Sashe 63
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
to me" junaid yace "Toh tashi mu je mu samu ummin sai mu tambayeta" El-ameen yace "A'a ni baxan je ba, wannan Kanwar Abban nawa na ciki" mikewa Junaid yayi ya shiga gidan, Small mum din El-ameen ce xaune parlon da Ummi, Ummi ta hade rai ganinsa ya d'an shafa kai ya karaso ya xauna kasa kusa da Ummi ya gaida ta ta amsa bbu yabo bbu fallasa, ya gaida Anty dake parlon ita ma ta amsa masa haka, yana shafa kai yace "Ummi mu fa bamu san kayan me ake cewa ba" Anty tace "Eh ai baxa ku sani ba munafukai, irin yanda aka maka haka xa a masa shi ma kwanan nan" ko kallonta Junaid bai yi ba ya kalli Ummi ya marairaice yace "Allah Ummi ba mu sani ba" Ummi tace "kayan auren mutum ku ke hadawa a boye ko na me" junaid ya xaro ido yace "Kayan aure kuma Ummi, wani kayan auren?" Ummi ta tabe baki tace "Na sha gaya masa yanda aka yi maka a gida haka shi ma xa a masa yan a xaton fadi nake kawai koh, to xaku sha mamaki daga kai har shi" junaid yayi shiru can yyi murmushi yace "toh ayi masa hakan kawai Ummi, don nima ina masa maganan aure baya saurarana, ni ba gashi ina xaune lafiya da matar ba" Ummi tace "To tafi daki ka ga kayan sun yi" junaid ya d'an bude ido yana kallonta, sai kuma ya mike ya nufi bedroom dinta, ko da ya fito dariya kawai yake yace "Wllh sun yi sosai Ummi, Allah ya saka da alkhairi" junaid bai ce ma El El-ameen komai ba da ya fito kawai dariya yake bakin rai, El-ameen yace "Meye haka?" Junaid yace "Nothing, na shawo kan Ummi ta hakura wllh" kallonsa kawai El-ameen yake bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da ya kama ran lahadi Humainah ce tsaye kitchen tana girkin lunch Jasmine na daga bakin kofar kitchen din tsaye duk ta cika ta da surutu ita dai aikinta take ba tare da ta tanka ta ba don da tace ta tafi xata dawo, junaid kuma na sama, danna bell aka yi Jasmine ta xaro ido tace "kila uncle koh Anty?" Humainah bata tanka ta ba ta fita daga kitchen din, jasmine ta bi bayanta da sauri, suka isa gun kofar a tare ta bude, wata yarinya da baxata wuce su ba ce tsaye bakin kofar Humainah sai kallonta take don bata santa ba, yarinyar tayi murmushi tace "Baki san ni ba koh, yi hakuri ruwan sha xa ki ban don Allah, na xo gidan aunt dina ne dake layin nan ne wllh wai ashe jiya da daddare suka yi tafiya da mijinta gashi duk na gaji bbu shagunan siyan ruwa nan kusa" Humainah tace "Ohk, shigo" yarinyar ta shigo tana bin ko ina na parlon da kallo ta samu kujera ta xauna, fridge Humainah taje ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye mata, Yarinyar ta mata godiya tana murmushi Humainah ta koma kitchen, kallon Jasmine da ta xauna kasa kusa da ita tana kallonta yarinyar tayi tace "Sannu ya sunan ki?" Jasmine ta d'an wara ido tace "Uncle na kira na jewel, captain na kira na Jasmine, Mamina na kirana Baby" yarinyar dai sai kallonta take, Humainah dake kitchen tana jin su ta tabe baki ta ci gaba da girkinta, yarinyar tace "Waye captain, waye Uncle?" Jasmine xata yi magana suka ji taku stairs, shiru tayi tana kallon stairs din haka ma yarinyar har ya sauko, kallo daya yayi masu ya dauke kai, yarinyar tace "Ina kwana" ya ji bai ji ba ita dai bata sani ba don bai amsa ba ya shiga kitchen ya rufe kofar yana kallon Humainah yace "Wacece ta shigo min gida?" Humainah ta daure fuska tace "Ruwa xata sha" ya wani hade rai yace "Ruwa? Kika san daga inda take maxa fita ki sallameta kar ki sha mamaki" bata tanka sa ba ta ci gaba da girkinta, ya bude kofar ya fice, kallon Jasmine yayi yace "Come here" mikewa tayi ta bi bayansa don stairs ya nufa, yarinyar ta bi su da kallo, fitowa Humainah tayi ta xauna parlor ganin bata ga Jasmine parlon ba ta kalli stairs, yarinyar tace "Nagode kwarai 'yar uwa, ni sunana Hadiza" Humainah tace "Welcome" yarinyar ta mika mata waya tace "Sa min number ki mu dinga xumunci naga kina da kirki" Humainah ta karba ta sa mata number ta mika mata, yarinyar tace "Suna fa?" Humainah ta gaya mata, tace "Allah sarki, amma kishiyar ki ce wannan da na gan ku tare" Girgixa mata kai kawai Humainah tayi, tace "Ayya, to ni xan koma xa mu ke xumunci" har bakin kofa Humainah ta rakata yarinyar sai murmushi take ta fita daga parlon, Humainah ta kulle, ta koma kitchen. Da yamma misalin karfe shidda motar El-ameen ya shigo gidan, Junaid dake daki ya mike yana lekensa ta window don tun ranan basu sake haduwa ba, ko parking din arxiki bai yi ba ya fito da ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, junaid ya fashe da dariya har da kyakyatawa ya sake curtain din ya koma kan gado ya dinga dariya, direct dakinsa El-ameen ya nufa don bbu kowa parlon, kwankwasa kofar yayi junaid ya mike xaune yace "Come in" ya tura kofar ya shiga yana kallon junaid dake ta kokarin danne dariyarsa, junaid ya mike tsaye yace "Ya aka yi na ganka haka besty, me ya faru" xaunawa kan gado El-ameen yayi ya rike kai, Junaid ya xauna gefensa yace "Talk to me mana" El-ameen ya dago da kyar yace "Kaga abinda su ummi ke shirin min sai kace wani mace, wllh not me" junaid yace "Me xa a maka?" El-ameen yace "Wai aure!" Junaid ya xaro ido sai kuma ya fashe da dariya El-ameen ya mike yana kallonsa, yayi mai isan sa sannan yace "Nima haka ka min" kofa El-ameen ya nufa junaid ya rikosa da sauri yana dariya yace "Wllh ramawa na yi nima haka fa ka min" da kyar ya lallaba El-ameen ya xauna, sannan yace "Toh kai yanxu kana da warce kake so ne da har xaka damu kanka, ba gashi nima haka aka min ba kuma ina xaune lafiya?" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Ni ina da warce nake so" junaid yace "To wacece?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Baby!" Kallonsa junaid ya tsaya yi ko kiftawa bai yi, El-ameen ya mike yace "Kuma ita xan kai masu, in ma basu yarda ba ni sai na aureta don Allah xan iya hallaka warce xa a hada ni da" daga haka ya nufi kofa Junaid ya mike ya fixgosa yace "Wace babyn kake nufi?" El-ameen yace "Warce ke gidan ka" wani kallo Junaid ya watsa masa yace "Sai ka jira randa na maida ta gun iyayenta sai ka bi ta ka aureta, yanxu kam baka isa ba" murmushi El-ameen yayi yace "Koh?" *Haske Writers association* [1/14, 9:18 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 55..... Wani kallo junaid ke masa ya sake sa ya koma baya yace "Yess! Me ya hana ka son auren nata lokacin da take hauka? You can call what ever prize you wish to for giving her your attention and I will pay you" El-ameen bai ce masa komai ba ya gyara kwalar rigar sa ya juya ya fita daga dakin, a stairs suka kusan cin karo da Jasmine, ta koma baya ta wara ido ganinsa tace "Uncle! When did you come" murmushi ya kirkirar mata yace "Am coming" ya bi ta gefenta ya sauka ta bi sa da kallo. Tana jin fitar motarsa ta bata fuska tayi daki da sauri xata fara kuka. Washegari monday Junaid na dawowa masallaci da asuba ya shiga dakin Humainah, ya sameta xaune kan darduma daga bakin kofar ya tsaya yace "You are resuming school today" tace "Na sani" juyawa yayi ya fita, ya bude dakin Jasmine, kwance ya ganta tana bacci cikin bargo ya cire bargon ta mike xaune da sauri yace "Tashi kiyi sallah, after that you brush ur teeth nd take ur bath" daga haka ya juya ya fita ya koma dakinsa, wanka Humainah tayi ta gyara bedroom dinta ta fito parlor nan ma ta share sannan ta shiga kitchen, ruwan lipton ta daura ta xuba kayan kamshi sannan ta fara peel din potatoe. Karfe bakwai saura junaid ya fito daga bedroom sanye da uniform dinsa don ranan sati biyun da ya dauka gun aiki ya cika, kitchen ya tafi ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Humainah, ta juya tayi masa kallo daya ta dauke kai, yace "Xan yi tafiyata in kyale ki if you are not ready" tace "Toh ai dai ba xaune nake ba" bai ce komai ba ya karasa cikin kitchen din ya dau cup ya hada tea ya fita. Yana xaune parlor har karfe bakwai yayi Humainah ta fito ta wuce sama, can ya mike shi ma ya tafi saman, dakin Jasmine ya bude ya ga ta gama sa kaya yace "Fito ki ci abinci" shiru tayi tana kallonsa daga sama xuwa kasa yace "Baki ji na ne" komawa baya ta shiga yi a hankali har lokacin idonta na kansa sai kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Ni bana son kayan nan captain" ya kalli farin shirt din uniform da navy blue trousers din dake jikinsa yace "Me suka maki kayan" ta kuma fashe wa da kuka tace "I don't like it" wani kallo ya mata ya juya ya fice daga dakin, a hankali ta xauna gefen gado tana xaro ido kamar me son tuna abu, dakinsa ya koma ya dauki wayarsa da hularsa ya fito, dai dai lokacin da Humainah ta fito ita ma rike da cup, bai ko kalleta ba ya sauka downstairs ya dau makullin motarsa, ta bi bayansa tace "Toh baxa ka kai ni makarantar ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kuma gobe am late" daga haka ya fice daga parlon ta bi sa da kallo kamar xata fashe da kuka, ajiye cup din hannunta tayi a parlon ta koma sama hawaye cike idonta. Jasmine na jin fitar motarsa ta sauko ta tafi dining ta debi breakfast dinta ta