Sashe 39
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
din dake gaida sa ba ya haura sama da ita ya bude office dinsa suka shiga, key ya sa ma kofar sannan ya juya yana kallonta ya sauke ajiyar xuciya yace "We've got a good solution koh" kama hannunta yayi ya nufi bedroom din dake office din ya xaunar da ita kan gado yana kallonta, kwan kwasa office dinsa ya ji ana yi ya mike da sauri ya fita, mikewa tayi ita ma da saurinta ta bi bayansa, ganin ta biyosa yasa bai bude kofar ba yace "Who's there?" Muryar nurse yaji tace "ur attention is needed at the theatre sir" a fusace yace "Toh da ban xo ba fa" shiru tayi yyi tsaki ya kama hannun Jasmine ya maida ta dakin, xaunar da ita ya kuma yi a hankali yace "Look jewel, yanxun nan xan dawo kar ki bi ni plss" ya kusa second goma yana kallonta sannan ya mike a hankali xai fita ita ma ta tashi da sauri, yace "Ohhw ina xan kai ki jewel?" Fita yayi ta bi bayansa, ya isa show glass din dake office din me dauke da magunguna da ruwan allurori ya bude ya dauki wani kwalban allura ya rufe, syringe ya dauka ya juya suka kusa cin karo, yace "Sorry!" kama hannunta yyi suka koma dakin ya sa ta xauna, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata a lap, 'yar kara kawai tayi masa tana bata fuska, yayi kasa da murya yace "Sorry jewel!" sun kusa minti goma xaune yana yi yana kallon agogo, yaji an kuma kwankwasa kofa, ya mike da sauri ita ma ta mike sai dai da ganinta kasan duk jikinta ya mutu, rike hannunta yayi ganin yanda take layi ya fito office din yace "Yes!" Muryar Abbansa yaji yace "S'ako na bai iso gare ka bane, ka wani garkame office kana ce min yes" xaro ido yayi yace "Ohh No, kaya nake canzawa ne Abba gani nan xuwa yanxu" Abba bai kuma cewa komai ba, hakan yasa ya kama hannunta suka koma dakin, kwantar da ita yayi ta lumshe ido, ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya bude inda kayan shiga theatre dinsa suke, ya cire na jikinsa ya saka sannan ya lullubeta ya fito daga dakin ya rufe da key. Sha biyu saura ya fito daga theatre, yana komawa office ya bude dakin yaga bacci kawai take, toilet din dake nan ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kananun kayansa ya fito office ya xauna ya kifa kansa kan table don bacci yake ji, wata nurse ta shigo rike da cup din coffee ta ajiye masa kan table tace "Sir" dagowa yayi yace "Thanks" har ta kai kofa xata fita yace "Nurse Sharifah" juyawa tayi ta dawo tace "Sir?" Yace "Nan sama kike ko k'asa yau?" Tace "a nan nake duty" yace "good, akwai patient a dakina, i want you to stay with her throughout the nyt, mental disorder gareta, in case xata farka cikin dare ki rakata restroom" shiru tayi tana kallonsa tsoro bayyane fuskarta, murmushi yayi yace "She won't hurt you, bata komai, just in case kar ta tashi ne yasa nace ki tsaya da ita" a hankali tace "Ohk sir... Let me explain to..." Katse ta yayi yace "No! Xan je in mata bayani" daga haka ya mike ya fita. Ta lallaba ta isa kofar dakin ta tura a hankali ta leka ta ganta tana bacci cikin bargo, a haka ya dawo office din yace "Ki shiga baxa ta maki komai ba nace" gyada masa kai tayi ta shiga dakin, ya dau coffee dinsa ya sha bayan ya huce sannan ya mike yayi kwanciyarsa kan kujeran dake office din. Can misalin Karfe uku ihunta ya farkar da shi ya mike da sauri ya nufi dakin dai dai lokacin da nurse din ma ta fito da gudu, shiga dakin yayi ya ganta tsaye sai ihu take, ya karasa da sauri ya rike hannunta yace "Jewel!" Tsit tayi tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya ya xaunar da ita gefen gado, ya juya xai fita ta mike ta bi sa da sauri, nurse din na tsaye bakin kofar fita office har lokacin yace "Taho ki rakata restroom nace babu abinda xata maki" da kyar ta karaso ta shigo dakin, shi ya kaita toilet din, ya juya yana kallon Nurse din ta karaso a hankali ita ma ta shiga toilet din ya juya ya fita. Da asuba yana kwance idonsa lumshe bayan ya dawo daga mosque yaji mutum kusa da shi, bude ido yayi da sauri ya mike xaune yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace "Good morning jewel" dagota yayi ya xaunar da ita gefensa, remote ya dauka ya kunna mata tv, wani kallo ta dinga yi ma TVn kamar idonta xai fito, dariya ta basa ya mike ya shiga daki yaga nurse din rakube kasan gado tana bacci, yace "Nurse Sharifa" mikewa tayi da sauri tana murxa ido duk da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi yace "Kin yi sllh?" Tace "Yes sir" yace "Good" toothbrush da paste dinsa ya dauko ya mika mata yace "Xaki wanke mata baki" ta karba tana kallonsa, ya fito ya dagota taki tashi idonta kyar kan TV ko kiftawan kirki bata yi, dariya ta basa sosai ya kuma dagota ta fasa masa ihu har lokacin bata dauke idonta kan kallon ba, ya dau remote ya kashe tvn, sai a sannan ta juya ta kallesa, yayi murmushi ya dagata ta mike ya shiga daki da ita, kin yarda nurse din ta wanke mata baki tayi, hakan yasa ya wanke mata da kansa, ganin hadiye komai take yasa bai mata amfani da ruwan toilet din ba, ya fita ya dauko table water ya bude ya bata ta sha ya kama hannunta suka fita, ya kalli nurse din yace "Tea xaki je ki hado min plss" ba musu ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea ya karba yace "Thank you, kafin ki tafi ki dawo" tace "Ohk sir" sannan ta fita, jasmine ya shiga ba tean, ta sha kadan taki shan sauran da alama tea bai dameta ba, mikewa yayi ya tafi ya wanke bakinsa toilet, juyawan da xai yi ya ganta tsaye bayansa, murmushi yayi ya kama hannunta suka fito office, ya xaunar da ita sannan ya shanye sauran tea'n, TV ya kunna mata don yana son fita ya gaida Abbansa, ai ko ta nutsu sosai tana kallon mutanen dake yawo a tvn, ya mike a hankali yanda baxata lura ba ya fita ya haura last floor xuwa office din Abbansa, wani aikin Abban nasa yasa sa, ransa bai so ba amma bai yi musu ba ya shiga yi, yana cikin yi aka yi interrupting power, ya xaro ido sanin kila yanxu xata fara ihu, da sauri ya dinga signing files din, cikin minti sha biyar ya gama ya fice, ya sauka xuwa office dinsa, yana budewa yaga wayam daki ya nufa ya tura nan ma wayam, ya xaro ido ya shiga toilet nan ma bbu ita, wani mugun tashi hankalinsa yayi ya fito da sauri ya dinga dube dube ya sauko har downstairs yana kallon nurses din yace "wata patient bata sauko ba yanxu" bai jira cewarsu ba ya fita haraban asibitin da sauri, ya dinga dube dube bai ganta ba, gun masu gadi ya nufa da sauri ya tambayesu suka ce basu ga kowa ba, komawa reception yayi ya dinga yi ma nurses din masifa basu ga wata ta sauko ba yanxun nan, nan suka shiga dube dube su ma cikin ward,haka aka yi ta nemanta cikin asibitin har da likitoci da cleaners, wasu na tunanin anya kuwa Dr El-ameen dai dai kansa yake ganin yanda ya wani rikice nurse Sharifa ma duk hankalinta ya tashi barin da tasan ba mai hankali bace patient din, har Abba sai da ya sauko jin wai ana neman patient daga bakin wani likita, kallon d'an nasa kawai yake yana son sanin wace patient ce wannan wanda shi kadai yasan da ita a asibitin, Salatin da Dr Ibrahim wanda office dinsa ke kallon na El-ameen yayi ya ja hankalin nurses da wasu likitocin, da hanxari duk aka karasa wajen aka gansa tsaye bakin office din yana kallon ciki da mamaki, El-ameen ya karasa shima yana kallon office din, tsaye take a office din duk tayi kaca kaca da uban files din dake kan table dinsa, ta bude show glass duk ta watsar da magunguna da allurorin dake ciki, El-ameen ya d'an saci kallon Abbansa da ya rungume hannu yana kallon ikon Allah, daga likitocin har nurses din kallonta suke su kalli El-ameen, hakan ya bata tsoro sosai ganin yanda aka taru bakin kofar ana kallonta, ta fasa wani shegen ihu da karfi tana kallon El-ameen, sunkuyar da kansa yayi, ta dinga ihu can ta tafi bayan glass da gudu ta labe har lokacin ihu take, da kyar ya dago kai yana kallon Abbansa yace "Abba... Brain disorder gareta, I..I... She's under medication ne Abba, jiya da xan xo na taho da ita..." Wani mugun kallo Abba ke masa yace "Asibitina yayi kama da na mahaukata?" Sosa kai yayi xai yi magana Abba ya masa wani uban tsawa yace "Uwar ka xaka gaya min, wasu mahaukatan iyayen ne suka baka 'yar su ka sata under medication har kake yawo da ita?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yace "No, A gida nake mata treatment din Abba, dama...dama akwai injection da nake mata da daddare ne to kuma ka kirani clinic shi yasa na taho da ita... Yanxu ma xan maida ta gidansu..." Abba yace "Amma arnaye ne iyayenta koh?" Shiru yayi bai ce komai ba, Strictly Abba yace "Ka maida masu 'yar su ka basu shawaran su kai ta asibiti, na kuma hanaka aikin nan daga yau, in ma kana son concentrating a field dinka na neurology ne yanxu you can go and apply for work a psychiatry ba ka dinga yawo da mahaukata ba har kana kawo min su asibiti suna min barna" daga haka Abba ya juya ya bar wajen, nurses din ma duk suka juya, jiki a sanyaye El-ameen ya karasa cikin office din ya kamo hannunta suka fita, sai wani shisshigewa jikinsa take a tsorace, likitocin dake gun suka bi sa da kallo,