Sashe 86
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
turo Baki tace "I still can't believe ma kai ka tsince ni, or are you angry don bance kayi accompanying dina bane" murmushi yayi yace "How will you believe it, tunda ba sani kika yi ba lokacin da kike xuwa in bude maki Zip, in raka ki toilet, kike xuwa bedroom dina daure da towel..... Infact har lokacin da nake taimaka maki idan kina menses....." Xaro ido tayi, tayi wani kara tace "Nooo...." Ya gyada kai yace "Yesss! Har lokacin da......" juyawa tayi da gudu ta bar gun, bai san lokacin da ya fara dariya ba har da xama. Washegari kasa fitowa Zahrah tayi, kenan idan haka ne kila har nakedness dinta ya taba gani, har da kukanta da tayi wnn tunanin, sai da Umma ta bata rai sannan ta mike ta fita xuwa gaida su da safen, hijab tasa tsabar bata jin xata iya kallon junaid, tana shiga parlon ko ta gansa shi kadai xaune yana shan tea, kin dago kanta tayi ta kuma kasa karasawa can bedroom, kallonta kawai yake yana kokarin boye murmushin fuskarsa, juyawa tayi xata fita ya mike tana ganin haka ta kwasa da gudu, wani dariya ya taho masa bai san lokacin da ya fashe da dariyar ba, Abdul da El-ameen suka fito da sauri, buda baki Abdul yayi ganin ashe yana iya dariya haka, El-ameen kam karyar da kai yayi ya rungume hannu yana jinjina abinda ya ba junaid dariya haka, da kyar ya tsaida dariyar ya daga kai yana kallonsu, Abdul yayi murmushi yace "Ohh that's more beautiful of you captain" El-ameen ya tabe baki yace "Ko xa mu iya sanin abinda ya baka dariya haka Ahmad, na tabbata mu sai mun yi fiye da wanda kayi" shafa kai junaid yayi yana murmushi yace "Bana son ku haukace da dariyar just let it" El-ameen ya daga kafada yace "Lallai kam" daga haka ya juya ya koma dakin, Abdul ya karasa ya xauna gefensa yace "Gist me more about ur self captain...." Murmushi junaid yayi yana kallonsa. Karfe sha daya junaid ya gaji da xama don Abdul da El-ameen sun fita, bbu kuma yanda basu yi da shi ya bi su ba yace A'a baxae je ba, suka yi tafiyarsu suka barsa, dama bayan azahar xasu gana da wasu yan uwan mai martaba kafin su kama hanyar kt ranan, mikewa yayi ya fita yana rike da wayarsa, tafiya sosai yayi ya ga wani waje kamar gun shakatawa ga tsuntsaye sai shawagi suke, carpet grass ne shimfide gun, shiga yayi ta wani babban kofa ya dinga tafiya yana bin ko ina na wajen da kallo, wasu kuyangu guda uku ya gani suna tahowa ya bi su da kallo kafin yace "Ana shigowa nan kuwa" a tare suka gyada masa kai, daya daga cikinsu tace "Sai dai Gimbiya na nan ita ma!" Yace "Wace gimbiyar?" Tace "Gimbiya Zahrah" bai ce komai ba yayi gaba abunsa, xaune take ita kadai tana kallon cartoon da laptop din dake ajiye gabanta ta xauna kan kafafuwanta, gefenta kuma bowl ne me dauke da kayan itatuwa, juyawa tayi jin taku bayanta, suna hada ido ta mike da sauri har tana ball da bowl din fruits din gabanta, ta kuma juyawa da shirin gudu tayi karo da laptop dake ajiye, tsallakesa tayi ta bi wani hanyar da gudu, bin ta yayi da kallo kafin ya tabe baki ya xauna ya daga laptop din, ya dau apple daya ya shiga ci ya canxa cartoon din xuwa something meaningful yana kallo yana murmushi. Da yamma misalin hudu da wani abu junaid da El-ameen ne xaune a fadar me martaba dake dauke da mutane da dama tun daga waziri, advisern sarki har xuwa kasa, sannan ga 'yan uwansa da abokan arxiki, kanninsa mata da maza, Abdul na xaune daga gefen Abbansa, Ummi na xaune daga daya bangaren sa, Umma da Kilishi ma duk suna fadan xaune, Zahrah ce karshen shigowa ta nufi gun Ummanta ta xauna gefenta, kallon Junaid kawai sarki yake, can kuma sai ya kalli El-ameen, bayan kusan minti biyu na silence sarki yayi gyaran murya yace "Ahmad!" Dago kai junaid yayi yana kallonsa, Sarki yace "Nasan ba lallai in iya biyan ka abinda ka min ba amma ka fadi duk abinda kake so nan duniya in dai bai saba ma shari'a ba nayi maka alkawarin yi ma shi idan Allah ya yarda," shiru junaid yayi, can ya dago ya kalli Zahrah da idonta ke kansa suna hada ido ta dauke kai, kallon El-ameen yayi yaga wani gu daban yake kallo, can ya girgixa Kai yace "Bana bukatan komai mai martaba, I helped her for Allah's own sake" kallonsa kawai Sarki ke yi, can ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shknn, Allah ya albarkaci rayuwar ka Ahmad" cikin sanyin murya junaid yace Ameen, sarki yayi murmushi ya juya yana kallon El-ameen yace "Kai fa takwara na?" Kallon junaid El-ameen yayi suka hada ido junaid ya sauke kansa kasa, Zahrah ma idonta na kan El-ameen gabanta na faduwa, haka kawai junaid ma ya ji gabansa na faduwa, bayan kusan second ashirin El-ameen yace "Ina son ka min alfarmar bani aurenta, na kuma yi maka alkawarin xan rike ta da amana...." Wani mugun bugu xuciyar junaid yayi, Zahrah kam kallon El-ameen take ko kiftawa babu, Mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido shi ma yayi murmushi yace "Na baka! Xan kuma biya maka sadaki" kallon mamaki duk occupant din palace din ke ma sarki sanin baya magana biyu, El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace "You are blessed in'sha Allah son" El-ameen ya kama hannunsa ya lumshe ido ya kai lips dinsa, mikewa Zahrah tayi hawaye cike idonta ta kalli junaid da yaki dago kai har lokacin tayi ficewarta daga fadan. *Haske Writers association* [3/19, 9:36 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 80...... Ko k'adan Junaid bai kuma gane abubuwan da sarki ke cewa ba a wajen gashi bai yarda ya dago kai ba, mikewar da El-ameen yayi ya sa shi mikewa shi ma, kiran sunansa da ya ji anyi ya sa shi juyawa yaga sarki ne ya kirasa, sarki na kallonsa yace "Allah ya tsare hanya, ina kuma sauraron xuwar kakar ka" da kyar ya iya amsa masa yana kirkirar murmushi sannan ya juya ya fita, tun a hanya ya dake yayi patting shoulder din El-ameen yana murmushin karfin hali yace "Congrat frnd!" Kasa ce masa komai El-ameen yayi yana kallonsa, suna isa part din Abdul junaid bai ko kalli kayayyakin sawan da Abdul ya jido masu a boutique jiya ba, atm dinsa ya dauka da waya xai fita, wani abokin Abdul yace "Baxa ka canxa kaya ba Captain, Abdul din da xai kai ku airport ma bai gama shiri ba" cike da karfin hali junaid yace "Yeah, ina waje nan...." Daga haka ya nufi door, El-ameen dake tsaye ya bi sa da ido, a hanya Junaid ya hadu da Abdul, Abdul yace "A'a ina xa ka captain" junaid ya kirkiri murmushi yace "Ina jiran ku a waje" hannunsa Abdul ya kama yace "Noo baka isa ba, sai ka sake wanka ka canxa kaya" duk yanda Junaid ya so Abdul ya kyalesa kin saurarensa yayi har sai da ya mayar da shi part dinsa, dole yayi wanka ya canxa kaya, duk suka shirya, Abdul ya tafi da su xuwa gun Mum dinsa suka yi mata sallama ta hadasu da turarruka masu tsadan gaske, sannan ya kai su part din Umma, ita kadai ce xaune parlor da jakadiyarta, tana ganinsu ta saki fuska nan suka yi mata sallama ta dinga sa masu albarka, shi dai Junaid kansa na kasa, tsaraba sosai ta hada masu su biyun su kai ma Mum dinsu, El-ameen yayi mata godiya, shi ma junaid da kansa ke kasa yayi godiyar, Abdul yace "Umma ina Zahrahn fah?" Umma tace "Ina jin bacci take" mikewa yayi ya nufi bedroom din Umma, Umma ta bi sa da kallo har ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo Ummi na xaune gefenta tayi tagumi, Abdul ya karasa da sauri yace "What's wrong with her" a hankali Ummi tace "She's just crying, me yasa Abba xai yi mata haka.... In ma haka ne ba sai ya basu kudi me yawa ba, ina jinin sarauta da auren....." Wani kallo ya watsa mata ya cire bargon yana kallon Zahrah, mikewa xaune tayi ta fashe da kuka tana kallonsa, ya xauna yace "Look ki hadiye kukan nan ki min magana, aurensa ne baki so?" Shiru tayi bata ce komai ba sai hawaye, yace "Ki min magana mana" girgixa kai tayi a hankali tace "A'a...." Yace "Baki son auren?" Tana goge fuskarta tace "Ni baxan iya cewa bana so ba, they helped me and...." Ya mike yace "Good you know that! Kina hauka ma duk sun xauna da ke da amana bare aure, yarima kamar ki kike so ko wa?" Girgixa kai tayi yace "to yanxu tashi ki wanke fuska ki taho kuyi sallama da su" mikewa tayi da kyar tayi yanda yace mata ta daura alkyabbarta ta rufe kusan rabin fuskarta ta bi sa suka fita tare da Ummi, sosai Umma taji dadin ganin ta fito don bata yi tunanin xata fito ba a yanda ta dinga kuka, har mota ta rakasu Ummi na rike da hannunta, shi dai Junaid yana gaba sai dai yayi murmushi idan aka ce wani abu, Ummi tace "Ya Abdul mu raka ka airport din plss?" Yace "Alryt mu je" front seat junaid ya bude ya shiga, El-ameen ya koma baya Ummi ta shiga sannan Zahrah, Abdul da Ummi kadai ke hira a motar, daga Zahrah, Junaid har El-ameen bbu me cewa komai, a hankali ta daga alkyabbar fuskarta suka yi ido hudu da Junaid don kallonta yake ta madubi, ta sauke idonta da sauri, suna isa airport junaid ya fita sannan El-ameen, Ummi ma ta sauka, sai da Abdul ya fita sannan Zahrah ma ta fito, karasawa El-ameen yayi kusa da Zahrah ya mika mata wani disc din hannunsa, ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta karba, kallo daya junaid yayi masu ya fara tafiya, Abdul ya bi bayansa haka ma Ummi, da kyar Zahrah tace "What's this?" Ya rungume