← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 104

Sashe 44

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba" bata ce komai ba ya juya kamar munafuki ya fita, a tsatstsaye yayi breakfast ya fita xuwa gaida Abbansa, Hajiya ce parlon tana hada masa breakfast, ya xauna kasa ya gaida Abbansa sannan ya gaisheta, tayi murmushi tace "Lafiya lau Ahmad" ya kusa minti biyar xaune parlon jin Abba bai ce masa komai ba ya mike yayi masa sallama ya fita. Karfe goma saura Junaid ya shirya yayi ma Mumy sallama ya fita, Mumy dai jin sa kawai take da yace ranan xai kawo mata surkarta, yana fita gidan Hajjo ta diro da 'yar Jakarta babu notice. Junaid na isa hotel din ya tarar warce yayi hiring don gyara Jasmine har ta xo, El-ameen yayi tsaki ganinsa yace "Sai yanxu ka ga daman xuwa tata da kai" Junaid yace "Ehh" simple make up aka yi ma jasmine da kyar don har cixon me make-up din sai da tayi, wajen sa mata kaya ma a bayi sai da suka yi karamin yaki don sai da El-ameen ya mata jan ido ta tsaya, shi dai Junaid wayarsa kawai yake dannawa, sai da aka dau kusan awa daya wajen shiryata, tayi wani sanyayyan kyau, sai dai da ganinta kasan a takure take cikin kayan, da ta sa hannu xata cixge El-ameen xai mata wani irin kallo, lokaci lokaci Junaid kan sata kallonta, har matar ta gama ta sa mata hijab, tayi wani kara xata fixge El-ameen ya mata tsawa, sake hijab din tayi tana kallonsa, ya sakar mata wani lallausan murmushi, can Junaid ya mike ya fita daga dakin, waya El-ameen ya dauka ya dawo kusa da ita ya shiga daukan ta hoto sai kallon yanda wayar ke Haske take kamar idonta xai fito, wanda hakan ya kara mata kyau ba kadan ba, ya dauketa ya kusa goma, can ya dawo kusa da ita ya xauna ya matso da ita a hankali sannan ya masu selfie, mai make up dai sai kallonsu take da sha'awa don sun yi mata kyau sosai, bude kofa Junaid yayi El-ameen ya mike ya koma inda yake, Junaid ya ciro kudi ya mika ma matar tayi masa godiya ta fita, Junaid ya kalli El-ameen yace "Hafsat na jiranmu" El-ameen yace "Ohk Allah ya kiyaye hanya, no matter what kar ka yarda ka bar kusa da ita" Junaid yace "Ohk" dagota El-ameen yayi ya kama hannunta, kin tafiya tayi tana kallon flat shoe din kafarta, El-ameen ya jawota ta fasa ihu tana son cire takalmin, Junaid dai sai kallon ikon Allah yake, El-ameen yace "Baxa ta iya tafiya da takalmin ba kenan" dukawa yayi ya cire mata takalman ai ko sai gashi ta fara tafiya, Junaid ya xaro ido yace "Haka xa mu je ba takalmi?" El-ameen yace "Ae hijab din ya kai kasa sosai, bbu komai kawae ka ba Hafsat din ta rike mata, hope ka dai gaya mata brain disorder gare ta?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Tabdi!" Daga haka ya juya ya fita, El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa yana rike da hannunta, kallonsu kawai ake tun daga cikin hotel din har suka fito haraban hotel din, junaid na isa gun motarsa ya juya yana kallonsu, wani mugun faduwa gabansa yayi suna hada ido da ita, ya tsura masu ido su biyun, a hankali take tahowa kamar me tausayin kasa, El-ameen na rike da ita har suka iso gun motar ya bude front seat ya shigar da ita, junaid ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Jikina na bani baxa mu yi nasara ba..." El-ameen ya girgixa kai yace "No! Allah xai daura ka kansu, just pray before going in, nd ka nuna masu ba ta da lafiya ka taho da ita, kaga hakan baxae sa a takurata tayi magana ba, kuma duk me aka ajiye mata kayi saurin dauka ka bude ka bata, if not saukowa kasa xata yi ta xauna ta jawo gabanta, though in TV a kunne yake ma ba lallai ta lura da komai na parlon ba attention dinta gaba daya xata ba Tvn, idan kaga kallon xai yi yawa kawae ka kashe Tvn ma, don't force her on anything don sai ta iya maka ihu" a hankali junaid yace "Ohk!" El-ameen yayi murmushi ya gyada masa kai, juyawa junaid yayi ya bude mota ya shiga ya tada suka bar haraban hotel din, a hanya ya dau Hafsat kamar yanda suka shirya, sai kallonta Hafsat take gaban mota don ita bata ga alamar hauka tare da ita ba, junaid na kallonta ta madubi yace "Bata yi kama da mahaukaciya ba koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba har suka iso gida, a parking lot ya ajiye motar, sai a sannan yaji gabansa na faduwa, ya juya yana kallon Hafsat yace "plss xaki kama hannunta..." Ta yi shiru sai kuma tace "Baxa ta min komai ba" ya gyada mata kai yace "Yea baxata maki komai ba" bude motar yayi ya fito ita ma ta fito, ya xaga xuwa daya side din ya bude ya fito da ita, kalle kalle kawai take idon nan Maa shaa Allah, Hafsat ta kasa karasowa don duk tsoro ya cika ta, Junaid yace "No plss kar ki sa a xargi abu, wllh baxata maki komai ba, xo ki riketa plss" da kyar ta karaso tana kallon Jasmine, yana d'aga kai yaga Umma da Hajiya xaune balcony as usual wani mugun bugu xuciyarsa yayi, ya dauke kai da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa. Hafsat na mika hannu xata rike nata tayi bayan junaid da sauri, kiris ya rage xuciyarsa ya shige cikinsa don yayi xaton ihun nan nata xata yi, ganin yanda su Umma ke ta lekosu yasa kawai ya kama hannunta ya nufi part din Mumy, Hafsat ta bi bayansa da sauri. *Haske Writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 33..... Mikewa Hajiya tayi da sauri tana kallon kafar Jasmine tace "Balki tashi ki ga ikon Allah" da sauri Umma ma ta tashi ta bude baki tana kallon kafarta, a hankali Junaid ya tura kofar parlon ya shiga gabansa na faduwa, babu kowa parlon ya karasa ciki yana rike da hannunta har lokacin ya isa 3 sitter ya xaunar da ita shi ma ya xauna ya kalli Hafsat ya nuna mata gefen jasmine, ta karaso ta xauna suka sa ta tsakiya, kalle kallen parlon kawai jasmine ke yi, yana son xuwa ya sanar ma Mumy xuwansu amma yana tsoron kar ta bi sa, haka suka ta xama parlon, Hafsat dai sai kallonsa take ganin bai da niyar ta shi ya sanar da mutan gidan xuwansu, fatima ce ta fito parlon, ta d'an xaro ido ganinsa tace "Lah Ya Ahmad!" yace "Kira Mumy" kallon Hafsat tayi ta gaida ta, Hafsat ta amsa da murmushi, ta juya tana kallon Jasmine ita ma ta gaida ta, kallonta kawai Jasmine ke yi kmr idonta xa su yi magana, Junaid yace "Leave ki je kiyi abinda na sa ki" juyawa tayi ya bar parlon tana mamakin abinda yasa taki amsa gaisuwarta, Junaid ya kalli Hafsat da sauri yace "Tana fitowa sai ki gaisheta duk me xata ce kiyi ta bata amsa kawai" Hafsat ta gyada masa kai, ba a dau lokaci ba Mumy ta fito parlon, kwata kwata bata dauka da gaske Junaid yake ba, murmushi dauke fuskarta ta karaso tana kallonsu ta xauna tace "Sannun ku da xuwa" Hafsat tace "Yauwa Mama ina yini" tace "Lafiya lau, ya hanya" Hafsat tayi kasa da kai tace "Alhmdllh," ganin hankalin Mumy na kan Hafsat Junaid yyi saurin cewa "Tana gaishe ki Mumy" ya fadi hakan yana nuna Jasmine, Mumy ta kalli Jasmine don ita dai bata ji tace komai ba, ta dai yi murmushi tace "Lafiya lau, sannun ku da xuwa" Hafsat tayi saurin cewa "Yauwa Mama" Mumy ta kira fatima ta fito tace "Dauko masu ruwa fatima" kitchen ta shiga ta fito da tray ta nufi fridge ta bude ta fiddo ruwa da drink ta dawo parlon, kusa da Jasmine ta ajiye tray din ta kuma komawa kitchen ta dawo da snacks, Jasmine ta kalli Junaid da gabansa ke ta faduwa ta fara kokarin sauka kasa ai da sauri ya riketa yanda bbu wanda xai lura, ya jawo remote yayi powering tv, tvn na kawowa ta koma ta xauna tana kallo, sallaman su Umma da Hajiya yasa xuciyarsa kusan shigewa cikinsa, suka karaso parlon su Suhaima na biye da su a baya ko warce da murmushinta a fuska, Hajiya tace "Ashe bakuwar har ta iso ko a sanar da mu, sannun ku da xuwa," Mumy tace "Ae kuwa, da wai idan sun tashi tafiya xa su shiga su gaida ku" Umma tace "Allah sarki" Hafsat tace "Ina yinin ku" suka amsa mata a tare, Mumy dai sai kallon mamaki take ma jasmine dake ta kallo kamar her life depend on it ganin bata gaida su ba, Junaid ya lura da hakan hankalinsa ya tashi ba kadan ba, su kansu su Umma kallonta suke, Hajiya tace "Toh wai wacece surkuwar ta mu a ciki" Junaid na shirin cewa Hafsat ce, Hafsat ta riga sa ta hanyar nuna masu jasmine, ya xaro ido don shkkn tasa ta samesa, Umma tace "Ikon Allah, sannu Amaryar mu" nan ma dai ko dagowa Jasmine bata yi ba idonta na kan TV, Hajiya tace "Toh fah, anya amaryar nan na jin mu kuwa" Hafsat tayi saurin cewa "ba ma ta jin dadi ne muka fito..." Umma tace "Ikon Allah, ana burin auren lafiyayya shi kuma ra'ayinsa kenan bawan Allah, Allah sarki naga ma kamar ciwo gareta a kafa don bbu takalma ku ka shigo" lumshe ido Junaid yayi a hankali ya bude, shi kam ya shiga uku da matan ubansa, Mumy dai bata tanka su ba ta kalli fatima tace "Xubo masu abinci fatima" Guri Hajiya ta nema ta xauna tana cewa "Tun da baki gare mu bari mu xauna" Junaid ya watsa mata wani kallo ta gefen ido, Umma ma ta xauna tana cewa "Toh baxa a kai ta gun Hajja ba tun da tana nan..." Gaban Junaid yayi wani mugun faduwa jin sunan warce ta kira, Mumy tace "Xa su je" Hajiya tace "Ya kamata kam, ai da mun san da xuwansu da ko 'yar girki ne mun yi" kallonsu kawai Hafsat take ko ba a gaya mata ba tasan matan
Chapter 44 · 0% Book details