← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 104

Sashe 79

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

fado masa, murmushin takaici yayi, yayi saurin kauda tunanin, ido hudu yayi da Hadiza da ke tsaye sakale da jakarta alamar tafiya xata yi ga nikab a hannunta, Umma da Hajiya ma na tsaye balcony din, suna hangosa Umma tayi mata alamar da ta shiga parlor, da sauri ta shiga ta kullo kofa, girgixa Kai yayi nufi balcony din, Umma da Hajiya aka kafa masa ido da mamaki don a tunanin su gaishesu xai xo yi, ko kallonsu bai yi ba ya bude kofar ya shige parlon, Hajiya ta xaro ido tace "Ikon Allah Meye haka Ahmad?" Hadiza dake tsaye parlon ta xaro ido ganinsa, bai yi wata wata ba ya fincikota ya kai mata naushi a baki, wani kara tayi Umma da Hajiya da tuni suka shigo parlon suka shiga salati suna tambayar yana da hankali kuwa, ko sauraransu bai yi ba ya fixgota ya fito da ita tsakar gidan, dukanta ya shiga yi yana ball da ita kamar an aikosa, ta dinga ihu tana cewa a taimaketa, tuni 'yan matan gidan suka fiffito, Mumy ma ta fito, su Hajjo da aka diro daxu ma aka fito, Hajiya da ko ina na jikinta rawa yake ta dinga jan Junaid murya can kasa tana cewa "In ma laifi tayi maka kayi hakuri Ahmad.... Ka rufa mata asiri" ko saurarenta bai yi ba bugunta kawai yake kamar an aikosa, a fusace Hajja ta karaso ta fixgoxa ta sauke masa mari tace "Don uwar ka Amina dama shirin tafiya gidan ka nake yanxu, ban taba tunanin cewar da mahaukaci Muhammadu xai hada jikata ba, ita Humainahr ka sakar min, tsabar haukan naka ya girmama har gida kake xuwa jibgan mutane yanxu" kokarin gudu Hadiza take ya wani fixgota ya kuma sauke mata mari, Abba ne ya shigo compound din daga masallaci, ya tsaya da mamaki yana kallon tsakar gidan, Junaid da ban da tafasa babu abinda xuciyarsa yake ya fara waige waigen inda xai ga Humainah, ganin bata compound din ya ja Hadiza har part din Mumy duk aka bi sa da ido ya shiga har parlor da ita, salati Umma ta dinga yi tana cewa anya Ahmad lafiyarsa kuwa, ku ceci 'yar mutane don Allah, fitowar Humainah kenan daga daki ya jefar mata da Hadiza nan gabanta yana kallonta sannan ya juya ya fice daga parlon, kallon mamaki Humainah ke mata, tuni duk aka shigo parlon, Abba kam dama part dinsa kawai ya nufa, Hadiza da ko ina na jikinta rawa yake ta mike da sauri xata fita, Humainah ta rikota tace "Me ya kawo ki nan?" Juyawa tayi tana waigen inda xata ga su Umma, Hajjo tace "Ina kika santa?" Hawaye ne ya cika idonta tace "Ita ta ja min komai, ni ban santa ba...." Hajjo tace "yo ni daxu tare muka shigo gidan nan da ita, ita ce ma ta shigo min da kayana daga adai daita kuma tace min Ita 'yar wan Bilki ce, me ta maki?" Kuka sosai Humainah ta fara ta durkushe gun tace "Ita ce silar komai, ita ke xuwa gidana kullum...." Salati Hajja ta saki tace "Ita ta sa ya sake ki kenan?" Humainah ta gyada kai hawaye na sauko mata, Hajja ta cakumo Hadiza tace "Ni dama nasan ba yin kan jikana bane wannan, nasan baxai aikata haka a banxa ba, to ko ki fadi wanda ke tura ki gidan ta ko in xuba maki fetur yanxu in babbakaki" juyawa Umma tayi ta fice daga parlon Hajiya ta bi bayanta da sauri, Hajja ta kwada mata mari tace "Baxa kiyi magana ba" Mumy da duk jikinta yayi sanyi ta karaso tace "Ki yi hakuri Hajja ki sake ta...." Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Ke ja can dalla" shaketa Hajja ta yi tace "Baxa kiyi magana ba?" Hadiza ta fashe da kuka tace "Ni Umma ce da Hajiya suke tura ni" salati Hajja ta saki tace "Suke tura ki kije kiyi me?" Shiru Hadiza tayi Hajja ta ja ta xuwa gun tv tana neman wayar wuta tace "Toh xa ki ga ikon Allah idan ba ki bude baki kin ban labari ba" juyawa Humainah tayi hawaye na bin kuncinta ta koma daki, Hadiza da tayi mugun tsorata jikinta na rawa tana hawaye tace "Wllh tura ni suke in je in dinga xugata" Hajja ta saketa tana tafa hannu tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, dama su suka kashe ma jikata aure, to su ma na su na rawa yanxu, ina Muhammadu" daga haka ta fice daga parlon kamar xata tashi, jigum Mumy tayi tana kallon Hadiza dake ta waige waige kamar munafuka, can kuma ta fice da gudu daga parlon. Tafiya kawai El-ameen ke yi a hankali, haka kawai gabansa ke faduwa ganin anguwar da ta nuna masa wai nan xa su bi, tafiya me nisa suka yi tace "Here!" Juyawa yayi da sauri yana kallonta yace "Where?" Nuna masa babban entrance din tayi tana bin ko ina da kallo ganin canji da dama tace "there!" Kasa daina kallonta yayi tace "Just horn, sai ka sauke glass xan masu magana" girgixa kai yayi yace "Wai gidan sarautan nan?" Kallonsa ta tsaya yi kafin tace "Eh gidanmu ne!" Dauke kai yayi can ya juyo yace "Kina nufin ur father is a king?" Bude motar ta shiga kokarin yi tace "Yeah my father is a king" danna horn yayi kamar yanda tace har lokacin idonsa na kanta, ita ko sai kalle kalle take fuskarta dauke da mamaki ganin changes da dama, wasu dogarai ne suka fito suna kallon motar, karasowa suka yi ta sauke glass tana kallonsu, ganin bata gane ko daya daga cikinsu ba ta bude motar ta fito tace "Ku bude mana hanya" daya daga cikinsu yace "Daga ina?" Fitowa El-ameen yayi yace "Baki daga katsina" bude masu hanyar aka yi, ya koma mota ita ma haka, ya ja motar ya shiga ciki, tafiya mai tsayi suka yi kafin su kai wani gate, kallon El-ameen tayi kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, wasu guards suka karaso gun motar, sauke glass tayi daya daga cikinsu yace "Daga ina?" kallonsa kawai take don shi ma bata san sa ba, toh yaushe aka canxa guards din bakin gate kuma, a takaice tace "Bude mana gate" El-ameen yace "Sorry, baki daga katsina, mai martaba na sane da xuwan mu" komawa yayi aka bude gate din ya ja motar xuwa babban haraban palace din, juyowa tayi da sauri ta kallesa tace "Everywhere looks strange" kashe motar yayi yace "How strange" a hankali tace "Naga changes da yawa ne" *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 74..... Bude motar tayi ta sauka, shi ma ya sauko, har ta nufi kofar shiga fada sai kuma ta juyo tana kallonsa tace "Ni xan bi ta baya, may be Abbana na tare da baki, you follow there" girgixa kai yayi yace "No i will wait out here" tabe baki tayi ta juya ta dau wata hanyar daban ya bi ta da ido har ta bace masa, ajiyar xuciya ya sauke ya koma can inda wasu bishiya ke a jere ya ja daya daga fararen kujerun dake gun ya xauna, wayarsa ya ciro ya shiga kiran layin Junaid, bugu uku ya daga, El-ameen yace "Amm muna bauchi Man" Junaid dake xaune laptop gabansa yace "Ohk, it's good" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Guess what frnd?" ajiye laptop din yyi a gefensa yace "Not in the mood" Murmushi El-ameen yayi yace "Ohk Gudnyt" katse wayar junaid ya jefar da wayar hannunsa ya mike ya fice daga dakin. A hankali Zahrah ta tura kofar ta shiga babban parlon da nan ne masaukin manyan baki a fadan, bbu kowa parlon, ta dinga bin parlon da kallo ganin shi ma ya canxa mata, hanyar da xai sada ta da bangaren Ummanta ta nufa da sauri, lokaci daya taji gabanta na faduwa, jakadiyar Umma ce mutum ta farko da ta fara haduwa da a hanya, wara manyan idonta tayi ta karasa da sauri tace "Baaba na dawo, ina ummana, ina su Ummi.....!" Wani kara jakadiyar tayi a gigice ta saki kayan hannunta ta juya da gudu ta bar gun tana salati, still Zahrah tayi ta bi ta da kallon mamaki, kan kace me sai ga ma'aikatan fadan sun bubbullo jin ihun jakadiya, sai dai duk wanda yayi tozali da ita sai ya bar gun a guje, duk ko ina ya hargitse, ita dai tana tsaye kamar warce aka dasa a gun cike da mamaki, a hankali ta shiga bin jikinta da kallo ko wani abu ne jikin nata, bata gama recover ba sai da yayanta ya shigo parlon taga yana mata wani kallo, da sauri ta nufesa ta ga ya juya ya bar gun, sosai jikinta yayi sanyi ta ji kafafuwanta sun kasa daukarta, Umma ce ta fito da stepmum dinta, sai dai ga mugun mamakinta sai gani tayi ita duk sun yi still a position dinsu suna kallonta ko kiftawa babu, Ummi ce ta shigo ita ma suna ido hudu ta fasa wani kara a rikice ta juya da gudu ta bar gun, juyawa Zahrah tayi da sauri hawaye cike idonta ta fita da gudu, a hankali Umma ta sulale gun ta fadi kasa a sume, rikicewa jakadiyar ta da sauran ma'aikatan dake gun suka yi suka yo kanta, Zahrah na fita dama inda ta hango El-ameen ta nufa tana isa gunsa ta xube gun ta fashe da kuka sosai tace "Why is everybody running away from me, mene a jikina da suke gudu plss tell me" shiru yayi yana kallonta, sai ya ji tausayinta, a hankali yace "Bbu abinda ke jikin ki, they are just surprise ne...." Girgixa kai tayi cikin kuka tace "Noo, what are they surprise at, do I look new? Tell me plss, dukkansu guduna suke yi" lumshe ido yayi yace "Kila basu yi xaton ganin ki yanxu bane" buda ido tayi tace "Why is that?" Takun da suka ji yasa su juyawa gaba daya, Mai martaba ne tafe da dogaransa a baya, mikewa tayi da sauri ta nufesa da sauri tace "Abba!" Kallonta kawae yake, ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumesa cikin kuka tace "Abba ni ce pa Fatima" daura fuskarsa yayi a kanta cikin sanyin
Chapter 79 · 0% Book details