← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 104

Sashe 81

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

fah" Kilishi ta kalleta tace "Mai martaba ne yace tare xa ku" bata fuska tayi tace "Yanxu xanje in gaya masa, Mumy bana son ta kara tafiya ita kadai ne...." Kilishi tayi murmushi tace "Toh Allah yasa ya amince" daga haka Ummi ta kama hannun 'yar uwar tata suka fita, basu sha wahalan shawo kan Abbansu ba ya amince xa ta bi su, motoci biyar ne xa a tafi katsinan da, mai martaba kuma flight xai bi da Zahrah da El-ameen da Ummi, Abdul kuma xae bi tawagar Abbansa ta mota sai su hade a masarautan kano daga can kuma su dau hanyar katsina. Karfe daya motocin tawagar sarki El-ameen suka iso masarautan Kano, ko minti talatin basu kara a Kano ba suka dau hanyar katsina, Zahrah da Ummi suka shiga mota daya da Mahaifinsu, El-ameen bai yarda ya shiga motar sarki da ya sa masa takwara ba ya hau motar gaba, uku da wani abu suka shiga garin kt, duk da El-ameen ya san ba lallai junaid na gidansu ba, can ya sa suka nufa gaba daya, hudu da minti goma suka iso kofar gidansu Junaid, El-ameen ne ya fara fitowa, sannan dogarawan sarki, kafin sarki ma ya fito tare da aminansa, Sarki na kallon El-ameen yace "Masallaci mafi kusa, xa muyi la'asar!" Masallacin kofar gidan ya shiga da su bayan sun daura alwala, su Zahrah dai na mota a xaune, hudu da minti ashirin duk suka fiffito daga mosque din, Sarki yace "Shiga kayi mana sallama da masu gidan, El-ameen ya shiga compound din, bbu kowa tsakar gidan sai Khadija dake xaune balcony din Mumy, ya karasa har inda take, ta gaishesa da fara'ar yake, amsa kafin yace "junaid fa?" Ta girgixa kai tace "yana can gidansa!" Yace "Abba fah?" Ta kalli bangaren Abba tace "Yana ciki, amma yana da baki" El-ameen yace "Su waye?" Tace "Hajja na ciki, kawu Abbakar ma na ciki sai Abokansa biyu" ya d'an bude ido yace "Meeting din me ake" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Junaid koh?" Gyada masa kai tayi, yace "Su Hajiya fah?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Mumy fa?" Kallon kofar parlon tayi tace "Tana ciki" yace "Ohk pls ki gaya min taron me ake a parlon" ta tabe baki tace "Humainah ce ta gaya ma Hajja abinda ya sa ya saketa daxu da safe" El-ameen ya d'an bude ido yace "Ta basu labarin mahaukaciya kenan" gyada masa kai Khadija tayi, El-ameen yace "Toh me Abba yace?" Hawaye ya cika idonta taki cewa komai, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh bai xo ba junaid din" hawaye na sakko mata tace "Tun daxu ake kiransa ya ki ya xo" El-ameen bai kuma cewa komai ba ya nufi parlon Mumy, xaune ya ganta da ganinta ba karamin kuka ta ci ba, kasa karasawa yayi cikin parlon ya juya ya fita kawai, kofar gida ya koma ya ba sarki hakuri sannan ya ce su shigo, Fitowa Zahrah tayi da 'yar uwarta suna daga gefen mahaifinsu suka shiga gidan, har parlon Abba yayi musu iso, tuni Khadija ta mike tana kallon ikon Allah ganin jama'ar dake shigowa gidan, El-ameen ne ya fara shiga parlon da sallama ya gaida Abba da ladabi, Hajja tace "Alhmdllh kun ga babban munafukin abokin nasa nan, ae wllh sai Allah ya mana hisabi da ku...." El-ameen bai ko kalleta ba yana kallon Abba yace "Abba baki kayi daga masarautan Bauchi, mai martaba sarkin bauchi ne da kansa" Abba da ya wani xaro ido tun kan yace komai Sarki El-ameen ya shigo parlon da sallama Aminansa biyu da Zahrah da Ummi ma suka shigo sai Abdul sauran dogarawan sarki suka yi cirko cirko bakin kofa, da farko tsaye sarkin yayi ganin yanda ake kallonsa da mamaki barin Abba ya sa shi samun kujera ya xauna, parking Junaid yayi kofar gida ya tsura ma manyan motocin dake Parke a jere ido, mamaki ne ya cika sa sosai lokaci daya yaji gabansa ya fadi ya bude motar ya fita da sauri ya shiga cikin gidan, uniform ne jikinsa sai hula dake kansa, ko lura da dogarawan da suka cika compound din bai yi ba, shi dai burinsa ya ga Mumynsa, hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya ga jerin takalma dake kofar parlon Abba, da part din Mumy xa shi kawai ya fasa ya nufi parlon Abba da sauri ya shiga. *Haske writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 76...... Tsaye yayi bakin kofa yana bin kowa na parlon da kallo irin na mamaki, ido hudu suka yi da Zahrah dake kallonsa ko kiftawa babu, hade rai yayi ya juya xai fita El-ameen dake tsaye har lokacin ya kama hannunsa yana kallon Sarki da shi kansa kallon Junaid yake yace "Ahmad junaid kenan, kuma dominsa ku ka taho katsina." Mikewa Hajja tayi da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Me yayi? Yaron da ko hanyar bauchi na san ko xa a kashe sa bai sani ba, ashe kai mugu ne Aminu ba mu sani ba..... Meye hadin jikana da masarautar Bauchi can kace ko ina?" Abokin Abba ne yace "A'a Hajja ba tashin hankali bane, ae ba mu jira mun ji me ke tafe da su ba, kuma ko gaisawa fa ba a yi ba, sannan ance sarki ne nan gabanmu ba fa waxiri ba....." Wani kallo ta watsa masa A fusace tace "Yo ni ina ruwana da sarautarsa, ka gan ni nan ban tsoron kowa sai Allah, kuma bbu irin fitintinun da ban gani ba a duniya, ya fadi me jikana yayi masa in ji, Ahmad da ko titin da xai kai sa Bauchi bai sani ba" Abba dai kasa cewa komai yayi, don shima jiran jin me only son din nasa yayi kawai yake, Sarki kam banda murmushi babu abinda yake sai dai ba lallai ka gane murmushin ma yake ba sbda turban din kansa, Aminin sa da shi ma ya samu gu ya xauna gefensa cikin kaushin murya yace "Mind you all, ba fa karamin mutum bane xaune a gaban ku, sannan mu alkhairi ne ya kawo mu in'sha Allah, Mai martaba sarkin bauchi kenan da kansa don haka a samu nutsuwa don Allah....." Hajja tace "Ina xa mu samu nutsuwa ba ku fadi me ke tafe da ku ba, ni dai nasan Ahmad ko cinnaka baxae iya kashe wa ba...." Sarki ya kalli Junaid yace "Toh karaso ka xauna Ahmad" tsaye junaid yayi kamar baxai karasa parlon ba gashi gabansa sae faduwa yake ya rasa dalili, sarkin bauchi kuma, is she related to the royal family? Abba ne yace "Ka kasa tahowa ke nan?" Da kyar ya d'aga kafa ya karaso ya xauna nan tsakar parlon Hajja ta xauna gefensa tace "Kwantar da hankalin ka Amadi bbu wanda ya isa ya cutar da kai matukar ina raye a doron kasa, su fadi me kayi in ji" tana magana ne tana matsar kwalla, Abba ya kalli El-ameen yace "Tafi ka kira Amina" juyawa yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo parlon tare da Mumy, k'in xama Mumy tayi ta kalli junaid ta kalli Sarki sannan Abba, Sarki ya kalli Zahrah da ke xaune daga kasa kusa da shi, sannan ya kalli Junaid yace "Kasan yarinyar nan?" Junaid ya daga kai yana kallon kwayar idonta, Sunkuyar da kai tayi da sauri ta dalilin faduwa da gabanta yayi, sai da sarkin ya kuma nanata tambayar sannan ya gyada kai kawai, Hajja da ko k'adan bata gane Zahrah ba ta yo waje da ido tace "A ina ka santa don ubanka?" Kallonsa kawai sarkin ke yi, a ransa kuwa tunani yake anya shi din El-ameen ya basa labari jiya, da irin fadin ran nan ya taimaki 'yar sa kenan, A fili kuwa cewa yayi "Toh a ina ka santa Ahmad?" Kallon El-ameen Junaid yayi yace "Shi ma ai ya santa, ya ma fi ni saninta" Hajja ta mike tace "Atoh a hankali gaskiya dai xata bayyana don ni nasan jikana bai santa ba sai dai abokinsa" Aminin sarki ne yace "Ahmad kake koh? Toh kasani ba karamin mutum bane nan gaban ka, am repeating this, you go straight to the point and answer his questions right away, takanas ya taso tun daga bauchi domin ka don haka kar ka maida mu kananan mutane" Mumy ji tayi ta kasa tsayuwar ma, da kyar ta samu waje ta xauna tana kallon ikon Allah, Junaid kam dama ba direction dinsu yake kallo ba, Sarki ya nisa yace "Ahmad, ni ne Mahaifin Zahrah, ka kuma min abinda har karshen rayuwata baxan taba mancewa da kai ba, ka dawo min da farin cikina ka fitar da ni kunci lokaci daya, ashe har yanxu akwai sauran mutanen kirki a duniya? ashe akwai masu xuciya irin taka a duniya, kaf rayuwata ban taba jin na kaunaci mutum kamar yanda naji kaunar ka daga jiya ba, da kai na kwana a raina jiya Ahmad....." Hajja sai wuwwulla ido take tana jiran jin me yayi ma sarkin, Sarki yace "Xan so ka ban labarin yanda ka ga Zahrah har ixuwa jiya Ahmad" k'in dagowa Junaid yayi da farko can ya dago suka hada ido da sarkin sai yaga yayi masa kwarjini, da kyar ya iya cewa "Nayi xaton El-ameen ya fadi maku ranka shi dade" Sarki yayi murmushi yace "Ehh, amma xan so sake jin labarin daga bakin ka" Junaid ya shafa kansa ya kalli Abba dake kallonsa, sannan ya dauke kai, xaunawa Hajja tayi tana jiran jin labari ita ma, Kamar baxae ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace "It all happened on a faithful tuesday evening....." Lumshe ido yayi ya bude ya shiga ga bada labarin tun daga ranan da ya fara ganin Zahrah a gefen titi, bbu abinda ya canxa daga wanda El-ameen ya fadi ma sarkin jiya, yanda ya kama mata gida da farko daga karshe kuma suka koma gidan El-ameen, irin hidima da wahalhalun da suka yi shi da El-ameen a kanta, da yanda suka boye ma iyayensu, mama jummai da suka dauko.... kai bbu abinda ya boye har gida da ya kawota da nufin aurenta da yanda iyayensa suka gane ba mai hankali bace..... Bbu wanda jikinsa bai yi sanyi ba a parlon, Hajja ta rushe
Chapter 81 · 0% Book details