Sashe 98
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kona masa rai, sai a snn yasan ashe shariya na da ciwo, wani tsawa ya mata yace "Kee!" Dago manyan idonta tayi ta hade rai tana kallonsa can ta mike ta kwabar da cup din tean hannunta ta nufi sama kmr xata tashi sama, bin ta da kallo yyi baki bude, tunda yake shi mace bata taba yi masa haka ba, fasa breakfast din ma yyi gaba daya ya koma sama ya dau wayarsa da car key ya bar gidan. Sai wajen biyar ya dawo gida har lokacin ransa ba dadi, xaune suke parlor tana gyara Humainah gashi, ya wani hade rai yace "Duk ku bar parlon nn Immediately" ba tare da Zahrah ta kallesa ba tana ci gaba da combing gashin Humainah tace "And may we know y?" Karasawa parlon yyi cikin tsawa yace "ku bar min parlor nace" Zahrah ta yatsine fuska ta kwashi kayan gyaran gashin tace "it doesn't call for shouting! Maman baby tashi mu je" Humainah ta tabe baki ta tafi sama, Zahrah ta bi bayanta, xaunawa yyi kan kujera yana tunanin hukuncin da xai dauka kan Zahrah bai taba tunanin shariya da daukan kai na da ciwo ba sai ynxu, ranan ma tare Zahrah ta kwana da Humainah, shi dai bai ce masu komai ba, washegari ya gama shirin fita aiki ya sauko downstairs ya samesu tare suna breakfast, yana kallon Zahrah yace "Royal being, har yanxu bayin na ki basu iso bane ko dama kawai fadi aka yi" ko kallon inda yake bata yi bare ta tanka sai cin potatoe da ketchup dinta take, tsaye yyi yana kallonta, can yace "I can see you are deaf..." mikewa tayi irin ya takurata din nn a fusace ta yi hanyar stairs, bin ta yyi ya fixgota ya hadata da jikinsa kan yace komai cike da tsiwa tace "Me yasa ka fiye takura ne Mr man, get away from my life, i hate disturbance, I don't want...." Bai bari ta kai karshe ba sai jin kiss tayi, Humainah dake kallonsu dama dauke kai tayi ta ci gaba da jujjuya potatoe din gabanta, turata yayi yana mata wani kallo sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri, bin sa da kallo tayi a tsorace, can ta saci kallon Humainah sai kuma ta tafi sama da sauri, Junaid ya kusa minti goma xaune cikin motar kafin ya tada motar ya bar gidan. Har rana Zahrah bata fito ba, wajajen Karfe uku ganin ta fara jin yunwa ta fito daga dakin, bbu kowa parlon ta shiga kitchen ta hada tea ta fito ta dawo sama dai dai lokacin da Humainah ta fito daga dakinta, har Zahrah xata mata magana sai taga ta wani hade rai kmr bata ganta ba ta sauka kasa, Zahrah ta juya ido hade da tabe baki ta shige dakin ta. Da yamma kusan a tare Junaid ya shigo gidan da Hajja, ya wani hade rai ganinta, ita din ma ko amsa gaisuwarsa bata yi ba ta shige parlor tana kwala ma Humainah kira, Humainah dake kwance daki ta fito da sauri jin muryar Hajja, rungumeta tayi cike da jin ddin ganinta, Hajja ta turata tana kallonta daga sama har kasa tace "Ramar meye wnn Humainah, daina baki abinci yyi don yyi aure ko yaya?" Humainah tayi 'yar dariya tace "Ni ba Ramar da nayi Hajja" Hajja ta kalli sama murya can kasa tace "Yar sarkin na sama koh?" Humainah ta gyada mata kai kawai, Hajja ta tabe baki tace "Xata ci ubanta, ko da kuwa shugaban kasa ne uban nata...." Shigowar Junaid ya sa tayi shiru ta balla masa harara, dai dai lokacin da Zahrah ta sauko jin muryar Hajja, hajja ta tsuke fuska sosai, daga inda take tsaye ta gaida ta Hajja ta saki salati tana tafe hannu tace "Yanxu 'yar nn kya gaida Uwar da ta haifi uwar ki a tsaye?" Kallonta kawae Zahrah take, Hajja tace "Toh wnn ba dab'iar arxiki bane, don da Humainah ce ko kaffara baxan yi ba baxa ta yi haka ba, ba fa masarauta kike ba yanxu!" Wani kallo junaid yake ma Hajja don ji yyi kmr ya shaketa, Zahrah ta juya ta koma sama, bin bayanta yayi Hajja tace "Munafuki, hbayaala har ta fara girki ta basa yaci ne?" Humainah dai bata ce komai ba Hajja ta ce "Toh shi ma xae ci uban nasa ne" tsaye Junaid ya ganta gaban mirror, da kmr baxae karasa ba sai kuma ya karasa kusa datace ita, juyo da ita yyi yana kallonta yace "Me yasa kika gaisheta a tsaye!" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, tambayar ya kuma maimaitawa nn ma dai shiru kke ji, a fusace yace "Don me xan dinga maki magana kina share ni" ga mamakinsa har lkcn bata kalli inda yake ba, ya fixgota yace "Wllh na sake maki magana kika share ni I will..." kallon mamaki yake mata ganin bama ta da niyar kallonsa, can ya juya fita. Har dare Hajja bata bar gidan ba tana dakin Humainah, Junaid ya samu Humainah dake kitchen tana xuba ma Hajja abinci yace "Zahrah ta ci abincin?" Bata kallesa ba tace "I don't know!" Ficewa yayi daga kitchen din ya koma sama ya shiga dakinta, xaune ya sameta ya karasa kusa da ita yana kallonta kana ganinta kasan tayi kuka, bai san lokacin da ya durkusa gabanta ba ya kamo hannunta yace "Zahrah!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya matsa hannunta a hankali, sauke idonta tayi kasa, can underneath his breathe yace "My arrogant princess!" Bata dago ba bare tace komai ba, ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Meye amfanin miskilanci da girman kai Jasmine!" *Haske writers association* _Mata-Maza ce Khaleesat Haiydar ba namiji ba_ *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 89..... Zahrah ta kalli cikin idonsa tace "Who's Jasmine?" A hankali yace "You!" Dauke kai tayi ya mike ya dawo gefenta ya xauna yace "Baki bani amsar tambayata ba" shiru tayi bata ce komai ba, matse mata hannu yyi ta wurga masa wani kallo tace "Stop that" yyi d'an murmushi yace "Nasan abinda zan maki ki sauke girman kan nn naki...." Fixge hannunta tayi ta mike ta nufi toilet tace "You can't change who I am, beside you are more arrogant" daga haka ta shige toilet ta rufe, mikewa yyi ya fita daga dakin yana murmushi har lkcn, sai bayan ya fita ya dinga mamakin kansa, then what just came over him, karfe goma saura Zahrah ta shirya cikin kayan bacci ta fita daga dakinta, dakin Humainah ta tura ta shiga, suna xaune kasa ta gansu, Humainah ta daura kanta kan kafar Hajja, magana suke amma suna ganinta suka yi shiru, ko a jikinta ta karasa ta xauna gefen gado ta kalli hajja tace "Sannu da hutawa!" A dakile Hajja tace "Yauwa!" Daga nn Zahrah ta maida dubanta kan tv, Hajja ta kalli Humainah kmr xata yi magana sai kuma tayi shiru ta kyabe baki, Humainah ta d'an kalli Zahrah tace "Abincin ki downstairs" ba tare da Zahrah ta kalleta ba tace "Am not hungry" Hajja ta galla ma Humainah harara ta hade rai, har kusan sha daya Zahrah na dakin ita dai bata ce masu ba suma haka, tun da ta shigo kuma sun ki yin hirar da suke, can dai ta kalli Hajja tace "Sai da safe" da sauri Hajja tace "Ehh Allah ba mu alkhairi" ba sai Hajja ta ga tana kkrin kwanciya kan gado ba, ta yo waje da ido tace "Mai xan gani haka?" Humainah da ta danne dariyar da ya kusa taho mata tace "Nan xata kwanta mana" Zahrah ta kalli Hajja tace "Bacci xan yi a nn" Hajja ta wage baki tana mata kallon mamaki can dai tace "Su wa kika bar ma dakin naki ne" Zahrah tace "A nn nake kwana" Hajja ta kalli Humainah tace "Wai?" Humainah ts gyada mata kai, Zahrah ko tayi kwanciyarta, can dai Hajja ta rufe baki tace "Wai tun da aka kawo ta nn take kwanan maki?" Humainah tace "Uhm" Hajja tace "Tabdi, toh me salubabben yace?" Humainah tayi yar dariya tace "Ba ruwansa" Hajja tace "Toh Allah ya sauwake maku gaba daya" tuni Zahrah ta ja bargo, Hajja da ta kasa daina mamaki tace "Wai meye haka nake gani, to ni ina xan kwanta?" Humainah tace "Ki tafi dakinsa ku kwanta" dai dai nn Junaid ya shigo dakin, yayi mamakin ganin Zahrah kwance dakin, Hajja tace "Yanda yake wawa haka ya samo mata duk wawaye, banda haka ni ko a tarihi ban taba jin kalan abinda nake gani a dakin nn ba, toh shigowa Kayi Kai ma ka kwanta a tsakiyarsu ko ko?" Mikewa Humainah tayi ta dinga dariya, Junaid dai sai kallonta yake don har ya mance rabon da ya ga tana dariya haka, dauke kai yyi yana murmushi can dai ya kalli Hajja yace "Toh yau kinga hakan a gidan Ahmad Junaid" wani kallo ta wurga masa tace "Yi man shiru, gantalalle har kullum wautan yan fari ba cika ka xai yi ba, dama Kai kace ta dinga xuwa kwana nn?" Junaid ya kalli Humainah yace "You leave the room for them nd come to my room" daga haka ya juya ya fita, a fusace Hajja tace "Ka xagi Muhammadu wllh, ke kuma uwar me yace?" Humainah tayi murmushi tace "Yace kije dakinsa ki kwanta" duka take shirin kai mata ta mike da sauri ta fita daga dakin, daga nn bata sake ganin Humainah ba tayi jiran tayi jiran har ta gaji, kwafa Hajja tayi tace "Lallai yaran nn, dakin mijinta ta tafi ashe" kallon Zahrah da tayi bacci tuni kan gado tayi, sai kuma ta fara mamaki, taga dai ko kwana hudu ba ayi da tarewarta tabe baki tayi ganin ta kasa gano komai ta mike ta dau bargo ta shimfida a kasa da pillow, can misalin biyu Zahrah ta farka mikewa xaune tayi ita kadai ce kan gadon, can ta kalli Hajja dake ta sharar bacci a kasa, sauke kafafuwanta kasa tayi ta mike ta xaga inda take ta durkusa ta shiga tada ta, bude ido Hajja tayi tana salati, Zahrah tace "Akwai sanyi kasa meyasa baki hau gado ba" Hajja tace "Kai ai sai jikina yyi ciwo, nn ya ishe ni" Zahrah tace "Toh" mikewa xaune Hajja tayi