← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 104

Sashe 52

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa ta sakin fitsari, dukanta yake kamar an aikosa, ta dinga ihu iya karfinta tana kiran Hajiya da Umma, Dama suna labe balcony, Hajiya ta saki murmushi haka ma Umma a tare suka ce "Alhmdllh" duk suka sauko compound din, sosai suke jin ihun Suhaima, Hajiya ta saki salati da karfi tana kwala ma suhaimar kira tana cewa "ina kike, me ya same ki" Umma ma ta dinga kwalo mata kira duk suka cika tsakar gidan da hayani, su khadija ne suka fara fiffitowa sannan fatima, Hajiya tuni ta nufi part din junaid har lokacin tana kwalo ma Suhaima kira, Abba ne ya fito shi ma jin hayaniya, Ya kalli Umma yace "Meye haka?" Umma tace "Yo ina muka sani Alhaji, ihunta kawai muke ta ji mun rasa inda take" Fitowa Mumy ma tayi jin abinda Umma tace, Tuni Hajiya ta isa kofar junaid ta shiga bubbuga kofar tana kiran Suhaima, bude kofar junaid yayi bayan ya lallasata iya son ransa da belt ya cillota waje ya kulle kofarsa, birgima ta dinga yi tana cewa "Wayyo Hajiyarmu bai sha ba" Hajiya da idanuwanta suka firfito ta dagota da sauri ta toshe bakinta a jikinta tace "Ba kya ji Suhaima kin tsokanesa kenan koh?" Abba ne ya karaso yana kallonsu yace "Meke faruwa ne wai?" Da sauri Hajiya tace "A'a ita ce bata ji Alhaji fitsara tayi masa daxu, mu je kawai maganinta kenan" Abba ya kwalo ma junaid kira Hajiya da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tace "oh Alhaji don ya hukuntata shine wani abu, bata dawowa da wuri ne daga makaranta yayi mata magana tayi masa fitsara shine ya xaneta, ai ni ya min dai dai, mu je kawai Alhaji" Mumy ce ta karaso wajen Hajiya tace "Ohh Amina ku rabu da yaron nan, don ya doketa ya hukuntata shine me... Yanxu da fatima ce ai baxa ki ce komai ba" juyawa kawai Mumy tayi ta bar wajen, Abba ya girgixa kai shima ya koma part dinsa, Sumsum Hajiya ta ja Suhaima da ke kuka tana soshe soshen suka bar wajen, Umma ta hadiye yawu da kyar ita ma tayi part dinta. Wasa wasa har biki ya rage kwana biyu, banda shirye shirye babu abinda ake a gidan kamar irin shi ya zabi matar din nan, tuni 'yan uwa da abokan arxiki aka fara xuwa daga garurruwa daban daban, sai a lokacin Junaid abun ya fara damunsa on like before da lamarin ke basa dariya, babban damuwar tasa rashin sanin wacece iyayen sa suka xaba masa, babu yanda bai yi da Mumy ta gaya masa ba ita ma tace bata sani ba, Tashin hankali gun Umma da Hajiya baya faduwa don sun rasa abun yi, komai suka yi ba nasara ciki gashi basu san wacece shegiyar da xa a aura masa ba don basu ga alamar daya daga 'ya yansu bane, da yammacin ranan Hajja ta diro gidan, magiya junaid ya dinga mata kan ta gaya masa wacece matar tasa tace ubansa yayi kadan balle shi, sosai hankalinsa ya tashi, bayan magrib Abba yasa a kira sa, yana shiga parlon ya xauna Abba yace "Babu wani shirin da za kuyi ku, ko walima ne?" Ya gigixa kai yace "A'a Abba, walimar da xa ayi a nan gida ya isa" Abba yace "Toh shkkn, hakan it's Ohk" ranan kasa bacci junaid yayi har kusan karfe dayan dare, wayarsa ya jawo daga karshe ya shiga neman number Humainah don yasan baxa ta rasa sanin matar ba, har ya gama ringing bata daga ba ya sake kiranta sai gashi ta dauka, cikin sanyin murya yace "Kina ji na Humainah" "Um" kawai tace masa kamar anyi forcing dinta, ya lumshe ido ya bude yace "Plss nasan baxa ki rasa sanin warce xa a aura min ba, ki gaya min wacece plss" taki cewa komai na kusan second talatin har sai da yace "Hello" sannan tace "Ban sani ba nima" yace "Plss" kamar xata yi kuka tace "Ban sani ba," tsaki yayi ya katse wayar ya jefar. Washegari alhamis da asuba yayi shirin fita aiki ya fice ya bar masu gidan, haka ya wuni bai da sukuni ranar, yana barin gun aiki Clinic ya tafi gun El-ameen, da damuwa yace "Frnd har yanxu fa ban san wacece matar nn ba" El-ameen yayi murmushi yace "gobe idan mun kai ka xaka ganta, sbda son da Abba yake maka shi yasa yake son surprising naka" Junaid yace "Plss ka daina bata min rai more, what sort of surprise is this, and what if fitinanniya ce taki yarda da xaman yarinyar a gidan?" El-ameen ya hade rai yace "Sai ka korata nasu gidan don bata xo maka da gida ba, and tana tarewa gobe ita kuma xata tare ran lahadi don ranan Dr Sumayya xa su yi tafiya, tsaf ita ma kuma xa a gyara mata nata dakin" Junaid ya dafe kai yace "Ba haka ba frnd, kasan tana iya xuwa tayi reporting ma su Abba fa" El-ameen yace "Shit, gashi har xa a maka aure gobe baka xama mature person ba, ka ki girma har yanxu junaid, look yanxu you are going to leave a free.... When I say free I mean a free life, no more Mumy Mumy Mumy, you are going to head a family of ur own don haka ko wani decision kayi a gidan ka is right ba sai wanda parent dinka suka maka ba, from tomorrow you will be on ur own" junaid yace "Uhum?" Tsaki El-ameen yayi, can yayi kwafa yace "da rabon matar nan ta rainaka idan ta lura you don't have a say of ur own!" Mikewa Junaid yayi yace "Baka san ni ba kenan" daga haka ya fice daga office din. *Haske writers association* [1/14, 9:15 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 44/45 Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace "Sllh!" Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito daure da towel, gaban mirror ta xauna ta gama shafe shafenta sannan ta shirya cikin Abaya baki da veil dinsa ta d'an gyara fuskarta ta koma gado ta xauna tayi tagumi. Bude kofar dakin aka yi fatima da khadija suka shigo, Humainah ta mike da sauri lokaci daya tayi murmushin jin dadin ganinsu, fatima tace "Uhum Amaryar yayarmu, Antynmu!" Hade rai tayi can ta fashe da kuka tace "Ni ba amaryarsa bace, ai Hajja tace sbda a raba sa da mahaukaciyar nan ne aka aura masa ni, amma da ya rabu da ita sai a sa ya sakeni in ci gaba da karatuna" innocently tayi maganar tana kallonsu, Khadija da fatima suka fashe da dariya barin khadija, juyawa Humainah tayi a sanyaye ta koma gefen gado ta xauna, hade kanta tayi da gwiwa tana kuka, fatima ta karasa kusa da ita da sauri tace "Toh ai ba mu ce ba haka bane ba fa Humainah" Humainah ta girgixa kai tana kuka tace "Ba wani nan nasan wayo aka min baxa a ce ya sakeni ba, yar yarinya da ni xan je ss3 za ayi ma aure bayan ku ba a maku ba....." Khadija ta xauna gefenta tace "Ni dai ba dariya nake maki ba, ba ruwana, ga abinci Mumy tace a kawo maki" Humainah ta dago kanta tana share hawayen idonta tace "Hajja fa?" Khadija tace "Ta ce anjima xata xo" Junaid ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonsu yace "A baki aka ce ku bata abincin?" Kallonsa suka yi gaba daya basu ce komai ba, ya nuna masu kofa duk suka mike, Humainah ta hade rai tana kallonsa tace "Ba yanxu xa su tafi ba toh" Ko kallonta bai yi ba, ganin su fatima sun nufi kofa kamar xata fashe da kuka tace "Don Allah kar ku tafi" murmushi fatima tayi ta raba ta gefen yayan nata ta fita khadija ta bi bayanta, kuka sosai Humainah ta shiga yi, ya karaso cikin dakin ya xauna d'an nesa da ita yace "baki san ke ba yarinya bace yanxu tun da har aka aurar da ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Ni dai yarinya ce" murmushi yayi yace "Toh naji! tsoron xama ke kadai kike a dakin da kike son su xauna da ke?" Ta kallesa hade da gyada masa kai, yace "Toh xan samo maki warce xata dinga taya ki xama ai kina so?" Tana kallonsa tace "Amma babba ce?" Ya girgixa mata kai yace "No yar yarinya ce kamar ki sai ta dinga taya ki xama kuna kwana ma tare" sosai ta hade rai tace "A'a bna so, xan iya xama ni kadai" shiru yayi yana kallonta, can yace "Saboda me?" Ta mike tace "Haka nan kawai, xan iya xama ni kadai abuna" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, lumshe ido yayi ya bude yana naxarin abinda ta ce, Mikewa yayi shima ya fita daga dakin ya koma nasa. Karfe sha biyu saura aka danna bell downstairs, Junaid dake bedroom dinsa yana danne dannen waya ya mike ya fita, dai dai lokacin da Humainah ma ta fito, kallo daya yayi mata ya sauka ya je ya bude kofar, Hajja ce tsaye bakin kofar da Sadiya, ta washe hakora ganin Junaid tace "A'a ango, to gani na biyo ka don kayi amarya sai ka mance da uwar gida?" Juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor, Hajja ta shigo tare da Sadiya da gudu Humainah ta sauko jin muryar Hajja ta rungumeta, Hajja tace "Lalala kinga yanda kika yi kyau kika yi fresh kuwa? Lallai Amadi ya iya kiwo
Chapter 52 · 0% Book details