← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 104

Sashe 85

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

so, my novel Aneesah had 112 if am not mistaken, Dr Khaleel had 120 pages also, 'ya mace kyautar Allah na goni also have the same, kuma duk an san bbu ma banxa a novels din nan, I don't write anyhow may be just once in a year, but idan nayi i will alwayz make sure it makes sense, am just in page 54 a Capt Ajay kuma nasan nan gaba xai kai har 120 ne but see what my fans are saying, you never judge a book by it cover, and am not in a haste while writing my books, ban taba novel da na dakata for weeks ba sai capt a jay, toh kullum xan dinga xuwa media ina announcement mahaifiyata bata da lafiya, ina ma nake da nutsuwar rubutu uwa ta ba lafiya yanxu haka ma bata kasar, ga kuma karatu da nake, i can't be coming to media and giving excuses everyday, all the same am grown up yanxu I won't retaliate but nagode kwarai Allah bar xumunci. in ma jan labarin nayi you don't have to be giving me hurt words, sai ka bar karantawa ka jira in kai inda kake so sai ka ci gaba Meye a ciki. Duk Allah ya baku hakuri. [3/19, 9:36 PM] El-hajj : *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ Da sauri ta sauka ta bi bayansa, junaid ya bi ta da kallo har lokacin xuciyarsa bai bar bugawa ba, da kamar ya koma part din Abdul sai kuma kawai ya bi bayanta, ji yayi gaba daya yaji haushin kansa, ya ja tsaki ya ci gaba da tafiya kamar bai son yi, tsaye Zahrah taga El-ameen da wasu dogarawa suna hira, ta kasa karasawa gun, juyawa yayi suna hada ido ya sakar mata murmushi, kasa mayar masa tayi, yace "ban san hanya ba, I've to wait for you....." Karasowa tayi da kyar ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, bai bari suka hada ido da junaid dake tahowa ba ya daga ma dogarawan hannu ya bi bayanta, tafiya kawai take amma ji take kamar xata harde ta fadi kasa, duk yana lura da ita hakan yasa ya karasa suka jera da ita yace "Masarautan nan naku da girma sosai" ta gefen ido ta kallesa tace "Yyeah!" Rasa abun cewa yayi shi ma can kuma yace "But kin gama sec sch kuwa?" Shiru tayi sai kuma ta gyada masa kai tace "Ehh!" Yace "Dat's good" junaid dai na biye da su a baya, wata hanya daban ta dauka suka haura bene sannan ta bude wata babban kofa ta juya tana kallonsu, suna hada ido da El-ameen ta sauke idonta kasa ta ci gaba da tafiya, tsarin gun kamar na Kilishi da suka baro, babu kowa babban parlon sai jakadiya da wata me goge goge, Ta nuna masu kujera, jakadiya ta bi ta da kirari kafin tayi masu sannu da xuwa, El-ameen ne kadai ya amsa mata yana murmushi, Bedroom din Umma Zahrah ta nufa ba a dau lokaci ba sai ga ta sun fito da Umman, murmushi ne shimfide fuskarta har ta karaso parlon tana kallonsu gaba daya tace "Sannun ku da xuwa...." Sakkowa El-ameen yayi har kasa Junaid ya bi sa da ido kafin shima yayi kasa da kansa ya sauka, suka gaisheta gaba daya, tana murmushi har lokacin ta amsa, tuni jakadiya ta cike gabansu da kayan marmari da shaye shaye, Umma tace "To waye Ahmad waye takwaran mai martaba" El-ameen yayi murmushi yace "Ni ne El-ameen...." Ta kalli junaid cikin sanyin murya tace "Kai ne Ahmad kenan" kai ya gyada mata ba tare da ya dago ba, a sanyaye tace "Allah ya albarkaci rayuwar ku, yasa ku gama da iyayen ku da duniya lafiya....." El-ameen yayi saurin cewa "Ameen Umma mun gode" Umma ta kalli Zahrah tace "Kin kai su gun Kilishi?" Ta gyada kai tace "Can muka fara xuwa" Umma tace "To Maa sha Allah" ba su wani dade part din Umma ba ta dalilin bakin da tayi, Zahrah ta nufi fada gun Abbanta da su, sai dai wannan karan sauri kawai take bata bari sun jera da El-ameen din ba, bai takurata ba ya jira junaid, junaid na isa gunsa yace "ya kuma ku ka raba tafiyar?" Murmushi yyi yace "Yea hakan yafi don ni ba runguma bane iyakar abinda zan mata idan na kasa jure shariyarta gare ni" Wani kallo Junaid ke yi masa kafin yace komai El-ameen yayi dariya yayi gaba ya bar sa nan, suna shiga fada ta juya ta bar su tare da Abbanta. Da rana Umma ta takurata ta kai masu lunch tace ai masu aiki xa su kai masu, Mikewa tayi d'aga karshe dai ta fita nemo Ummi ta rakata. Sae da suka fara xuwa kitchen don tabbatar da cewar an kai abincin taga an kai, fura ta tarar ana damawa kitchen din, ta dau babban jug ta diba snn ta dau tray ta daura kai da cups ta fita tare da Ummi, suna isa part din Abdul Ummi ce ta fara shiga da sallama kafin ita, Junaid ne kwance parlon yana danna waya, yayi masu kallo daya ya dauke kai, Ummi ta xauna tana kallonsa ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ajiye trayn hannunta Zahrah tayi ta nufi bedroom ba tare da ta kallesa ba, El-ameen ta gani da Abdul suna kallo ga cake gabansu, El-ameen ya buda ido murya can kasa yace "princess!" Tace "Uhm, kun yi lunch?" Hararata Abdul yayi yace "Basu yi ba" 'yar dariya tayi ta kalli El-ameen dake kallonta, can ta karasa ciki ta xauna kusa da Abdul ta kai bakinta kusa da kunnensa kamar me rada tace "Why is he alone?" Abdul ya kalleta yace "Ahmad?" Satan kallon El-ameen tayi sai kuma ta dauke kai da sauri, Abdul yace "He said he's more comfortable there" da sauri tace "Alryt, ohk" sai kuma ta kalli El-ameen tace "Ga fura na kawo maku fa" ba tare da ya kalleta ba yace "Toh mun gode" mikewa tayi ta fita daga bedroom din, xaune ta samu Ummi har lokacin idonta na kan Junaid, "ki tashi mu je" ta fadi haka bayan ta dauke kai daga kallonta, shi dai idonsa na kan waya, Ummi ta mike tace "Ohk furan xa a xuba masu ne?" Da sauri Zahrah tace "Noo!" Sai kuma ta nufi tray din da ta dire daga gefensa ta durkusa ta dau cups din ta xuba furan ciki ta ajiye tana kallonsa fuskarta daure, kara wayarsa yayi a kunne ya mike xaune ya sakko da fararen kafafuwansa kasa kamar wanda aka tilasta yayi magana yace "kina ji na?" Kasa daina kallonsa Zahrah tayi, ya shafa kansa yace "Have you eaten?" Shiru ya d'an yi kafin yace "Ki dai daure ki ci, I will call back later" daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar lokaci daya ya sauke idonsa kan Zahrah dake kallonsa har lokacin, da sauri ta dauke Kai ta mike ta nufi kofa ta fice, har dare bata kuma komawa part din Abdul ba, duk ta rasa me ke mata dadi mugun haushin Junaid kawai take ji, har shi xae nuna mata ji da kai? mikewa tayi daga karshe ta fice ta nufi bangaren Abdul, El-ameen da Junaid ne parlon wannan karan, kmr daxu kwance Junaid yake waya na kare a kunnensa, Bata ko kalli inda yake ba ta karasa gun El-ameen dake kallon wani movie ta xauna kusa da shi tayi fari da ido tace "Are you okay? Bbu damuwa koh" Yana kallonta yace "Yea, am just missing home" murmushi tayi tace "Nan ma fa gida ne" yace "Yeah haka ne" ta mike tace "Ina son ka rakani mu je garden" yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "Yeah, I want you to keep me company" mikewa yayi yace "Alryt mu je," duk da wayar da ke kare kunnen junaid gaba daya ya mance waya yake, ba kallon direction dinsu yake ba amma gaba daya hankalinsa na kansu, kofa ta nufa El-ameen ya kalli junaid da yayi saurin dafa wayar kunnensa yace "Will be ryt back" ko kallonsa Junaid bai yi ba har ya fita, ya mike xaune, ji yayi xuciyarsa na tafarfasa kawai, ya kusa minti ashirin xaune har Abdul ya shigo, ko da ya tambayesa El-ameen cewa yayi bai sani ba, yana shiga bedroom ya mike ya fice daga part din gaba daya, ji yayi da ma safiya ce ko rana da babu abinda xai hanasa komawa katsina duk da sarki ne ya tsaida su amma da tuni sun tafi da yamma, can wani waje da bbu hayaniya kuma babu wani haske ya samu ya xauna, har sha biyun dare bai da niyar tashi ya shiga ciki, gaba daya El-ameen yayi tunanin wucewa junaid yayi don yasan halinsa barin ma Atm card dinsa na jikinsa, Abdul da mamaki ya cikasa yace "Why is he acting that way?" El-ameen yace "That's he's hobby" Abdul bai san lokacin da ya fashe da dariya ba, El-ameen yace "Yeah, an only son, mumy's pet" Zahrah dake tsaye ta tabe baki ta juya ta fita daga parlon sai dai duk jikinta yayi sanyi, kasa komawa part dinta tayi hakan yasa ta bi hanyar da tasan baxa a ganta ba ta fita waje, tafiya kawai take ba don tasan ina ma xata ba kuma meye ta fito yi, bata yi wani nisa da tafiyan ba tayi ido hudu da shi har lokacin yana xaune ya xuba ma taurari ido kamar me kirgan su, rasa abinda xata yi tayi a lokacin, ci gaba da tafiya xata yi ko juyawa xata yi ta koma, Dakewa tayi ta tsaya inda take, can ta karaso fuskar nan nata daure tana kallonsa tace "Don me xaka wani fito nan cikin dare ka ba mutum wahalan nemanka when I am suppose to be in bed" wani kallo ya watsa mata ta gefen ido ya ci gaba da kallon sky abun sa, fixge wayar hannunsa tayi tace "Malam magana nake maka fah?" Sai a sannan ya kuma kallonta suka yi ido hudu gabanta ne ya fadi sosai, ya mike ya warce wayarsa yace "Gadina aka baki ne?" Wani kallo tayi masa tace "Ehh sbda ta dalilina ka xo garin nan....." Shiru tayi sai kuma ta
Chapter 85 · 0% Book details