Sashe 102
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya kare course din ya dawo gida Nigeria, washegarin ranan da ya dira yayi deciding ya je gun amininsa abokinsa kuma d'an uwansa...." Kallonsa kawai Zahrah take, ya shafa fuskarta yace "are you there?" Ta gyada kasa kai, ya lumshe ido yace "Yana driving a hanya ya ga wani taro me yawa, a tunaninsa hatsari aka yi, kawai yayi deciding ya tsaya ya bada nasa taimakon... Yana fitowa ya shiga taron kin san abinda ya gani?" Boye fuskarta tayi a kirjinsa, ya dago kan yace "Are you there princess?" Ji yayi ta fashe da kuka, ya mike xaune da sauri ya dagota yace "Jasmine!" Ta kuma fashewa da wani kukan, jikinsa yyi sanyi lokaci daya, rungumeta yyi yace "Ohh I am sorry plss tunda ba ki so, sorry plss Princess na daina" lamo tayi jikinsa, a hankali yace "I didn't mean to hurt you" suna nn a haka har yaji alamun tayi bacci ya lumshe ido ya daura fuskarsa kam gashinta da ya cikasa da kamshi. Washegari da asuba kafin ya dawo daga Masallaci ta fita ta koma dakinta, yana dawowa dakin Humainah ya shiga ya tarda kwance ya karasa ya xauna kan gadon yace "Sallah fah?" Tace "Nayi" yace "Ohk Gud morning" mikewa xaune tayi tace "Ina kwana!" Yayi murmushi yace "Kin tashi lafiya" komawa tayi ta kwanta tace "Yeah" yace "to babyn fah" bata ce masa komai ba hakan yasa ya mike ya fita. Bakwai da minti goma ya sauka downstairs bayan yayi shirin fita aiki, kallo daya Zahrah da ta gama ajiye kayan breakfast kan dining tayi masa ta dauke kai, ya isa kusa da ita ya tsaya, ta gefen ido ta kallesa tace "Good morning" ya rungume hannayensa yana kallonta jin bai amsa ba ta juyo tana kallonsa ita ma, karasawa tayi gabansa ta langwabar da kai cikin sanyin murya tace "Gud morning" bai amsa ba still sai kallonta da yake, can ya kamo hannunta ta fixge tayi masa buttoning masa button din karshe na farin uniform din jikinsa ta kara gaba. Da yamma yana parlor xaune bayan ya dawo daga aiki su kuma suna kitchen aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, El-ameen ne tsaye daga gefensa kuma Dr Sumayya, El-ameen ya wara ido yace "ko mu koma" Junaid yayi murmushi yana kallon Dr sumayya ya bata hanya yace "Sannu da xuwa Dr, bismillah" murmushin ta mayar masa ta shiga parlon tace "Yauwa Captain ina daughter nah" yace "Uhm tana ciki bari in kirata" daga haka ya nufi kitchen, xama tayi parlor El-ameen ma ya xauna tace "Allah sarki rayuwa, kamar ba ayi ba yanxu koh?" Murmushi kawai El-ameen yayi, tace "Allah ya baku lada gaba daya.... Amma na so ace kai ka sameta ba wnn Capt mara son son jama'a ba" Junaid na shiga kitchen ya kamo hannun Zahrah dake tsaye Humainah kuma na ta aikin, yace "You know what princess, xaku gaisa da bakuwa yanxu, ta taimake ki ita ma sosai lkcn da baki da lafiya, you stayed with her for 3 month ta kuma kula dake sosai, she's Dr sumayya by name, tare suka xo da El-ameen" kallonsa kawai Zahrah take yayi murmushi yace "Yeah princess," juyawa yayi ya kalli Humainah dake ta harkan gabanta yace "Wife ki kawo masu drink pls" daga haka ya kama hannu Zahrah suka fita, kallonta kawai Zahrah take kamar yanda ita ma Dr Sumayyar ke kallonta har suka karaso parlon, Dr Sumayya ta mike tana murmushi ta bude mata hannunta, karasa Zahrah tayi ta shige jikinta, Dr Sumayya tace "Am happy you are back my baby.... Alhmdulillah, am happy for you baby" Zahrah ta rufe idonta da ya cika da hawaye Dr Sumayya ta janyeta jikinta tana kallonta cike da tausayinta. Su El-ameen na barin gidan bayan magrib Junaid ya shiga dakin Zahrah bai yi mamakin ganinta a sanyaye ba ya xauna kusa da ita ya kamo hannunta yace "Yeah you owe a lot to her, after you loosed ur memory ita ta rike ta kuma dinga nuna maki abubuwa, komawarsu abroad yasa kika dawo gidana,then baki ma son rabuwa da ita you were crying xa ki bita" kallonsa kawae Zahrah take, yayi murmushi ya lakaci hancinta yace "Yess princess..." Danna bell da aka yi downstairs ya sa ya kalli bakin kofa can yayi peck din cheek dinta ya mike yace "Am coming princess" daga haka ya fita ya sauka kasa, yana bude kofar yayi still yana kallon wa enda ke tsaye bakin kofar, Hajiya ce ta kirkiri murmushi tace "Ahmad, ina yini" bai amsa ba sai kallonta da yake, Umma dai sai wurga ido take, Hajiya tayi karfin halin bin ta gefensa ta shiga parlon sai a snn ya juya ya bar bakin kofar ya koma parlor, Umma ma ta shigo duk suka karasa parlon kamar masu tsoron taka tiles din parlon, xaman sa yyi parlor suma suka shigo suka xaxxauna, Umma tace "Sannu Ahmad ina yini ya aiki" sai a snn ya kallesu, can yyi kasa da kai yace "Sannun ku da xuwa" washe baki Hajiya tayi tace "Sannu Ahmad, ya iyali" yace "Alhmdllh" daga haka ya mike ya wuce sama, bin sa da kallo suka duk jiki yayi sanyi, dakin Humainah ya shiga ya ga tana bayi, ya fita ya koma dakin Zahrah tana nn yanda ya barta ya xauna kusa da ita ta kallesa tace "Waye?" Hannunta ya kama yace "My step mothers" d'an bude ido tayi tace "You have them?" Murmushi yayi ya daura goshinsa kan nata yana rike da hannunta yace "Yeah, and they don't like me" tace "Why?" Ya girgixa Kai yace "tafi ki kai masu ruwa" ba musu ta mike ta fita, tunanin abinda xai kawo su gidansa ya shiga yi, can ya mike ya koma dakin Humainah tana xaune gaban mirror yace "Ki tafi ki gaida su Hajiya" tana kallonsa ta madubi tace "Wace Hajiya" yace "warce kika sa ni mana" daga haka ya fita, ta kusa minti biyar tana naxari kafin ta mike ta sa hijab ta fita. Kasa karasawa parlon tayi yanda suke kallonta haka ita ma take kallonsu, Zahrah dai na xaune kasa bayan ta kawo masu ruwa har da abinci, can Humainah ta karasa ta xauna ita ma kasa tana kirkiran murmushi tace "sannun ku da xuwa" amsa ta suka yi ko Wanne na murmushin dole, bata kuma cewa komai ba can dai ta mike ta koma sama, har aka yi isha Junaid bai shigo parlon ba iyaka ya tafi masallaci ya dawo ya koma sama, can dai Umma na kallon Zahrah tace "D'an yi mana magana da shi xa mu koma ne" mikewa tayi ta tafi sama ta shiga dakinsa, yana danna laptop ta samesa ta karasa tace "Xa su wuce wai" kudi ya ciro har dubu hamsin ya mika mata yace "Ki basu" xaunawa tayi kusa da shi ta karbi kudin ta ajiye tace "Nooo, ka fito kuyi sallama" yace "Why?" A hankali tace "From there expression sun yi regretting everything" yayi murmushi ya dago fuskarta yace "And that's because basa gidanmu yanxu" tace "Kamar ya?" Mikewa yayi yace "Am coming" daga haka ya dau kudin ya fita, xaunawa yayi parlon ba tare da ya kallesu ba Umma tayi karfin halin cewa "Ahmad dama mun xo ne mu roki alfarmar ka taimake mu kayi ma Alhaji magana mu koma dakin mu, sai kuma a yafe juna abubuwan da suka faru a baya.... Sharrin shaidan ne" shi dai kansa na kasa can yace "Toh..." Ya mika masu kudin yace "Allah kiyaye hanya" Hajiya ta karba tace "A'a har da wahala haka Ahmad, to Allah yayi albarka" Ameen kawai yace ya mike ya nufi stairs yace "Bari in kirata" daga haka ya haura sama. Yau Zahrah kin fitowa tayi xuwa dakin Humainah don ma kar ya kuma kiranta dakinsa, duk ya kagu ya ji fitowarta amma shiru har Karfe sha biyu, to ko dai har ta xo ta wuce bai sani bane, mikewa yayi ya fita ya nufi dakinta, a hankali ya tura kofar ya ganta kwance, tana ganinsa tayi saurin rufe ido ya karasa ya xauna gefenta yace "Yau baki tsoron kwana ke daya kenan?" Ba tare da ta bude ido ba tace "Eh" wara ido yayi yace "Da gaske?" Xata juya masa baya ya rikota yace "Jasmine" bude ido tayi ta mike xaune ta buda masa hannu alamar what, murmushi yayi ya kamo hannunta yace "Nothing, m just missing you" tace "Ohk thank you, Gud nyt" yace "Uhm korata kike?" Gyada masa kai tayi yayi dariya yace "Ohk xan tafi, but you know what?" Kallonsa kawai take, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace "Ba mu taba sallah tare mun roki Allah ya albarkaci auren mu ba" tace "Ni na taba yi" ya buda ido yace "I mean togeda princess, c'mon tashi kiyi alwala muyi sallah" tace "Ina da alwala na" ya d'ago kanta yace "Gud" daga haka ya mike ya dau darduma ya shimfida masu, juyawa yyi yana kallonta yace "Taso mana" ta nuna masa hijab dinta tace "Bani" yace "Meyasa baxa ki dauka da kanki ba" tace "Nothing" murmushi yayi ya dauko ya mika mata ta sa sannan ta mike. Nafila ya ja su raka'a biyu, ya jima xaune yana addu'a bayan sun sallame snn ya juya yana kallonta, murmushi ya sakar mata ya dafa kanta, a hankali yace "Let me pray for you princess" rufe ido tayi bata ce komai ba har ya gama sannan ta bude ido tana kallonsa, langwabar da kai tayi tace "Is that all" ya gyada mata kai, ta mike ya bi ta da kallo, kofa ta bude ta juyo tana kallonsa tace "Gud nyt, I want to go to bed!" Wara ido yayi yana kallonta can yayi murmushi yace "Oh korata ma kike ko?" Girgixa masa kai tayi tace "A'a bacci xan yi ne" yace "toh ni a nan nake son in kwana" shiru ta d'an yi tana kallonsa can tace "Ohk," ta rufe kofar ta dawo tayi kwanciyarta ta ja bargo tace "Gud nyt" kai kawai ya gyada mata, kusa minti goma xaune snn ya mike ya kashe wutan dakin ya dawo ya kwanta ya birgina kusa da ita, Juyowa tayi da sauri murya can kasa yace "Baki yi bacci ba" "Uhm" kawae tace xata