← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 104

Sashe 88

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

you all his time, he took care of you, bai kyamace ki ba, bai kuma taba gajiya da ke ba....." Kuka sosai Zahrah ta shiga yi tana kallon yar uwarta, Ummi da jikinta yayi sanyi tayi shiru tana kallon ta ita ma, cikin rawar Murya Zahrah tace "Toh shi Ahmad fah?" Ummi ta sauke idonta kasa a hankali tace "Yeah yayi maki kokari sosai shi ma, just that na lura shi ba mai son hayaniya bane, sannan miskiline, kuma na lura bai son yanda El-ameen ke yi maki, sai naga ma kamar kishi yake duk da baya cewa komai, indai El-ameen na parlon naga baya xama sai kawai ya fita, idan kuma ku biyu ne kadai ya kan xauna kusa da ke, sai dai kuma baki saki jiki da shi yanda kika yi da El-ameen ba, bai kuma san ma yanda xai kula da ke ba" Zahrah ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido, Ummi ta kamo hannunta tace "El-ameen na son ki sosai Zahrah, duk da halin da kike ciki bai kyamace ki ba don har abinda kika kai baki yana ci....." Zahrah ta bude ido tana kallonta, murmushi ta kirkira tace "Yeah na gani" Ummi tayi murmushin ita ma ta mike ta dau Laptop din ta fice tana cewa "I just love this sweet sis, xan kai ma Abbanmu...." kuka sosai Zahrah ta fashe da bayan fitar yar uwarta, ita kanta ta rasa kukan me take ta mike da gudu ta shiga bedroom ta fada kan gado ta dinga rera kukan. Da kyar Junaid ya iya fita masallaci sallahn asuba, yana dawowa kuma yayi kwanciyarsa nan parlor kan kujera don bai jin xai iya fita aiki, ya rasa gane xaxxabin me ke son rufe sa, mikewa yayi daga karshe ya koma sama yayi wanka ko xai iya xuwa aikin, kamar kar ya fito ya ji wani sanyi na shigarsa duk da ba da ruwan sanyi yayi Wankan ba ma, ya dade kwance cikin bargo kafin ya mike ya shirya cikin kananun kaya ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa yana gama parking ya fito ya tafi bangaren Mumy kansa na sara masa, fatima ce xaune parlor da Humainah da khadija, bai iya ya amsa gaisuwar da suke masa ba ya shiga dakin Mumy, bbu kowa dakin ya kwanta kan gadon, bai yi minti biyar da kwanciya ba Mumy ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa can ta karaso kusa da gadon tace "Ahmad!" Bude ido yayi yana kallonta, hannu ta daura forehead dinsa tace "Are you sick?" Mayar da idonsa yayi ya lumshe yace "Just headache mum" mikewa tayi ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea tace "Tashi ka sha shayin sai in baka Magani" ba musu ya mike xaune ya karba cup din ya shiga shan tea din, kadan ya rage ya ajiye, Mumy ta dauko masa paracetamol da ruwa a cup ta mika masa, ya karba ya hadiye maganin, tsaye tayi tana kallonsa don ta ma yi mamakin da ya karba maganin, mikewa yayi da sauri tace "You better don't do that...." Tsayawa yayi da farko yana yamutse fuska ta galla masa harara, sai kuma ya shige bathroom sai amai, tana nan tsaye har ya fito, bai bari sun hada ido ba ya koma ya kwanta ya lumshe ido, tace "Sai ka tashi mu tafi asibiti, saura in mun je ka gudo" girgixa Kai yayi cikin sanyin murya yace "Wllh bacci nake ji Mumy jiya ban yi bacci ba, idan na tashi sai mu je" ta kusa minti biyar tsaye tana kallonsa bata ce komai ba, har ta ga alamar bacci ya fara daukarda, karasawa tayi ta dau wayarsa ta sa masa a silent ta ajiye sannan ta fita. Sai kusan karfe sha biyu junaid ya farka da wani matsanancin ciwon kai, da kyar ya mike xaune, El-ameen ya gani dakin xaune yana hada drip ga injections a gefe guda, El-ameen ya sakar masa murmushi ya mike yace "You are awake!" Dauke kai junaid yayi yana kokarin mikewa, El-ameen ya xauna ya riko hannunsa yace "What's wrong with you, lafiya muka rabu jiya fa?" Junaid ya dake yace "ce maka aka yi bani da lafiya?" El-ameen yace "Yeah, Zahrah ma na son gaishe ka wai, I told her you are sick" daga haka ya jawo wayarsa, wani kallo junaid ke yi masa xuciyarsa na tafarfasa. *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 82..... El-ameen ya gama danne dannensa ya Kai wayar kunne bayan few seconds yace "Hello Zahrah, here is the captain" daga haka ya mika ma junaid wayar yana kallonsa, kin kallon inda yake junaid yayi, har sai da yace "Ahmad!" Sai a sannan junaid ya kallesa yace "Did I told you am sick?" El-ameen yace "Yeah! I know you are okay, but karbi wayar...." Wani kallo junaid ke yi masa kafin ya karbi wayar ya kai kunne, gabansa ya fadi sosai jin muryarta da ya daki ear dinsa tace "Hello!" Dakewa yayi yace "Yeah, ina ji" shiru tayi shi ma haka, bayan kusan second ashirin ya kalli screen din wayar ya ga ba a kashe ba, mayarwa yayi kunnensa ya hade rai yace "Hello!" Tace "Yeah! Ina ji nima" tsaki ya ja ya katse wayar ya jefar kan gado ya juya yana kallon El-ameen yace "Kaga ka bar ja min raini gun yarinyar nan plss, ku je can ku karata ka daina sako ni a abun ku...." Murmushi El-ameen yayi yace "Alryt.... Yanxu dai bari in sa maka ruwan nan in maka allura am leaving" a fusace junaid yace "Wai ca nayi maka bani da lafiya ne, let me plss" mikewa yayi ya shige toilet ya kulle ya hade kansa da kofa, Murmushi El-ameen yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo tare da Mumy, tana kallon kofar toilet din tace "Ahmad!" Sai da ta kuma kiransa sannan ya amsa a hankali, strictly tace "Come out" ba musu ya fito jiki ba kwari ya karasa kan gadon, Mumy na tsaye El-ameen ya sa masa drip din sai a snn ta juya ta fita, El-ameen yayi 'yar dariya yace "Gaskiya ne Mumy's boy" ko kallonsa Junaid bai yi ba ya koma ya kwanta kan gado, El-ameen ya dau makullin motarsa da waya ya fita, lumshe ido Junaid yayi xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma da fitar El-ameen aka bude kofar dakin, Humainah ce ta shigo ya bude ido yana kallonta, karasowa tayi kusa da gadon ta durkusa tana kallonsa tace "Baka da lafiya ne?" Chin dinta ya dago yana kallon fuskarta yace "How are you feeling now" a hankali tace "Alhmdllh" yace "Kina cin abinci yanxu?" Girgixa masa kai tayi ta kwantar da kanta kan gado har lokacin tana kallonsa tace "Only tea" gefensa ya nuna mata, ba musu ta mike ta dawo kusa da shi, ya daura hannu kan tummy dinta yace "Ya babyn?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yayi murmushi tayi kwanciyarta gefensa, komawa yayi shi ma ya kwanta tare da lumshe ido. Sha daya saura aka buda kofar dakin Hajjo ta shigo, fashe wa da kuka tayi sosai ta karaso kusa da gadon tace "Ya baxa ka kwanta ciwo ba ka yaudare ni ka ci amanata Ahmad, har ni xaka dinga ma bakin ciki, to dadin abun dai ni ba talaka bace, kuma dukiya me uban yawa mijina ya mutu ya bar min wanda ko da xanje makka sau dari baxa su girgixa ba, ku abun duniya ya tsole ma ido kai da uban ka" tana kai wa nan ta nufi kofa fuu, junaid ya bita da kallo har ta fita, Humainah kam murmushi tayi ta koma ta kwanta. Da yamma junaid na kwance duk ya rasa me ke masa dadi so yake kawai ruwan ya kare ya cire ya fita daga gidan ko xai ji dadi, ba don Mumy ba da tuni ya tuge drip din, Humainah na kwance nesa da shi tayi bacci tun daxu, bude kofa aka yi El-ameen da Aliyu suka shigo dakin, kallonsu kawai yake Aliyu ya karaso shi ma yana kallonsa yace "Baka ji dadi ba ashe" junaid bai ce komai ba, Aliyu ya kara da cewa Allah ya sauwake" sai a sannan yace "Ameen thank you" El-ameen yace "My frnd Dr Aliyu hope ka gane sa" Junaid bai ce komai ba ya nuna ma Aliyu kujera ya xauna, Aliyu yace "Am ohk here" El-ameen yace "How are you feeling now Ahmad?" Dakewa junaid yyi yace "Naji sauki ka cire min ynxu" El-ameen yace "No! Sai ya kare, am coming back later" Junaid ji yayi kamar ya shakesa sai dai bai ce komai ba, El-ameen yace "Idan kaji sauki in shaa Allah xuwa gobe xa ka rakani bauchi, sarki na nemana" duk da faduwar da gaban junaid yayi bai nuna ba yace "baxan iya barin aikina in je bauchi ba" El-ameen yace "Alryt, Aliyu sai ya rakani," daga haka ya juya ya nufi kofa yace "Sai na dawo ltr" ba tare da Aliyu ya kuma kallon Junaid ba yace "Allah ya kara afuwa" daga haka ya fita shi ma, mikewa xaune junaid yayi ya dafa kansa. A can bauchi kuwa Zahrah duk ta daga ma mahaifanta hankali ita fa sai an kai ta gun dattijuwar matar nan duk inda take, da farko lallabata mai martaba ya dinga yi yace ta bari xa a nemo matar a kawo ta masarautan ganin ba hakura zata yi ba yasa yace a kira masa El-ameen. Washegari El-ameen ya dau hanyar bauchi tare da Aliyu, haka kawai yaji gabansa na faduwa, addu'a ya dinga yi a xuciyarsa Allah yasa ba fasa basa auren mai martaba yyi ba, Aliyu dai sai dariya yake masa yace "Ana xaune kalau xaka jajibo ma kanka aure, auren ma daga gidan sarauta.... Tab xaka sha takaici kuwa" murmushi El-ameen yayi yace "Can xa a sha takaici ba ni ba" Aliyu yace "Ni dai don kawai ina son ganin babe din ne shi yasa xan bi ka amma bbu ruwana da neman aurenka, ni bayan Hafsat nake" El-ameen bai tanka sa ba ya kuma cewa "Toh wai yasan kana da mata kuwa?" Gyada kai El-ameen yayi yace "Yeah, I told him everything" Aliyu ya xaro ido lkci
Chapter 88 · 0% Book details