Sashe 80
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
murya yace "Fatima!" Rungumesa tayi sosai, hawaye na sakko mata tace "Abba kila su Umma basu gane ni bane koh?" Kasa ce mata komai yayi, El-ameen dai sai kallonsa yake yaji tausayinsa ba kadan ba, dago kai sarkin yayi yana kallonsa, mikewa yayi ya karasa inda suke ya sunkuyar da kai yace "Barka dai mai martaba, ga Zahrah na maido gida, Allah ya kiyaye gaba" kallonsa kawai sarkin yake, El-ameen yace "Na bar ku lafiya" juyawa Zahrah tayi tana kallonsa, Sarki ya taka ya isa har gabansa, hannunsa ya kama ya nufi fada da shi, tsaye duk occupant din masauratan suke ko wanne a tsorace, Mai martaba da har lokacin bai sake El-ameen ba ya nufi babban parlonsa da shi, Zahrah dai na biye da shi a baya kamar xata shige jikinsa ganin wani kallo da ake mata duk inda suka wuce, xaunawa sarki yayi ya nuna ma El-ameen kujera ya xauna, ya kusa minti biyar bai ce komai ba, Zahrah dake xaune kusa da Abban ta sai jiran jin me xai ce take, hawaye ne ya sakko idonta tunawa da tayi da irin kallon da ake mata, ta daura kanta kan kafar Abban nata muryarta na rawa tace "Abba na canxa ne wai, me yasa ake guduna?" Da kyar me martaba ya saita kansa, yana rike da hannunta yace "Baki canja ba mamata" kallon El-ameen yayi yace "Bawan Allah, a ina ka ga Fatima?" Shiru El-ameen yayi kamar baxae ce komai ba, sarki dai sai kallonsa yake, sunkuyar da kai yayi yace "Bani na ganta ba ranka ya dade...." Sarki yace "Waye shi?" Dago kai yayi yace "Aminina ne, shi ne silar komai" Sarki yace "Kana da masaniyar inda ya ganta, kuma yana ina?" El-ameen yace "Ehh nasan inda ya ganta, yana katsina yanxu haka,!" Sarki yace "Ina ya ganta" kallonta El-ameen yayi yaga yanda ta kafa masa ido tana jiran jin me xai ce, lumshe ido yayi ya bude ya kalli Sarkin yace "Tana da matsala ne a lokacin" sarkin yace "Wani irin matsala?" El-ameen yace "Ehh toh, A lokacin ta samu matsalar kwakwalwa" mikewa tayi tana kallon El-ameen, sarkin ma kallonsa yake ko kiftawa bai yi, da kyar yace "Matsalar kwakwalwa?" El-ameen ya gyada kai yace "ehh, Ban mancewa dawowarsa Egypt kenan ya taso xae xo guna da yamma ya ganta gefen titi a halin Hauka....." Labarin yanda Junaid ya ganta, da irin tausayinta da yaji El-ameen ya shiga ba sarkin, bai boye masa komai ba har lokacin da junaid din ya nemi shi ma ya taimaka ya nuna shi bbu ruwansa, da yanda dai ya amince daga karshe, kuma bbu abinda ya rage tun daga hidimar da Junaid yayi da ita na Magani abinci sutura, nemo me kula da ita da yayi, har da irin matsalar da ya shiga gun iyayensa ta dalilin ta, da challenges din rayuwa da ya dinga fuskanta, duk da haka kuma bai taba gujenta ba, bai kuma fasa yi mata duk abubuwan da ya dace ba, har gidansu da ya kaita da niyar aurenta lokacin da iyayensa suka takurasa yayi aure, da dai yanda abubuwa suka gudana a lokacin, hatsarin da suka yi da ya maido mata da hankali sai dai kuma tayi loosing memory, da aurensa da Humainah da sakinta da yayi kan Zahrahn, kai bbu abinda ya boye ma sarkin har xuwansu bauchi sai dai bai fadi tijaran da Zaharar tayi masa ba, rike kai sarkin yayi don tuni idonsa ya canxa launi, Zahrah kam hawaye ne kawai ke saukowa idonta jikinta yayi mugun sanyi, tuni ta kasa ci gaba da tsayuwa ta durkushe wajen ta fashe da kuka sosai, da kyar sarkin ya iya dago kansa daga karshe, ya goge idonsa da Handkerchief din hannunsa cike da karfin hali yace "Shekara daya da watanni biyar kenan rabon mu da fatima, tun da suka yi hatsari a hanyar Kano, and....." Kasa ci gaba yayi ya mike yace "Gobe da safe xa mu tafi katsinan" daga haka ya dau hanyar da xai sada sa da Bedroom dinsa, kallon El-ameen kawae take, can ta mike a hankali ta isa gabansa ta durkusa wasu sabbin hawayen na sauko mata cikin sanyin murya tace "Will he ever forgive me?" Kallonta El-ameen yake, yayi murmushi bai ce komai ba, ta fashe da kuka sosai tace "Don Allah ka gaya min xae iya yafe min....." Saukowa El-ameen yayi yace "He will in'sha Allah" tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "toh Meye sunansa?" Yana kallon kwayar idonta yace *Captain Ahmad Junaid* a hankali tace "Ahmad Junaid" gyada mata kai yayi yana murmushi ta sauke idonta kasa. *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 75..... Washegari da ya kasance litinin misalin karfe takwas na safe Zahrah ta fito daga part din mai martaba bayan ya bata umarnin da ta tafi ta gaida Ummanta da stepmum dinta kilishi, bata yarda ta kwana ko ina ba sai gun sa tunda shi kadai ne bai gujeta ba, kuma ga bakin da suka dinga tururuwan xuwa ganinta tun a daren jiyan hakan yasa tayi xamanta gun Abbanta, a nan part din nasa tayi shiryawarta ta saka kayan da jakadiyar Umma ta kawo mata da safen, bangaren Ummanta ta nufa fuskarta rufe da hular alkyabbar jikinta don bata son kallon da ake mata, xuciyarta fal tunanin Junaid ta dinga tafiya a hankali, ta rasa dalilin da ya tsaya mata a rai haka, har mafarkinsa sae da tayi daren jiya, gashi ko ganesa ta tabbatar baxa tayi a hanya ba da xa su hadu, bata damu da mutanen da ta dinga wucewa ba wasu na gaisheta wasu na mata sannu da xuwa har ta iso bangaren Umma, xaune ta sameta parlor ga baki da dama xaxxaune parlon, da ganinta kasan har lokacin bata yi recover daga shock din jiya ba, a sanyaye Zahrah ta karasa har tsakar parlon ta duka ta gaida mutanen dake ta kallonta ko wannensu ya amsa mata cike da fara'a, karasawa tayi gaban Ummanta ita ma ta gaisheta, amsa mata tayi cikin sanyin murya tana kallonta, kasa ci gaba da tsayawa gun Zahrah tayi, ganin Umma taki sakewa da ita, ta mike kawai ta fice hawaye cike idonta, bangaren Kilishi ta nufa nan ma baki ta samu fal a parlon, ba laifi kilishi ta ja ta jikinta hawaye na sakko mata tace "Sannu Zahrah, Allah ubangiji ya kara mana tsawon rai mai amfani...." Rungumeta Zahrah tayi tana kuka, nan ta dinga lallashinta tace "Gode ma Allah xatayi da bawan Allahn da ta dalilin sa ta dawo gida yanxu" jikinta ya kuma yin sanyi sosai ta ji banda taga junaid bbu abinda ke damunta yanxu, mikewa tayi tana share hawayen ta, Ummi ta gani tsaye ita ma tana hawayen, da sauri ummin ta karaso ta rungumeta tace "I missed you sweet sis...." Zahrah bata iya cewa komai ba sae hawaye, janye jikinta tayi ta fita daga parlon, a hanya ta hadu da yayanta tana ganinsa xata canxa hanya ya janyota ya rungumeta, rufe fuskarta tayi a kirjinsa, a sanyaye yace "Welcome back Lil sis, ba gudun ki muke ba, it's just....." Girgixa kai yayi lokaci daya idonsa ya kada yace "We missed you Zahrah" bata iya ta ce komai ba sai kai da ta gyada masa kawai, yace "Baki je gun bakon da ku ka xo tare ba" goge fuskarta tayi tace "yanxu xan je" saketa yayi yace "Yea ki tafi yanxu, nima daga can nake" gyada masa kai tayi ta nufi bangaren saukan baki inda El-ameen yake, Xaune ta gansa parlor yana waya, ta nemi gefe ta xauna sai kallonsa take, yana gama wayar tayi saurin dauke idonta daga kansa, ya d'an bude ido yace "Good morning princess" d'an murmushi tayi tace "Good morning" yana murmushin shi ma yace "How you!" Ba tare da ta kallesa ba tace "Am good," yace 'Happy to be home ryt?" Lumshe ido tayi ta bude ta gyada masa kai, yace "My wife said I shud send her regards" kallonsa tayi tana murmushi tace "Am grateful" yace "In the next 1hr xa mu kama hanyar katsina" da sauri tace "Amma ai da ni xa a je koh?" Yace "No I don't think so...." Bata fuska tayi tace "Nima nace xan je" dariya yayi yace "Ohk ohk!" Shiru tayi sai kuma tace "Nuna min hoton matar ka" da mamaki ya kalleta yace "Really" bai jira cewarta ba ya dauko wayarsa ya bude ya shiga gallery ya nemo hoton Hafsat ya mika mata, mikewa tayi ta karasa kusa da shi ta karbi wayar ta dawo ta xauna, kallonta kawai take sannan ta kallesa tace "She's... She's beautiful!" Murmushi yayi yace "Ohh tnxx" kallon hotunan ta shiga yi, can ta mike da sauri tace "Ohh this is me" mikewa yayi ya koma kusa da ita yana kallon wayar ya ga hoto ne da yayi masu ita da Hafsat, gyada mata kai yayi yace "Yea, ke da Hafsat" a sanyaye ta ci gaba da kallon hotunan taga duk hotunanta ya fi yawa a wayar, ajiye wayar tayi ta koma ta xauna ta lumshe ido, yana kallonta yace "What?" Bude ido tayi ta girgixa masa kai cikin sanyin murya tace "Have you taken breakfast?" Gyada mata kai yayi yace "Yea" bata kuma cewa komai ba can kuma tace "Ban san sunanka ba!" Wara ido yayi yace "I am El-ameen Ahmad..." Gyada kai tayi tace "You have the name of my dad" murmushi yayi yana kallonta, ta mike tace "Xan je gun Abba yanxu" bin ta yayi da kallo har ta fita. Karfe goma saura sarki da tawagarsa suka shirya tsaf domin tafiya kt, shiga ce yayi na alfarma irin ta sarauta, da farko bai amince Zahrah ta bi su ba sbda b'akin dake ta xuwa masarautan dominta amma yayanta na sa baki sarki ya amince su je tare, don har da shi xa'a, rungume yayan nata tayi tace "Thanks bro" Ummanta ta tafi tayi ma sallama sai a sannan Umma ta rungume 'yar tata ta fashe da kuka, jikin Zahrah yayi sanyi ita ma hawayen ya shiga sakko mata da kyar ta fita daga dakin ta je yi ma step mum dinta sallama, Ummi ta gani ita ma ta shirya tsaf, Ummi na ganinta tace "Zahrah tare xa mu je