← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 104

Sashe 55

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana gyada mata kai, ta juya ta ci gaba da wanke plates din, yace "Me xa ki ci for Supper?" Ta juyo tace "Supper?" Ya gyada mata kai yace "Yea dinner" ta d'an langwabar da kai a hankali tace "na koshi" wara ido yayi yace "me kika ci?" juyawa tayi ta ci gaba da wanke wankenta. Har ta gama yana tsaye bakin kofar, ta juyo tana kallonsa, murmushi yayi mata ya fita daga kitchen din ta bi bayansa suka haura sama, yace "Tafi kiyi sllh" kai ta gyada masa ta shiga dakin da take, shi ma ya shiga nasa. Ana idar da sllh ya tafi siyo masu abinci, ajiye abincin yayi a parlor bayan ya dawo ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera, can ya mike ya shiga kitchen ya dauko plate ya dau take away daya ya juye ya sa spoon ya dau ruwa ya tafi sama, xaune ya sameta bakin kofar dakin tana ganinsa ta mike tsaye, yace "uhum!" a hankali tace "Tsoro nake ji" kallonta ya tsaya yi kafin ya shigo dakin ya ajiye mata abincin hannunsa yace "Toh xo ki ci abinci" ta karaso ta xauna inda ya ajiye mata abincin, bin sa da kallo tayi har ya fita sai dai bai rufe mata kofar ba. Har xai shiga dakinsa ya tsaya ya kalli dakin Humainah, karasawa yayi ya bude kofar, xaune ya ganta can karshen gado kanta hade da gwiwa, a hankali ya karasa kusa da ita ya xauna yace "Still crying?" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ya ce "Ina xa ki?" Ta fashe da kuka sosai, rungumeta yayi a hankali yace "Alryt am sorry, kiyi hakuri... She's going tomorrow tun da baki so" boye fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, yace "Toh ba nace kiyi hakuri gobe xata tafi ba" muryarta na rawa tace "Toh wacece ita" dago kanta yayi yana kallonta, can yace "Ohk I will tell who she is" janyeta yayi a jikinsa ya koma baya yana kallonta yace "Amma fa it's a long story" sunkuyar da kanta tayi, nan ya fara bata labarin ynda ya hadu da jasmine har xuwa wannan lokacin, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu bata kuma ce komai ba, ya lumshe ido ya bude yace "Tana regaining memorynta Idan Allah ya yarda xa ta koma gun iyayenta, ita din abun tausayi ce, a yanxu bata da kowa sai mu da muka taimaketa" dauke kai Humainah tayi, ya matso kusa da ita yace "Baki ce komai ba" turo baki tayi tace "Toh ka kai ta gidansu El-ameen mana" murmushi yayi yace "In tambaye ki" ta dago kai tana kallonsa, yace "wai kishi na kike Humainah?" Hade rai tayi tace "Kamar ya? Sbda me xan yi kishin ka" yace "Toh me sa baki son ta xauna nan?" Tabe baki tayi tace "Ta xauna mana ni ina ruwana, kawae abinda na sani ka kai ni sch next week" murmushi yayi ya mike ya fita daga dakin, abinci ya dauko mata ya ajiye dakin yace "Ga abinci!" Ko kallonsa bata yi ba ya fita daga dakin. Karfe tara da wani abu ya mike daga kwancen da yake ya fita xuwa gun Jasmine, xaune ya sameta bakin kofa tayi jigum, ya d'an bude ido yace "kina nan har yanxu" mikewa tsaye tayi kamar xata yi kuka tace "Ni kadai xan yi bacci a nan?" Kallonta kawai yake ya ga hawaye idonta, girgixa mata kai yayi yace "A'a ba ke kadai xaki kwana ba, ina xuwa" daga haka ya fita ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta daure da towel gaban madubi, hade rai tayi tace "Kaya xan sa" yace "Uhm did I hold you?" Marairaice masa tayi tace "Ka fita plss" karasowa yayi kusa da ita ta mike da sauri, ya d'an bude ido yace "what?" Kamar xata yi kuka tace "Ka fita plss" yace "Alryt xan fita, amma abokiyar kwana xan kawo maki" kallonsa tayi da sauri tace "Kamar ya?" Yace "ku kwana tare da yarinyar plss" da mamaki take kallonsa tace "Mu kwana?" Matsowa yayi kusa da ita ta koma baya da sauri tace "Wayyo ya A jay ka fita plss" ya langwabar da kai yace "Toh in kawo maki ita?" Gyada masa kai tayi da sauri, yayi murmushi ya juya ya fita ta bi sa da kallo, tsaye ya samu Jasmine a daki tana ganinsa ta nufesa da sauri ta juya masa baya tace "Cire min abun" kallon Zip din kawai yake daga sama xuwa kasa na kusan minti daya, ta juyo a hankali tana kallonsa, kifta ido yayi da sauri yace "Na'am" a hankali tace "Ban iya cirewa ba, Mami da farida suke cire min" gyada mata kai ya shiga yi kamar kadangare, ta kuma juya masa baya, yayi baya da sauri yace "Ohk Ohk mu je a cire maki nima ban iya ba" daga haka ya nufi kofa ta bi bayansa, dakin Humainah ya shiga ita ma ta shiga, kallonta kawai Humainah ke yi daga sama xuwa kasa gabanta na faduwa, karasawa Jasmine tayi kusa da ita ta juya mata baya a hankali tace "ki cire mun abun" kallon Junaid Humainah tayi, ya gyada mata kai yace "Help her wai bata iya ba" da kyar Humainah ta daga hannu ta xuge mata Zip din, kokarin cire rigar ta shiga yi da sauri Junaid ya juya har yana buge kofa ya fita daga dakin, Jasmine ta kuma kallonta tace "Baki cire dayan ba" Humainah ta balle mata bra din ta koma gaban madubi, bin ta da kallo Jasmine tayi tace "Ina san inyi wanka" ko kallonta Humainah bata yi ba, Jasmine ta bi ta tace "Xan yi wanka" ba tare da Humainah ta kalleta ba ta nuna mata kofar bathroom, Jasmine ta nufi kofar ta bude ta shiga, a bude ta bar kofar, Humainah ta mike ta koma gefen gado ta xauna xuciyarta na bugawa, har Jasmine ta fito daure da towel dinta, ta gefen ido kawai Humainah ke kallonta, ta iso kusa da ita tace "cloth dina" Humainah ta hade rai tace "ki saka wanda kika cire mana" "toh" kawai jasmine tace ta tafi inda kayan da ta cire yake ta dauka ta sa ta kuma dawowa ta durkusa kusa da ita tace "Sa min" xuge mata Zip din Humainah tayi ta kwanta abunta, jasmine ta mike ganin ta kwanta ita ma ta kwanta nan kasa. Junaid na fitowa daga wanka ya dau wayarsa dake ring ya ga El-ameen ne ke kiransa, dagawa yayi El-ameen yace "Matar taka ta hakura dai koh?" Junaid yace "May be" El-ameen yace "Kasan me, bata yarda fa ta kwana ita kadai ya xa ayi gashi amarci ku ke ci...." Junaid yace "Ko kuma angwanci ba" El-ameen yace "Serious xata yi ta maku ihu ne cikin dare bata yarda ta kwanta ita kadai" junaid yace "ta gaya min, tana dakin Humainah yanxu ma" El-ameen yace "Ohk bata waya plss" Junaid yace "Kace mata me?" El-ameen yace "kai dai ka bata" shiru junaid yayi can yace "Naji" katse wayar yayi hade da yin tsaki ya saka jallabiyarsa ya fita daga dakin, da sallama ya tura kofar dakin Humainah ya d'an bude ido ganin jasmine kwance a kasa ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "M e ya sa kika kwanta a nan" shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Humainah ya ga rufe idonta ma tayi, jasmine ya kuma kallo yace "Tashi ki hau gado" mikewa tayi ya nuna mata daya side din gadon ta xaga ta hau ta kwanta, a hankali ta matso kusa da Humainah shi dai kallonta kawai yake, wayar hannunsa ne ya fara ring ya kalli screen din, sai da ya kusa katsewa ya daga ya mika mata, karba tayi tana kallonsa yace "Kiyi magana" wayar ta kai kunnenta tace "Na'am" El-ameen yace "Baki yi bacci ba baby?" Ta kalli Junaid da ke kallonta ta sunkuyar da kai a hankali tace "Xan yi" juyawa junaid yayi ya fice daga dakin, "Kin ci abinci kuwa" tambayar da El-ameen yayi mata kenan ta gyada masa kai tace "Eh da afternoon ya bani wannan small rice da miya, na ci kadan Saboda ba dadi sai ya xo ya bani a baki" shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, Humainah ta bude ido da sauri tana sauraren abinda take cewa gabanta na faduwa, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Da ya baki a bakin sai kika ci?" Kai ta gyada masa tace "Eh da ya bani na ci, uncle he's kind, I like him just like Abba" mijin Dr Sumayya kenan, katse wayar El-ameen yayi, Humainah ta mike xaune xuciyarta na tafarfasa can ta mike ta fice daga dakin, da sauri Jasmine ta mike ta bi bayanta ita ma, dakin Junaid Humainah ta shiga ta gansa tsaye yana saka pyjamas dinsa, juyawa yayi yana kallonta ta xube wajen ta fashe da kuka sosai, karasowa yayi kusa da ita ya durkusa gabanta da mamaki yace "Me ya faru?" Jasmine ce ta shigo dakin ta karasa kusa da su a hankali ta durkusa ita ma tana kallon yanda Humainah ke kuka. [1/14, 9:15 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 48..... Sai kusan Azahar Jasmine ta tashi, tana ganin kofa rufe ta mike da sauri taje ta bude, fitowa Junaid yayi daga bedroom dinsa jin budewar kofar,ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, yace "Kin tashi" ta gyada masa kai ta koma dakin, karasawa ciki yyi yace "Are you hungry?" Ta daga kai ta kallesa tace "ina son in yi girki" yace "girki?" Ta gyada masa kai yace "Uhnn! Toh xo mu je kiyi" gun kayanta ta nufa tace "in sa wani kayan" dariya ta basa ya bi ta da kallo har ta isa gun jakarta ta bude ta fiddo wata yar top fari mara nauyi da wando mai kamar 3qtr pink ta ajiye, xaro ido yayi yana kallonta, yaga ta fara kokarin cire doguwar rigar kantin jikinta, da sauri ya juya ya fita daga dakin ya sauka downstairs, tana gama canxa kayan ta dau net ta saka a kanta kamar yanda suke a gidan Dr Sumayya, ta fito dakin ta sauko kasa, buda ido yayi yana kallonta har ta karaso inda yake, can ya shafa kansa yace "No! Je Dauko hijab ki sa" shiru tayi
Chapter 55 · 0% Book details