← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 104

Sashe 40

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

hijab dinta ya sa mata suka fita xuwa gun motarsa yasa ta shiga ya tada mota yyi warming ya bar haraban hospital din. Hotel ya nufa da ita don dat was the only option a lokacin, yana parking a haraban hotel din kiran Junaid ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kiran don yasan bai xuwa can gidan da safe bare ace yaje ne ya gani a rufe, ya kalli agogo yaga bakwai da wani abu, daga kiran yayi daga daya bangaren Junaid yace "I saw ur text jiya, kuma I hail you da ka nuna kai babba ne" El-ameen yace "what's he talking about" Junaid yace "Really! There's no need of pretending, kana ina yanxu" El-ameen ya kalli inda yake sannan ya gaya masa, Junaid yace "Me kake a hotel" El-ameen yayi shiru sannan yace "Why are you even asking?" Junaid yace "Magana xa muyi, shud I come over..." El-ameen yace "aikin fa?" Junaid yace "Na dau hutun sati daya..." El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Good! Taho ka same ni yanxu" daga haka ya katse wayar, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya dafe kansa don maganar da faisal yayi masa jiya ya tsaya masa, so yake yaji mai El-ameen xai ce game da shawaran faisal, in har shima ya basa go ahead xai jaraba ya ga ko me yiwuwa ne. *Haske writers association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 30..... Bude motar El-ameen yayi ya fito ya xaga ya fiddota yana rike da hannunta suka shiga reception din hotel din, babu wanda xai ganta yace mahaukaciya ce, xa a fi tunanin daga kauye ta fito duba da yanda take kalle kalle kamar idonta xai fito, tana kuma shisshige sa, daki yyi masu book aka basa makulli ya haura sama yana rike da hannunta, xaunar da ita yayi a dakin yana kallonta, tausayinta kawai yake a hankali yace "Allah ya baki lafiya jewel" ta dawo kusa da shi tana kallonsa, wayarsa ne ya soma ring ya dauka ganin Junaid ne ya d'aga ya gaya masa numbern room din da yake, cikin few minutes Junaid ya iso dakin ya murda kofa ya shigo, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonsu da mamaki, El-ameen ya mike ya d'aga kafada yace "Ummi ta kusa gano abinda muke, so I had to take her away daga gidana" Junaid ya xaro ido yace "Da gaske?" El-ameen ya koma ya xauna yace "nafi tunanin gulma aka kai mata, nd I suspect that khadija" junaid ya girgixa kai yace "No! Khadija baxa taba exposing dinmu ba, kila dai kanwarka ce sumayya..." Kallonsa El-ameen ya tsaya yi yace "Sumayya kuma? Ae bata san komai ba" tabe baki Junaid yayi ya karaso dakin yana kallon Jasmine da ita ma idonta ke kansa, ya juya ya kalli El-ameen yace "Nan ku ka kwana kenan" El-ameen ya girgixa kai yace "Clinic, nd you know what sai da ta tona min asiri ta sa Abba ya ganta and he wasn't happy" Junaid bai ce komai ba ya xauna gefen gadon dakin, ta mike a hankali ta dawo kusa da shi ta tsaya tana kallonsa, ya d'an bude ido yana kallonta shima yace "Good morning!" El-ameen da ke kallonsu ya dauke kai yace "I heard you are taking her to Ogun state" Junaid yace "Yea but na canxa plan yanxu" El-ameen ya kallesa yace "To Which?" Junaid ya rufe ido na kusan second ashirin sannan ya bude a hankali yace "Faisal ya bani shawaran in aureta kawae, you know gidanmu an takura in fito da mata nan da few weeks, but kaga frnd ban san yarinyar nan ba, ban san daga inda ta fito ba, ban san meye sanadin haukatan ta ba, infact ban ma san ko matar aure bace, kana ganin shawaran faisal yayi, ya bani good reasons da yasa yace in aureta but am not even sure it will be possible ba lallai 'yan gidanmu su yarda ba" tunda ya fara magana El-ameen ke kallonsa ko kiftawa bai yi, Junaid ya kallesa jin bai ce komai ba yace "You are quite" El-ameen yayi saurin lumshe ido tara da yin wani murmushin da xa a iya kiransa da na karfin hali yace "Yea shawara ce mai kyau, may be xa a fi samun nutsuwa gun nema mata lafiya babu fargaba...." A hankali Junaid yace "Toh how xan kai ta gida a matsayin warce xan aura a haukace, kuma sai in ce ina iyayenta?" El-ameen yace "Ai tana da nutsuwa, shiryata kawai xa ayi ka hada ta da budurwa kamarta irin ace kawarta din nan ku je tare, bai fi kuyi xaman ten minutes ba ku fito just dat ka tabbatar kana kusa da ita kar ka bar wajen, matsalar da xa a samu a nan shine baxata yi magana ba but wannan ba komai bane Kawar sai tayi mata xa ayi tunanin kunya ne da ita, kuma ai gun Mumy kadai xaka kaita komai xai xo da sauki, iyaye kuma ba matsala bane xa mu san yanda xa muyi...." shiru El-ameen yayi xuciyarsa na bugawa ya rasa dalili, Junaid yace "Uhunn will this be possible kuwa?" El-ameen ya kallesa ya dan yi murmushi yace "idan Allah ya yarda" junaid ya lumshe ido yace "Toh Allah ya sa, idan Allah ya bata lafiya sai in sauwake mata ta nemi 'yan uwanta" kallonsa El-ameen yayi da sauri sai dai bai ce komai ba, Junaid yace "Toh ita mama dake kula da ita ina ka kaita?" El-ameen yace "Na sallameta" Junaid ya kallesa da sauri yace "ohh Why?" El-ameen yace "I had to, don Ummi ta tura a duba gidan" junaid ya girgixa kai yace "Toh yanxu ya za ayi da ita a nan?" El-ameen yace "I don't know" Junaid yace "Ka kira wannan nurse din na ranan mana" ba musu El-ameen ya fiddo wayarsa bayan sun gaisa ya gaya mata dalilin da ya kirata ya kuma gaya mata inda xata samesa, kafin awa daya ta iso gun, El-ameen yace "Ga kayanta nan xaki shiryata, you will be staying with her na 2 dayz plss..." Nurse din tace "But sir ina da duty a asibiti da daddare" kallon junaid El-Ameen yayi, jin bai ce komai ba yace "Ohk xa mu san yanda xa ayi xuwa ltr" Daga haka ya mike yace ma junaid xai tafi gida, Junaid yace "But am also leaving" kudi ya ciro a aljihunsa ya mika ma nurse din yace "Gashi ki siya maku abinda xa ku ci kar ki kuma bar ta ita kadai a daki" shi dai El-ameen fita kawai yayi, junaid ya bi bayansa, tana ganin haka ta mike da sauri xata bi su a rikice amma tuni suka rufe kofar, nurse din ta kamo hannunta sanin bata komai ta ja ta suka koma dakin. Umma ce xaune tare da Hajiya a parlon hajiyar, da ganinsu kasan abun duniya ya dame su, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah shi kyauta, amma ita suhaima don uwarta bata tabbatar da abu ba xata xo ta fadi yanxu da ta xo gidan nan ya xa muyi, ga shi matar nan ba mutunci ne da ita ba, mu dai Allah bai yiwo mu masu sa'a ba kila" Hajiya tace "Ae ni naji dadi da abun ya tsaya iya waya balki, sai kin ji maganganun da ta gayan wllh, wai in cire ido kan d'anta, maganganu dai bbu dadin ji, sai dai ban to fa ba don mu muka ja ma kanmu, uhum Allah shi kyauta dai, duk Suhaima ce ta ja mana" Umma tace "Xai kuma iya yiwuwa fa kawai rufa ma d'an nata da junaid din asiri tayi, wannan tattaccen d'an nata, kinsan kuma fa bakinsu daya da Amina" Hajiya tace "Ni wllh duk abun ya ishe ni, duk inda muka billo ba nasara wannan wace irin fitina ce, gashi ni gabana kullum cikin faduwa yake kar yace tsinannar Humainan nan yake so, kai ni na tabbata ma ita uwar xata ce ya fito da, kinga fa 'yan kwanaki suka rage wllh duk hankalina a tashe yake" Umma tayi tagumi tace "ga dukkan alama uwar nan tasa ba a xaune take ba ita ma abinda muke shi take yi, baki ga yau tun safe ta fita ba, ita da bata xuwa ko ina" Umma tace "Toh ke sai yau kika sani, ni ai tun ba yau ba nasan ita ma a tsaye take, bar ganinta haka green snake under the green grass ce wllh, amma dai akwai wani plan din da nake ta shiryawa a raina sai dai wllh ni kaina tsoronsa nake, amma hakan kadai shine mafita ba boka ba malam cikin kwanciyar hankali, sae dai kuma plan din na bukatan hadin kan mu ne, bbu bakin ciki ko nuna banbanci bare kyashi in suhaiman inma muhibbar" Hajiya tace "Haba balki, Ae mun xama daya wllh kawai gaya min wani plan ne wannan" shigowar motar junaid suka ji ko wannen su tayi shiru tana tabe baki, Umma tayi kwafa tace "ka kusa shigowa hannu yaro" Junaid na gama parking ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlorn jin ana soye soye kitchen ya nufi kitchen din, Humainah ce kitchen din tana suyan nama, tana ganinsa ta hade rai ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, karasowa kitchen din yayi ya rungume hannayensa yace "Fitsara kika koyo gidan Ayshan kenan?" Daure fuska tayi sosai ta kashe gas din ta rufe naman da ta soya ta juya xata fita ya fixgota ta fado jikinsa, 'yar kara tayi ya Rungumeta yana kallonta, tuni jikinta ya dau rawa ta fara turasa tana cewa "Meye haka ya Ahmad ka sake ni..." D'ago kanta yay i ta kasa kallon fuskarsa sai kokarin kwace kanta take, yayi murmushi murya can kasa yace "Ba fitsara ba!" Ta girgixa kai da sauri ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "don Allah kayi hakuri ban gane kai bane, baxan kara ba" Muryar fatima da ya ji yasa ya saketa da sauri, ko second uku bata kara ba ta fice daga kitchen din tana tuntube, juyawa yayi shi ma ya fita yana mamakin hakan da yayi don bai taba shigen haka ba, mumynsa kadai yake runguma a rayuwarsa. Karfe hudu da wani abu yana kwance part dinsa kiran El-ameen ya shigo wayarsa, ya d'aga daga
Chapter 40 · 0% Book details