Sashe 30
Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mumy ta girgixa Kai ta ci gaba da xuba masa abincin da take yi. Kasa cin abincin Junaid yayi, Mumy ta lura da hakan tace "Dama ka ci abincinka ka share komai, I keep telling you Junaid never depend on ur father, duk da nasan you are not depending on him dama, kar ma ka sa rai da komai nasa, sannan kayi ta bin sa ku rabu lafiya, you can see how things are going this days nasan ba yin kansa bane, banda hada ka da shi bbu abinda ake yi, lastly be prayerful" a hankali yace "In'sha Allah Mum" tace "Ya maganan da yayi maka jiya, kasan dai yana can yana kirga kwanakin da ya baka, ko kuma ince ana can ana Kirga masa koh" shiru Junaid yayi, Mumy tace "It's better ka kwantar da hankalin ka ka fito da mata tun kan ya nuna maka matsayinsa gun ka kamar yanda yayi ikirari" ae gaba daya abincin fita ran Junaid yayi, da kyar ya dinga tutturawa, Mumy na kula da hakan duk tausayin sa ya rufeta, tasan ba yin kan Abba bane yake masa haka, amma bbu yanda ta iya sai dai ta dage da Addu'a kamar yanda ta saba. Mikewa yayi jin ana kiran isha ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito ya tafi masallaci, ana idar da sllh yana tsaye da Abdul suna gaisawa ya ga tsayuwar motar El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito suka gaisa da Abdul sannan ya kalli Junaid ya shiga gida, part din Mumy ya nufa suka gaisa ta tambayesa mutan gida yace Duk suna lafiya, ya kalli hanyar bedrooms yace "Wa ke kuka kuma Mumy?" Mumy tayi murmushi tace "Humainah ce, daga Abba yayi mata fada wai fa" dariya yayi bai ce komai ba, Mumy tace "toh je ka lallasheta kila tayi shiru, ni taki saurara na" shiru yayi sai kuma ya mike kamar munafuki ya nufi bedroom din Mumy, tura kofar yayi ya shiga ya sameta xaune can karshen gado tana rera kukanta, ya kusa minti biyu tsaye kafin yasa kai ya shiga dakin, ya karasa inda take a hankali, ya duka yana kallonta, tuni ta hadiye kukan da take ta kauda kai, ya d'an bude ido yace "Am, dama Mumy ce tace in xo in baki hakuri wai kina kuka" juya masa baya tayi da sauri, ya d'an sosa kai murya can kasa yace "Kiyi hakuri" taki cewa komai, a hankali yace "Kin ji" Junaid ne ya shigo dakin yana ganinsu ya saka dariya yace "Uhnn! har dakin ka biyota Dr, ba sai ka jira in dawo in kira maka ita ba" El-ameen ya mike yace "Mumy ce tace in xo in bata hakuri Mr man" daga haka ya fice daga dakin, Junaid yace "ba wani nan da'alla kai dai fadi gaskiya" Humainah ta mike xata shiga bathroom ya fixgota yana dariya yace "Oya sorry lil sis" fixge hannunta tayi tace "Ae next time ko boka aka kawo xa a ajiye bakin kofar ka baxan ce komai ba" dariya yayi sosai yace "Nafa ce kiyi hakuri, beside Allah ya fisu I believe" goge mata fuskarta yayi yace "Yanxu sai ki je ki wanke fuskarki kiyi kwalliya kin ga saurayin ki ya xo" Turasa tayi ta shige bathroom, yayi murmushi ya fita, a parlor ya tadda El-ameen yace "Mu je" mikewa El-ameen yayi, Mumy tace "Baxa ka ci abinci ba Ahmad" El-ameen ya girgixa kai yace "Naci abinci Mumy" Mumy tace "Toh shikenan," har sun fita Mumy ta kira Junaid ya dawo, ya isa gabanta yace "Gani Mum" tana kallonsa a hankali tace "Kayi addu'a kafin ka shiga" ya sunkuyar da kansa yace "Toh Mumy" daga haka ya fita daga parlon, suka nufi part dinsa da El-ameen, yayi yanda Mumy tace masa ya bude kofar ya shiga, El-ameen ma ya shiga, El-ameen ya xauna yana kallon Junaid yace "Did you tell anyone about our patient?" Junaid yayi shiru sannan ya girgixa kai yace "Not at all" El-ameen yace "Ohk, daxu mama Jummai take ce min xata je kauyensu gun dotan ta ta haihu, amma kwana biyu kawae xata yi, toh I don't know yanda za ayi abun, who will stay with ur patient during her absent?" Junaid yayi shiru yana kallonsa, can yace "Or shud we get a new...." El-ameen yace "Noo! Kwana biyu tace xata yi beside yarinyar tafi sabawa da ita kafin ta saba da wata kuma is something else, yau satin su kusan uku tare if am not mistaken" Junaid bai kuma cewa komai ba, El-ameen yace "Hurry plss ina son komawa can gidan kafin in tafi clinic" Junaid yace "I don't know what to say" El-ameen yace "How about khadija, naga u guyz are close" lkci daya maganganun Hajiya na daxu da safe ya fado masa wai khadija ce tace mata ta gansa da mace a mota, girgixa kai yayi yana murmushi coz yasan khadija won't do that, a hankali yace "Humainah?" El-ameen yace "Baka tunanin xata yi exposing din mu, beside wannan me kukan me ma xata iya yi?" Junaid yyi murmushi yace "She won't, matsalar kawai Mumy ce" El-ameen yace "Alright, y not make it look as if gidanmu xaka kai ta gun Ummi, daga nan dai xa mu san yanda za muyi" Junaid yayi shiru sannan yace "Ohk Allah yasa ta yrda" mikewa El-ameen yayi yace "Gud, yanda ku ka yi gobe ka kira ni" Junaid yace "Wait, but kasan da wuri nake barin gida ai" El-ameen yace "However, just make sure gobe around 12 tana gida na or she shud meet me at the clinic" Junaid yace "Wait plss don Allah kamar yaushe kake ganin xata samu lafiya, will it take long?" El-ameen ya wara ido yace "Uhn! Har ka fara gajiya da kashe kudi kenan?" Junaid ya girgixa kai yace "Not at all, ina son ta samu lafiya ta nemo 'yan uwanta case dinta ya fita daga hannuna, har kuma hakan ya kasance bana fatan 'yan gidanmu su san komai" El-ameen ya daga kafada yace "But I hope you weren't daft the other day I was saying it's difficult to predict how, when, or to what degree she's going to get better, dat aside ma kayi addu'ar kar tayi loosing memory idan ma ta samu lafiyan!" Zaro ido Junaid yayi yace "Loosing memory kuma, No No in'sha Allah hankalinta gaba daya xai dawo, if not ya za muyi da 'yar mutane?" El-Ameen yayi murmushi yace "Allah dai ya kiyaye hakan" daga haka ya fice daga parlon yana cewa "Am off!", Junaid ya bisa da kallo sannan ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ya Allah ka ba ma wannan baiwa taka lafiya" mikewa yyi shi ma ya fita, part din Mumy ya shiga ya tarda El-ameen yana ma Mumy sallamah, Mumy tace "Yauwa Ahmad ku fita tare ka siyo min fruits" Junaid yace "Toh Mumy" tare suka fita da El-ameen a motar El-ameen din, Suna isa inda ake saida fruits yyi parking, Junaid ya fita ya siya fruits leda biyu ya dawo motar, ya ajiye ma El-ameen daya yace "For our patient" El-ameen yace "za ka raka ni shopping complex xan siya ma Ummi perfume wai" Junaid yace "Ohk" Suna isa bayan El-ameen yyi parking suka shiga babban mall din, El-ameen ya nufi gun perfumes, ya debi wa enda yasan Umminsa na amfani da, junaid dai binsa kawae yake, Suna isa gun teddy bears manya El-ameen ya dauka wani me kyau yana kallo, Junaid yace "toh fah!" El-ameen yyi murmushi ya ajiye a basket yace "For ur patient" daga haka suka bar wajen, biscuits da chocolates me yawa El-ameen ya dauka a trolley din, shi dai Junaid binsa kawae yake har ya gama daukan abinda xai dauka suka tafi inda ake biyan kudi, Wata yarinya ce tsaye gabansu sanye da hijab har kasa tana rike da basket dinta, gabanta kuma mutane biyu ne, El-ameen ya dawo kusa da Junaid murya can kasa yace "Don Allah ka d'an mata magana kace sauri muke ta bari mu fara biya, dubi fa kayanta da yawa" Junaid yyi masa wani kallo yace "Tunda kai baka da baki sai ni" El-ameen yyi tsaki yace "matsalata da kai kenan kamar ba namiji ba" Junaid bai kuma ce masa komai ba, har aka zo kan yarinyar bude Jakarta tayi xata fito da Atm bayan ta xube kayan da ta siya kan table ana lissafawa, dube dube kawai take a jakar, El-ameen yyi dariya can kasa yace "are you seeing what am seeing frnd?" Sharesa Junaid yayi, yarinyar ta juyo tana duba kasa, Junaid ya tsura mata ido yana tunanin inda ya taba ganinta amma ya k'asa tunawa, juyawa ta kuma yi tana kallon mutumin dake xaune yana jiran kudi tace "Malam Atm card dina ne ban gani ba wllh, kayi hakuri ka ajiye kayan tukun" sai a sannan Junaid ya tuna inda ya taba ganinta ta dalilin muryarta da ya ji, ya laluba jikinsa yaji bai fito da Atm card dinsa ba, kallon na hannun El-ameen dake dariya can kasa yana cewa "Karyar banxa wai bata gani ba" ya warce atm card dinsa ya nufi gun biyan kudin, El-ameen ya xaro ido yace "Kaiii" ko kallonsa Junaid bai yi ba ya mika masu yace "Gashi ku cire kudin ku" kallonsa yarinyar take ita ma tana son tuno inda ta taba ganinsa, su ko tuni suka karbi atm ya danna masu pin suka cire kudinsu har dubu talatin da biyar. A hankali yarinyar tace "Thank you" da alama ta tunasa ita ma, yayi murmushi yace "Never mind, it pays to be kind" Murmushi kawai tayi, ya juya yana ma El-ameen wani irin kallo. *Haske writers Association* *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 21..... Karasowa Junaid yayi gun El-ameen da ya wani hade rai yana kallonsa, junaid yayi murmushi ganin bai da niyar motsi daga inda yake gashi jiransa ake ya karbi basket din hannunsa ya tafi ya biya kudin kayan ciki, godiya yarinyar ta kuma yi ma Junaid bayan ta dauki kayanta da aka yi packaging a leda ta bar wajen, El-ameen ya bi ta da harara har ta fita, Junaid ya dinga danne dariyarsa har aka masa package din kayan da El-ameen ya siya ya bar wajen yana kallon El-ameen yace "Let move frnd" wani mugun kallo yayi