" A hankali ta bude ido tana kallonsa. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid*