← Book details Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 104

Sashe 73

Captain Ahmad Junaid Complete Hausa Novel · about 8 min read

darduma. Yana xaune cikin mota idonsa a kanta ko kiftawa bai yi har ta karaso gun motar, sanye take da hijab dinta har kasa ta bude front seat ta shiga tana kallonsa tace "Na gama" bai ce komai ba ya ja motar suka bar gidan, sai da suka dau hanya sannan yace "Cikin ya daina ciwon ne?" Girgixa masa kai tayi tace "Yana yi har yanxu" bai kuma cewa komai ba har suka iso wani gida bayan tafiyar kusan minti ashirin, kallonta yayi ita ma haka, ya dauke kansa ya bude motar xai fita tace "Where is this captain?" Juyowa yayi yace "You wait for me, ba dadewa xan yi ba!" "toh" kawai tace ya fita ya kulle motar ya shiga gidan. Tsakar gida ne babba me dauke da sashi daban daban, xaune a tsakar gidan wata 'yar dattijuwa ce da yara mata biyu da baxa su wuce sha takwas ba, tana ganinsa tace "Ikon Allah, Ahmad ne a gidan namu yau!" Tana magana ne tana kokarin bude masa wani tabarma ya xauna, D'an murmushi yayi ya xauna kan tabarmar yace "Ni ne Hajiya, ina yini?" Da fara'a tace "Lafiya lau Ahmad, ya gida ya su Amina?" Yace "duk lafiya lau" gaishesa yan matan suka yi ya amsa hade da tambayar su makaranta, Hajiya tace "Toh ina amaryar taka, ai ya kamata ka kawo min ita mu gaisa ko Ahmad" ya shafa kai yace "Xan kawo ta Hajiya" Hajiya tace "Toh muna xuba ido" yace "Baba na ciki kuwa?" Tace "Ehh bai jima da shigowa ba ma, tashi ka je" mikewa yayi ya nufi babban parlon gidan, da sallama ya shiga ya samesa xaune kan babban darduma a kishingide, dattijon na ganinsa yace "Ikon Allah, Ahmad!" Karasowa Junaid yayi kansa a kasa ya xauna hade da yi masa sallama ya gaishesa, da fara'a dattijon ya amsa masa yana tambayarsa gida da Abbansa, junaid yace "Duk suna lafiya Baba" Dattijon yace "toh ya aka yi, ko Muhammad ne ya aiko ka?" Girgixa kai yayi yace "Shawara na xo nema gun ka baba" Gyara xama dattijon yayi yace "Toh bismillah, ina jin ka Ahmad" shiru Junaid yayi na d'an lokaci kafin ya fara basa labarin Jasmine tun daga lokacin da ya ganta har xuwa yanxu, kallonsa kawai dattijon ke yi, can yayi murmushi yace "Ahmad kenan, to amma meye ka boye ma iyayenka wnn aikin ladan da kayi, ai abun su yi alfahari da kai ne wannan" girgixa kai yayi yace "A'a ba lallai su fahimce ni ba ma" shiru dattijon yayi sannan ya sauke ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to tana ina yarinyar?" Junaid yace "Gidana take" "tare da matar ka?" Ya tambayesa yana kallonsa, shiru yayi kafin yace "Ehh!" Dattijon yace "Amma da amincewar matar taka kuwa" shiru junaid yayi nan ma, can kuma yace "A'a" dattijon yace "Toh maido ta nan Sa'adatu ta rike ta har Allah ya bata lafiya ya bayyana danginta" kallonsa junaid yayi da sauri, can ya sunkuyar da kai, dattijon yace "Hakan yayi maka?" Gyada masa kai kawai yayi yace "Nagode Baba" ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye masa dattijon yace "A'a je ka da abun ka Ahmad, duk lokacin da ka taso takanas don gaida ni xan karba" murmushi junaid yayi yace "Kayi hakuri baba, abubuwa ne suka yi yawa" dattijon yace "Allah kuwa" duk yanda junaid ya so tsohon ya amshi alkhairin kin karba yayi, haka yayi masa sallama ya fita bayan ya kuma jad'd'ad'a masa ya kawo Jasmine kar ya shiga hakkin matarsa, jinsa kawai junaid yayi ya fice daga parlon, yaran gidan ya bai ma kudin hannunsa yayi ma babarsu sallama ya fita, Malam tukur malamin mahaifinsa ne tun fil'azal, kusan gun sa junaid ya sauke littattafen addini da dama hakan yasa yake girmama tsohon. Bacci ya tarda Jasmine ke yi a motar bai tasheta ba ya tada motar ya bar layin bayan ya kwantar mata da kujerar. Yana xaune shi daya parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, gaba daya hankalinsa yayi gun mumynsa a lokacin, dama akwai tym din da xai xo ya dade haka bai je inda take ba without any reason, lumshe ido yayi duk ya rasa abun da ke damunsa yanxu, gashi ko kadan shawarar da Malam Tukur ya basa bai masa ba, muryar Jasmine yaji tace "Captain!" Ya bude ido da sauri yana kallonta tace "Anty baxa ta dawo ba?" Hade rai yayi yace "leave!" Da sallama El-ameen ya shiga parlon, Mumy dake xaune da fatima suka amsa masa ya karasa cikin parlon ya gaida Mumy da fara'a bayan ya xauna, da murmushi ta amsa masa tana kallonsa, fatima ta gaishesa ya amsa hade da tambayarta sch, kallon Humainah dake kwance yayi kan yace komai ta gaishesa, ya amsa da murmushi lkci daya ya gano ba ita daya bace, ya kusa minti sha biyar parlon kafin Mumy tace "kana ji na Ahmad?" Ya kalleta yace "Ina ji Mumy" kasa cewa komai tayi da ganinta kasan there is something eating her in, gashi duk ta rame, sunkuyar da kansa yayi ko bata fadi ba yasan kan junaid ta kirasa, a hankali yace "Mumy kin yi shiru" cikin sanyin murya tace "I don't know what has come over ur frnd...." Kallonta yayi yace "Me ya faru Mumy?" Tuni idonta ya kada ta kasa ci gaba, jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai kuma, bude kofar aka yi Abba ya shigo yana ganin El-ameen yace "Good u are here" xaunawa yayi ya fiddo wayarsa yyi danne danne ya kara kunne, junaid dake durkushe a lokacin kusa da Jasmine dake juye juye wai cikinta na ciwo ya kalli screen din wayar hannunsa gabansa ya fadi ganin Abbansa ne, da kyar ya d'aga daga daya bangaren Abba yace "Ka taho ina jiran ka yanxu" daga haka ya katse, bbu tunanin da junaid bai yi ba daga karshe dai ya mike bayan ya lullube Jasmine ya fita, xuciyarsa na raya masa Humainah ta fadi abu kenan a gida, cikin yan mintuna ya isa gida, yayi part din Mumy jiki ba kwari, bai yi tunanin Abba na can ba, yana bude kofar yayi still ta dalilin ido hudu da suka yi da Abban nasa, da kyar ya karaso parlon yayi ma El-ameen kallo daya ya dauke kai gabansa na faduwa, kasa kallon inda Mumy take yyi, ga Anty Nafisa ma dake parlon sai Aysha da Humainah dake jikinta, ya xauna ya gaida Abba, yaji no answer, a sanyaye ya gaida Mumy nan ma no answer, bai kuma gaida kowa parlon ba, cikin kaushin murya Abba yace "Ahmad!" Da kyar ya dago kai ya kallesa, Abba yace "Bani takardar Humainah!" Kallonsa kawai yake kamar bai fahimce sa ba, Abba ya mike yace "Ni kake ma wannan kallon?" Sunkuyar da kai yayi, A nutse Abba yace "Bani takardarta nace" junaid ya lumshe ido ya bude yace "Abba ni bbu abinda ya hada mu......" Bai rufe baki ba Abba ya sauke masa mari yace "You are very stupid ka bani abinda na tambayeka ko sai na saba maka" shiru yayi na d'an lokaci sai kuma yace "Babu takarda hannuna" Abba ya kalli Aysha yace "Ke tafi nemo min takarda" da kyar ta mike jiki a sanyaye ta shiga daki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da takarda Abba ya karba ya mika masa, karba yayi ya ciro pen din dake aljihunsa duk aka xuba masa ido a parlon barin Mumy da ko kiftawa bata yi, Humainah kam jikin kujera ta rufe fuskarta hawaye na sakko mata, cikin 'yan mintuna ya gama rubutunsa a jikin takardan ya mika ma Abba ba tare da ya bari sun hada ido ba, wani kallo El-ameen ke ma junaid yana son assuring kansa ba saki ya rubuta ba, Abba ya kusa minti uku idonsa na kan takardan kafin yayi wani murmushi ya mika ma Mumy da tuni hawaye ya cika idonta, ajiye takardar tayi don baxata iya gani ba, Anty Nafisat ta dauka da sauri cikin few seconds ta gama karanta takardan, mikewa tayi lokaci daya idonta ya canxa launi tace "Ehh lallai ka xama dan iska Ahmad, sakin ka rubuta da gaske?? Ashe kai mara imani ne?" Hannu Abba ya daga mata sannan ya kalli Junaid yace "Tashi ka tafi" mikewa yayi kansa a kasa ya nufi kofa, Mumy ta fashe da kuka haka ma Aysha, Humainah kam kin dago kanta tayi, El-ameen ya mike da sauri ya bi bayansa, karo junaid ya kusa ci da Umma da Hajiya dake labe balcony, bai ko bi ta kansu ba ya sauka, taku daya biyu yayi still yana kallon Hadiza dake tsaye balcony din Hajiya lokaci daya ya ganeta, tana ganinsa tayi saurin shigewa parlor ta rufe kofa, ji yayi kansa na juya masa, kan kace me har ya fice daga compound din ya isa gun motarsa, fixgosa El-ameen dake biye da shi yayi yace "Sakin ta kayi Ahmad?" Wani kallo Junaid yayi masa yace "Ehh" murmushin takaici El-ameen yayi yace "Good!" Junaid ya shige motarsa ya tada ya bar layin. *Haske Writer's Association* [3/19, 9:34 PM] El-hajj *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 66__67 to 70 Ko parking din arxiki bai yi ba ya shige cikin gida ya nufi dakinsa direct ya kwanta xuciyarsa na bugawa, har aka kira magrib yana kwance can ya mike yayi alwala ya fita xuwa Masallaci, sai da ya dawo ya shiga dakin Jasmine yaga bacci take, tashinta yayi ta bude ido a hankali, kallonta ya tsaya yi, ta mike xaune tace "Captain" kifta idonsa yayi yace "Cikin ya daina?" Ta gyada masa kai yace "Me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "am not hungry" mikewa yayi yace "toh kiyi sallah" daga nan ya fita daga dakin. Har kusan daya na dare junaid bai yi bacci ba yana dai kwance, mikewa xaune yayi jin kamar an bude kofar parlor ya kalli agogo, jasmine? Toh ina za ta? ya mike tsaye ya nufi kofa da sauri ya fita, dai dai lokacin da haske ya gauraye downstairs, still yayi a gun, can kuma ya bude kofar dakinta, ga mamakinsa sai ya ganta kwance, kansa ya daure ba kadan ba don ya kulle kofar ai, karasawa dakin yayi da hanxari gun gadon ya cire bargon jikinta ta bude ido a tsorace, dagota yayi tace "Captain"
Chapter 73 · 0% Book details