← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 104

Sashe 83

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ja motar suka dau hanyar fita daga layin. Tuni su Abba suka shiga gida, Hajja dai har lokacin bata fasa daga ma motocin da har sun bar layin hannu ba baki a wangale, El-ameen yace "Toh ae sai ki sauke hannun haka" juyowa tayi da sauri tace "Kaga ikon Allah ko Aminu, ashe dama tsinannun matan Muhammadu ne ke tare mana hanyar arxiki a gidan nan, yo gashi suna barin gidan sai ga sarki sukutum ya kwaso kafafuwa ya xo ganin jikana...." El-ameen yayi dariya yace "Toh jikan naki dai ba mutumin kirki bane don walakanci ya ma yarinyar daga ta bi sa tayi masa godiya kin dai san hali..." Tsuke fuska tayi ta kalli Junaid dake tsaye da sauri tace "Wato don ubanka ni xaka ma bakin ciki koh? Toh Allah ya isa idan aka hanani kujerun makka nah, kai baka yi murnar ta dalilin ka sarki ya shigo gidan ubanka ba, kasan alkhairin da yake shirin yi ma xuri'ar mu.... Ka xata sarauta abar wasa ce... Toh gobe gobe ka shirya mu je ka bata hakuri, kasan alkhairin da ubanta ke shirin maka...." Junaid da takaici ya ishe sa yace "Bana bukatar komansu don ni sbda Allah nayi, mahaifina na da rufin asiri dai dai gwargwado, nima ina da nawa rufin asirin don haka babu abinsu da xae rude ni, ke dai ki je a kai ki makkan....." Bude baki Hajja tayi tana kallonsa cike da masifa can ta gyada kai tace "Shegiya nake idan ban je na ce ma Ubanka mari ka sharara mata ba" daga haka ta shige gate fuu, El-ameen ya fashe da dariya, junaid ya hade rai sosai yace "Ka bar min irin wannan abun Ahmad bana so" El-ameen ya tabe baki yace "Haka kawai mutum ya daura ma kansa wani hali da baxai fishesa ba a rayuwa, to riban me ka ci don ka walakantata Ahmad, ka dai san tafi karfin ka...." A fusace Junaid yace "Ni dai na fi karfinta don bata ma gabana, don Allah nayi abinda nayi" dariya El-ameen yayi yace "Shi yasa naga ka dage sai satan kallonta kake...." Daga haka ya daga kafa ya shiga gidan ya bar sa nan tsaye. *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By khaleesat Haiydar_ 78..... Ranan laraba da safe misalin goma su Junaid suka yi set off din xuwa bauchi sai dai ta plane don yace baxae iya xaman mota ba, shi ma din ba karamin takurasa Abba yayi ba kafin ya amince xai je don da ca yayi shi baxae je ba don sbda Allah yayi abinda yayi, xuwa lokacin dae ba laifi Mumy na amsa gaisuwarsa sae dai ba kamar da ba hakan yasa duk ya ji ba dadi, tun ranan litinin yake gidan, ko yaje aiki nan yake dawowa da yamma, tausayin Humainah yake sosai hakan yasa ko da yaushe yana kusa da ita, part dinsa ya mayar da ita daga karshe ita dai Mumy nata ido, duk da luran da yayi su Umma basa gidan haka ma Suhaima da Muhibba ko sau daya bai taba tambayar inda suke ba, harkokin gabansa kawai yake, Hajja dake ta shiri tun daga ranan litinin din tana jiran ranan jumma'a da Abba yace za su je bauchi da su Junaid bata san har sun tafi ba safiyar laraban, suna cikin taxi da xai kai su Airport wayar El-ameen ya fara ringing, cirowa yayi yaga Aliyu ne ke kiransa, shi har ya ma mance da shi, d'an murmushi yayi ya daga kiran, daga daya bangaren Aliyu yace "Masu Jasmine/jewel/baby!" Murmushi El-ameen yayi yace "Yea, mara mutunci da abokina bai dawo sense dinsa ba sai dai ka ga sammaci wllh" dariya Aliyu yayi yace "Ae nasan ya dawo ne, bayan ka xo ka dauketa ka mayar masa ae magana ta kare" El-ameen yace "Exactly, kuma albishirin ka, ita ma ta dawo, ka dai gane me nake nufi..." Aliyu yace "Ohh really, dama na ga alama soon xata dawo.... But what brought her back!" El-ameen yace "That's a long story, yanxu ina hanyar bauchi ne" Aliyu yace "me xaka yi bauchi" El-ameen ya saci kallon junaid dake kallonsa yace "Ohk! Let's chat!" Daga haka ya katse wayar, wani uban tsaki Junaid ya ja ya dauke kansa, El-ameen yayi dariya, junaid bai kuma kallon inda yake ba har suka isa airport. sha daya suka sauka bauchi, El-ameen ya tare masu taxi duk suka shiga baya ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Sai a sannan ya juya yana kallon junaid yace "ka cika umarnin da sarki ya baka kuwa?" Junaid ya kallesa yana jiran jin umarnin me, ganin El-ameen bai kuma cewa komai ba har bayan kusan minti biyar yace "Wani umarnin?" El-ameen yace "Ashe kana da baki" dauke kai Junaid yyi, El-ameen yace "Na mayar da Humainah da yace kayi!" Shiru Junaid yayi masa na kusan minti sha biyar kafin ya juya ya kallesa yace "Ehh" ko kallonsa El-ameen bai yi ba idonsa na kan titi, murmushi Junaid yayi ya shafa kai, sha biyu saura suka isa masarautan, El-ameen ya fito daga taxin haka ma Junaid dake bin ko ina da kallo, Kudi El-ameen ya ciro ya ba mai taxin sannan ya nufi Entrance din masarautan junaid ya bi bayansa, gaba dayansu dakakkiyar Shadda ce jikinsu, shi El-ameen ruwan hoda, shi kuma junaid fari, yana biye da shi ne yana danna waya, tafiya sosai suka yi kafin su iso main Entrance din da xai kai su har palace din, fixgosa Junaid yayi ganin tafiyarsa kawai yake yace "Meye xaka wani dinga wucewa kana kyaleni a baya, ko na ce ma nasan hanya ne" kallon mamaki El-ameen yayi masa kafin ya duka yace "To hau!" Junaid bai san lokacin da ya fara dariya ba yace "Ka ji dan iska, kai har xaka iya goya ni?" Murmushi El-ameen yayi ya mike don ko ba komai ya sa shi dariya baxae shiga yana murtuke ma mutane fuska ba, a tare suka jera suna tafiya, Junaid yace "Wani disc ne na gani daxu a hannun ka a plane" El-ameen yace "Na ban mamaki ne" Abdul dake tsaye da abokansa biyu gun mota da alamar xa su fita ne ya hangosu ya karaso da sauri yace "Ohh baki gare mu haka... Welcome to you guyz, sannun ku da xuwa" hannu ya basu gaba daya biyun sannan yayi masu jagora har xuwa fada, ganin Abbansa na da baki ya nufi part dinsa da su, suna shiga parlonsa Junaid ya nemi gu ya xauna ya cire hular kansa, Abdul yace "Amma flight ku ka biyo koh?" El-ameen yace "Eh my oga at the top yace bai iya xaman mota ba sbda kura" dariya Abdul yayi yana kallon Junaid, junaid yayi murmushi yace "Manta da shi basir gare sa bai iya xaman mota shi yasa muka biyo jirgi" dariya suka dinga yi gaba daya, El-ameen ya jefa masa hular kansa yace "Kaji sharri...." Drinks kala kala da kayan marmari Abdul ya dire masu ya xauna yace "Toh ya mutan gidan, ya muka baro ku?" El-ameen ne kadai ya amsa don shi junaid kallonsa kawai yake ganin ba kaman wasa suke da kanwarsa ba, waya Abdul ya dauka ya ce bari in kira maku mutuniyar ku gaisa kafin Abba ya sallami b'akinsa, yana kara wayar a kunne bayan ta daga yace "Lil sis, ki taho ina jiran ki part dina" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon, wani alkybba dake daukar ido ne jikinta har yana jan kasa, shi kansa takalmin kafarta abun kallo ne, hular kanta ya rufe kusan rabin fuskarta, tana ganin mutane xaune parlon ta turo baki ta nufi bedroom don ta gaji da gaishe gaishe, Abdul yace "Ina kuma xa ki bakin ki ne fa" daga kai tayi da sauri ta maida hular saman kanta, ido hudu suka yi da junaid ya kasa dauke idonsa kanta, tayi saurin kauda idonta ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma ko kiftawa babu, wani kyalli take gaba dayanta, tayi wani kyau na musamman duk da ba make-up bane fuskarta, murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta karasa gun El-ameen ta durkusa nan kasa cikin sanyayyen muryarta tace "Welcome!" Kai kawai ya iya gyada mata, Abdul kuma yayi excusing kansa ya fita, da kyar El-ameen ya samo abun cewa yace "Ya gidan, ya su mama!" Ta langwabar da kai tace "Taso mu je ku gaisa da su" Junaid dai danna wayarsa kawai yake, El-ameen yace "Baku gaisa da captain ba?" Gefenta ta d'an kalla tace "Ohk, sannu da xuwa" daga haka ta mike tace "Mu je gun Ummata" mikewa El-ameen yayi ya dau Apple daya ya kalli junaid yace "taso mu je muyi gaisuwa frnd" junaid yi yayi kamar bai ji sa ba, Zahrah tuni ta nufi kofa ta fita abunta, warce wayar El-ameen yayi yace "kaga ka ajiye halin nan naka aside har mu bar garin nan, in girman kai ne da ji da kai toh gidansa ka xo, bbu wanda xaka nuna ma a nan sai dai ma ka kara course wajen su" mikewa junaid yayi yace "Dama don ku ci min mutunci yasa kuka dage sai na xo garin nan, how dare her xata shigo ta ki gaisheni tana min kallon rainin wayo, da ana rubuta hali a goshi wllh da ban fara ko da kallon inda take ba bare har na tausaya mata" yar dariya El-ameen yayi yace "Yau kuma ba don Allah kayi ba kenan......" Wani tafarfasa xuciyar junaid yake, El-ameen ya tabe baki yace "If you like kar ka fito muyi me ya kawo mu bar garin nan" daga haka yayi ficewarsa ya barsa gun tsaye, tsaye ya ga Zahrahn tana jiransu ga dukkan alama taji abinda suka ce, murmushi ya mata yana fatan Allah yasa ba jin dai tayi ba. Ta mayar masa da murmushin tayi gaba tana cewa "Kila yana da matsalar kunne ne, shi ya hanasa jin sannun da nayi masa," da sauri El-ameen ya kalli bayansa ya ga ko yana gun, ya ga ko fitowa bai yi ba, can ko sai ga shi ya fito, Tana gaba El-ameen na biye da ita a baya shi kuma junaid na bayan El-ameen, bangaren Kilishi ta fara kai su, sosai tayi
Chapter 83 · 0% Book details