← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 104

Sashe 72

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

bata gansa ya xo ba, gashi tana tsoron tambayar captain shi, shi ma captain din ba sosai take ganinsa ba don tun bayan incident din daren ranan bai barin su hadu sai tayi bacci, duk dare kafin ya kwanta sai ya shiga to make sure she's fyn, a haka ta cika wata daya a gidan, ranan wani lahadi tana sharan parlor don yanxu kusan ita take duka aikin gidan idan captain baya nan taji an danna bell, ajiye broom din tayi ta mike da kyar don tun jiya cikinta ke mata ciwo, karasawa gun kofar tayi ta bude xaro ido tayi tace "Aunty!" Sai ta rungumeta ta saka kuka tace "plss go with me aunty" Hafsat dake kallonta ganin yanda ta rame tausayinta ya cika ta tace "Ohk I will dear" kallonta kawai El-ameen yake, tana daga kai ta gansa ta karasa da gudu ta rungumesa hawaye na sauko mata tace "Don Allah Uncle ka tafi da ni kar ka bar ni" janyeta yayi jikinsa ya gyada mata kai kawai, Hafsat ta karasa cikin parlon, El-ameen ya kama hannunta suka shiga, kasa ta xauna kusa da shi tana kallonsa tace "In dauko kayana?" Yace "Captain fah?" Bude hannu tayi tace "Ban sani ba nima" xai yi magana aka bude kofar Junaid ya shigo, ya d'an yi mamakin ganinsu ya karasa cikin parlon suka gaisa da Hafsat, ya xauna yana kallon El-ameen da ya hade rai yace "Welcome Doctor" *Haske Writer's Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 64__65 Tashi ka je, k'asa tashi yayi Abba yace "Baxa ka bar min parlor ba?" A hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah, sharrin...." Mikewa Abba yayi yace "you are stupid, get away" mikewa yayi da kyar ya fita daga parlon, ya nufi gate, yana bude motar Jasmine dake xaune yanda ya bar ta har lkcn idonta rufe tace "Captain!" Ba tare da ya kalleta ba bai kuma ce komai ba ya tada motar, kiransa ta kuma yi bae tanka ta ba ya ja motar, laluba sa ta shiga yi, ya kama hannunta yana driving da hannu daya yace "Open ur eyez!" Ta girgixa kai tace "It's hurting me" bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, kallon b'akin motar dake Parke daga gefen flowers din da ya xagaye frontage din gidan ya dinga yi, mai gadi na bude masa gate ya sauke glass yace "Waye yayi parking can?" Mai gadin ya kalli motar yace "ca yayi wani yake jira a can gidan yallabai" junaid bai kuma cewa komai ba ya sake kallon motar sannan ya ja motarsa ya shiga compound, yana gama parking ya juya yana kallonta yace "Jasmine open those eyez idan ba haka ba xan yi tafiya ta in bar ki" da sauri ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "yana min ciwo captain, don't leave me plss, ka kira uncle kace ya kawo min Magani" wani kallo yake mata kamar tana ganinsa, can ya janye hannunsa xai sauka ta rikosa da sauri tace "No plss" hade rai yayi yace "toh ba sai na fita ba sannan xan fito da ke" a hankali ta sakesa ya fita ya xaga ya bude side din da take ya kama hannunta ta sauko ya rufe motar suka nufi cikin gidan, parlor ya xaunar da ita ya koma wani kujerar ya xauna ya dau remote yayi powering tv, a hankali tace "Captain!" Ya kalleta bai ce komai bs, kuma kiransa tayi yace "Yess!" Tace "kar ka tafi ka barni" dauke kai yayi bai tanka ta ba ya maida dubansa gun tv, can ya mike ya shiga toilet din dake parlon ya dauro alwala ya fito, nan parlon yayi don har anyi isha a mosque, yana idar wa ya koma ya xauna ya ci gaba da kallonsa, kiransa tayi ya juya ya kalleta yace "What?" A hankali tace "I want to ease my self" kallonta kawai yake har sai da ta kuma kiransa yace "Toh ki bude idonki ki je kiyi mana" girgixa masa kai tayi tace "Yana min ciwo ne" bai kuma cewa komai ba ita ma tayi shiru, har bayan kusan minti goma tausayinta ya ji ya mike da kyar ya karasa kusa da ita yace "Stand up" mikewa tayi ya kama hannunta ya nufi toilet da ita nan bakin kofar ya bar ta yace "Go in" daga haka ya juya ya dawo parlor, ba a dau lokaci ba ta fito tana kiransa yace "What?" Tana lalube ta shigo parlon ta xauna, sun fi awa daya xaune ganin yanda tayi lamo jikin kujerar kmr me bacci yace "Me xa ki ci?" Da sauri ta bude ido alamar baccin ya fara daukarta, ya mike yana kallonta ya karaso kusa da ita ya durkusa yana kallon idanuwanta da suka yi ja sosai yace "Good you open the eyez, ya daina ciwo yanxu" shiru tayi sai kuma tace "Yana min" yace "Me xa ki ci?" Bata ce komai ba ta yi kasa da kanta yace "Xa ki sha tea nd bread?" Ta kallesa tace "No! Only tea" mikewa yayi ya nufi kitchen ba a dau lokaci ba ya dawo rike da cup din tea, ya mika mata ta karba tace "Thank you!" Komawa yayi ya xauna, tana gama shan tean ya sa ta taje tayi alwala tayi sllh. Karfe goma saura ganin ta fara bacci yace "Go to bed if you are sleepy" mikewa tayi ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Washegari da asuba ya kwankwasa mata kofa, cire bargon jikinta tayi ta xauna tana murxa ido, can ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar ta bude, kallonta yake daga sama har kasa, yar rigar bacci ne jikinta tace "Captain" ya sauke idonsa yace "It's time for prayer," har ya juya xai tafi ya kuma juyowa yace "kina gama sllh ki shirya for islamiyya" ta gyada masa Kai ya juya ya bar bakin kofar, yana xaune parlor shirye cikin uniform rike da cup din coffee Jasmine ta sauko, kallon agogo yayi yaga Karfe bakwai saura minti goma yace "Tafi ki dafa indomie" tace "Toh" ta nufi kitchen, bin ta yayi da kallo yace "Come here" ta juyo ta dawo inda yake ta tsugunna tace "Na'am" yace "Baki iya gaisuwa ba" kallonsa kawai take wanda hakan ya sa shi dauke kai, a hankali tace "Good morning captain" ajiye cup din hannunsa yayi ba tare da ya kalleta ba ya mike yace "Morning" tashi tayi ita ma tana kallon white uniform din jikinsa tace "You've not buttoned all the buttons captain" kokarin barin wajen yake ta shiga gabansa tace "Let me help you" da sauri ya koma baya ya hade rai yace "No! I will do that my self" daga haka ya nufi stairs, ta bi sa da kallo. El-ameen ne xaune a study room dinsa earpiece makale a kunnensa yana duba wani littafi, aka turo kofar dakin hade da sallama ya daga kai ya mata kallo daya ya maida dubansa kan littafin gabansa, karasowa tayi tace "You have a visitor!" Yace "Who?" Tace "Yana parlor" rufe littafin gabansa yayi yace "Alryt!" Ta juya ta fita, ya mike ya fita xuwa bedroom dinsa, jallabiya ya daura kan kananun kayan jikinsa ya sauko parlor, Aliyu ne xaune parlon, El-ameen yace "uhn! Ashe ka san gidana Dr" Aliyu ya kallesa yace "No! da map na xo" El-ameen yayi murmushi yace "Da alama" karasowa yayi ya xauna yace "Toh ya aka yi Dr, don nasan ba haka nan ka xo ba" Aliyu yace "It's private, let move out" El-ameen yace "Uhm toh mu nawa ne a parlon?" Mikewa Aliyu yayi ya nufi kofa El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa. Bayan kwana uku Humainah na xaune kasa a parlor ta daura kai kan kujera duk ta rame ba kadan ba don ba karamin wahala take sha ba, Mumy ce xaune daga gefenta da sisternta Anty Nafee sai Abba dake parlon shi ma, Anty nafisat tace "Wai baxa kiyi magana ba Humainah, Meye haka kike yi" ta fashe da kuka tace "Ni ba abinda ya hadamu Mumy, ni ban masa komai ba" shiru duk suka yi suna kallonta, hawaye ne ya shiga sauko mata, Mumy ta jinginar da kanta jikin kujera a sanyaye, she's just imagining anya Ahmad dinta ne kuwa, Ahmad din da ta yarda da tarbiyar da tayi masa, Ahmad da tayi raise da hannunta, Ahmad da ko kadan bai son bacin ranta, wai yau har kwana biyar bai sake waiwayo gidan ba, girgixa kai tayi ta lumshe ido, mikewa Humainah tayi da sauri Anty nafisat ta bi bayanta, bedroom ta kai ta bayan ta gama aman, ta kwantar da ita sannan ta xauna gefenta tace "Humainah idan ma baxa ki iya gaya ma su Mumy abinda ya hada ku da Ahmad ba ni ki gaya min, take me as ur mum kin ji" girgixa kai tayi tace "Ba abinda ya hadamu Aunty" sai kuma ta fashe da kuka, Anty nafisat tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta. Junaid na xaune parlor da evening yana kallon wani program though absentminded, duk ya rasa dalilin da yasa ba shi da rest of mind daga jiya, haka kawai sai ya ji gabansa ya fadi, gashi yana son xuwa gida amma ya kasa, ko kadan bai son xamansa da Jasmine su biyu kadai, har aka kira magrib yana xaune parlon, can ya mike ya je yayi alwala ya wuce masallaci, yana dawowa sama ya tafi ya sameta xaune kan darduma, daga bakin kofar ya tsaya yace "Me za ki ci?" Ta d'an bude ido tace "Potatoe nd ketchup!" Tabe baki yayi ya juya ya fita ya dau makullin motarsa. Sha biyu saura na dare yana kwance idonsa biyu sai dai ya kashe wutan dakin yana son yin bacci amma ya kasa, murda kofa dakin aka yi jasmine ta shigo da sallama, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yace "What's it?" Karasowa take son yi yace "Tsaya nan, nd what did you want?" Tsayawa tayi tace "Cikina ke man ciwo" yace "Go nd sleep gobe xan baki Magani, stop disturbing me" a hankali tace "Ohk" ta juya ta fita, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya kwanta, har daya bai yi bacci ba yana son dubata amma ya ki xuwa daga karshe ya mike ya dauro alwala ya shimfida
Chapter 72 · 0% Book details