Sashe 25
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
_By Khaleesat Haiydar_ 17..... El-Ameen ya sakar mata murmushi murya can kasa yace "Sorry!" kauda kai tayi, ya mike ya d'agata suka tafi sama, bin bayansu mama jummai tayi, yana shiga daki ya xaunar da ita gefen gado ya xauna gefen gadon shi ma yana cire shirt din jikinsa Junaid ya fito daga bayin rike da shirt dinsa da ya wanke, ko kallonsu bai yi ba ya fice daga dakin El-ameen ya bi sa da kallo, yana sauka downstairs ya dau makullin motar El-Ameen ya fice daga gidan. Gida ya tafi, yana gama parking ya fito rike da shirt din nasa ya nufi part dinsa, su Hajiya dake xaune tsakar gidan suka bi sa da kallo ganin daga shi sai singlet da jeans, bae ko kallesu ba ya bude kofa ya shiga parlornsa ya rufe, kallon juna suka yi tare da tabe baki, bathroom Junaid ya shiga ya sakar ma kansa warm shower, ya fito daga karshe ya shirya cikin jallabiya duk jikinsa ba kwari ya kwanta har lkcn bae ji xuciyarsa ta dawo dai dai ba. Kiran magrib yasa shi mikewa ya fita xuwa masallaci, Yana dawowa mosque ya shiga part din Mumy, Humainah ce kadae xaune parlor tana kallo, ya xauna fuskarsa daure yace "Mumy fa?" Ta tabe baki ta dauke kai, bae kuma cewa komai ba har Mumy ta fito tace "Har ka dawo" ya shafa kansa a hankali yace "Eh Mumy" tace "ga abincin ka can, na daxu ma baka ci ba sai dawo da shi Humainah tayi" xae yi magana aka bude kofa Sadiya ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana taunar cingam tana kallon Mumy tace "Wae Abba a kira ki!" Mikewa junaid yayi yace "Ke don uwar ki baki iya sallama bane xaki shigo ma mutane parlor kamar dabba" Mumy ta hade rai tace "Ahmad!" Wani mugun kallo yake mata xuciyarsa na tafarfasa, ita ko ta tabe baki ta kauda kai tana murgurda baki, wani tsawa ya mata ya nufeta Mumy ta fixgosa tace "Xan saba maka wllh Ahmad, kana da hankali kuwa" Sadiya tayi tsaki ta fice daga parlon fuu, cikin bacin rai yace "Mumy ko gaisheni fa 'yar iskar nan bata yi a gidan nan yanxu, ni din sa'anta ne" Mumy tace "Sae me don bata gaishe ka ba, uwar me gaisuwarta xae kara maka, ko da can gaishe kan take idan ba gulma ba, kaje an bata maka rai a waje xaka xo ka huce ma mutane a gida, ina raba ka da mutanen nan baka ji koh Ahmad, dole ne sae ka tanka duk abinda suka yi" shiru yayi bae ce komai ba ya koma ya xauna ya rike kansa don shi kansa bai san me yasa yayi hakan ba, he just don't know what came over him, don da can ma ba gaishesa step sis din tasa take ba kuma bai taba ce wa komai ba, Mumy tayi kwafa ta dau hijab dinta ta fita. dawowa kusa da shi Humainah tayi ta xauna kasa a hankali tace "Kayi hakuri ya A.jay, nima daga yau baxan sake gaisheta ba, shikenan na rama maka" kallonta kawae yake bai ce komai ba, sai kuma ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idonsa, ta bata rai tace "Shine ka min shiru koh" ba tare da ya bude idon ba yace "Anki maki maganan, ke din gaishe ni kike?" Mikewa tayi ta take kafarsa ta nufi daki tana cewa "Idan ba sai na gaisheta ba gobe me nake!" ya bude ido da sauri ya bi ta da kallo yana murmushi, Bayan kusan minti talatin Mumy ta dawo parlor, junaid ya mike ya dawo gefenta ya xauna a hankali yace "Kiyi hakuri plss mum I don't know what came over me, baxan sake ba wllh" tace "It's ohk" daga haka bata kuma cewa komai ba shi ma haka, bayan kusan minti goma yace "Mumy fushi kike da ni I know, don Allah kiyi hakuri plss" ta girgixa kai cike da takaici tace "uhn naxari kawae nake ne Ahmad, kaji inda yan gidan nan suka kuma bullowa wae duk me girki shi xae yi girkin gidan gaba daya yanxu, sae kace da can basu suka ce kowa yayi nasa ba, ko me suke nufi da hakan kuma oho" junaid ya d'aga kafada yace "Sai su ci kayansu ai, don ni baxan ci girkinsu ba" daga haka ya mike ya nufi dinning, Mumy tayi murmushi a xuciyarta tace "Ae dama baxan ma bari kaci abinda ya fito daga bangarensu ba idan Allah ya yarda" Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai yafi danganta haka da tausayin baiwar Allahn da yake, Washegari Wednesday bai yi wani breakfast din kirki ba ya fita as early as 7, tun daren jiya El-Ameen ke kiransa baya dauka, a hankali yake driving ya kalli wrist watch dinsa yaga bakwae da minti goma, ganin yana da sauran time yasa shi nufan gidan El-Ameen, a waje yayi parking ya shiga gidan, kwance ya tarda El-Ameen a parlor yana bacci kan 3sitter, Mama kuma na kitchen, ya kusa second ashirin tsaye yana kallonsa sannan ya tabe baki yyi hanyar stairs, a hankali ya tura kofan dakin ya ganta kwance kan gado cikin bargo, ya karasa cikin dakin yana kallon empty roban drip din da aka cire mata, gefenta ya tsaya ya yaye bargon jikinta, ya tsura ma fuskarta ido, Ya fi minti biyu yana kallonta tana bacci, ya daura hannunsa a hankali a forehead dinta ya ji da d'an dumi, bude ido tayi da sauri ta mike xaune, kallonsa take ko kiftawa bata yi, lkci daya ta saki wani kara ta shiga komawa baya tana ihu da karfi, ya koma baya da mamaki yana kallonta, El-Ameen ne ya shigo dakin da sauri, ya tsaya daga bakin kofa ganin Junaid a dakin, sauka tayi daga kan gadon tayi kofa da gudu xata fita tana ihu har lkcn, El-Ameen ya fixgota yace "Keeh Meye haka!" Ihu ta dinga yi xata kwace kanta tana yi tana waigan Junaid, El-Ameen ya kalli Junaid yace "Ohhh it seems Khakin nan naka ke tsoratata fa Captain" Junaid ya juya yana kallon kansa a madubi, farin well ironed navy shirt ne jikinsa, well tucked in cikin navy blue trousers dinsa, sae hat dinsa a kai, sae black socks din dake kafarsa don ya cire takalmin a waje, juyawa yayi ya fice daga dakin, sai a sannan tayi tsit sai dai har lkcn jikinta rawa yake tayi lamo jikin El-Ameen, El-Ameen yayi dariya yace "Toh fah" xaunar da ita yayi gefen gado yana kallonta yace "That's intresting! kina tsoran soldiers kenan!" Kauda kai tayi ta xamo kasa ta kwanta, mikewa yayi yana kallon agogo, da sauri ya fita dakin ya sauko parlor sai dai bai ga junaid ba, ya kalli Mama dake shara yace "Mama junaid din ya tafi ne?" ta washe baki tace "Anya ya tafi, kaga makulli can ya ajiye kan kujera, ashe sojan ruwa ne yau na gansa da khaki" Dariya El-Ameen yayi yace "Ehh Navy ne" tace "Allah sarki, khakin sun masa kyau" kallon Makullin yayi yaga ta motarsa ce, ya d'an tabe baki ya karasa ya dauka yace "D'an rainin wayo" fita yayi don ganin ko motar tasa na waje yaga bbu motar makullin kawai ya kawo masa, girgixa kai yayi ya koma cikin gidan. Junaid na kwance parlor da yamma b4 magrib yana danne dannen waya, khadija ta shigo parlorn, Karasowa tayi ta xauna gefensa tace "Ina yini ya A'jay?" Yace "Lfya lau, kar ma ki fara tambayata kudi don bani da" dariya tayi tace "Kai yayana" sai kuma ta d'an yi shiru, a hankali tace "Kasan me yaya, karka ci abincin gidan nan yau, just go out and get somethin to eat ae kasan yanxu an daina girki daban daban koh" yana kallonta yace "Why!" Ta daga kafada tace "Just, beside ma porridge ne kuma ae bama ka ci" mikewa tayi tace ina xuwa, ta fice daga parlon, ya bi ta da kallo yana murmushi. Wayarsa ne ya soma ring ya duba ya ga El-Ameen ke kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne bai ce komai ba, daga daya bangaren El-Ameen yace "You try fa captain, nine ban san dadin gidanmu ba ko, how on earth xaka dinga bari na ni kadai ina fama da patient din ka?" Junaid ya tabe baki yace "Naga tana tsorona ne, kai ne bata tsoro dat's why I decided not to show up today" El-Ameen yayi tsaki yace "Didn't you see dat uniform dinka ke scare dinta, wear mofty while coming always, yanxu dai I will text u some drugs da xaka siyo idan kana tahowa, and ka siyo mata fruits taki cin abinci" Junaid ya kuma tabe baki ya katse wayar ya ajiye. Kallon agogo yayi yaga an kusa magrib, ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya dau makullin motarsa da Atm sae wayarsa ya fita ya rufe kofarsa. Bangaren Mumy ya fara shiga, yana kallon fatima dake guga yace "Mumy fa?" Tace "tana bayi" juyawa yayi ya tafi masallaci, ana idar da sllh ya dawo gida, Mumy da fitowarta daga kitchen kenan tace "Ga abincin ka a dinning can" kallon dinning din yayi yace "Porridge?" Mumy tace "Shi kake so?" Girgixa mata kai yayi yace "No khadija ce tace min porridge aka yi" Mumy tace "Ehh amma kai na maka girkin ka daban" yace "Toh nagode Mum, but xan d'an fita yanxu idan na dawo xan ci" tace "Fita kuma? Ina xa ka?" Yayi kasa da murya yace "xan d'an raka El-Ameen wani gun ne, daga can xa mu je kallon kwallo" ta tabe baki tace "Xa dai ku je tadi koh?" Dariya yayi yace "A'a fa Mumy" murmushi tayi tace "Toh kar dai ka wuce 8:30 a waje, ka ma shiga gun abbanka kuwa" yace "Ehh daxu na shiga" daga haka ya juya xai fita, Humainah tace "Ya Ahmad xan raka ka" yace " Nooo" daga haka ya fice daga parlon, Mumy tayi dariya tace "Ki bari ran lahadi ya xaga da ke katsina" tayi murmushi tace "Toh Mumy, ko yace A'a kiyi masa masifa sai ya kai ni" sae da junaid ya fara siyan abubuwan da El-Ameen